*_KE6ANCE RANAR JUMA'A DA YIN AZUMIN NAFILA!!!_*
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
*Zauren SA'ADATUL-MUSLIM*
.
السلام عليكم ورحمة الله وبركاته وصلاة والسالم على النبي المصطفة، محمد صلى الله عليه وسلم.
.
_Dan uwa na kasani lallai Allah madaukaki yayi maka rahama, kuma kasani wajibi ne a gareka ka koyi ilimin addinin ka na musulunci domin ka bauta wa ubangijin ka'aba yanda ya shar'anta maka ta hanyar Annabinsa Muhammad saw, domin tabbatuwa akan hanyar kwarai, wannan rubutu da zauren SA'ADATUL-MUSLIM yayi maku tsarabarsa a yau to in Allah ya yarda wani hadisi ne zamu dauka mu karanta domin tunstarwa kamar yanda musulunci yayi mana tanadi ga Allah muke neman taimako kuma muna rokon sa yayi mana agaji yayi mana jagoranci,_
.
_Dan uwa na kasani Lallai ke6ance ranar juma'a da yin azumin nafila bai halatta ba ga musulmi wanda yake kokarin bin tafarkin manzon Allah saw, lallai bai halatta ba ga kowwanene ya ke6ance ranar juma'a kadai yace zai dika yin azumi na nafila acikinta amma kuma kasani ya halatta ga wanda ya kasance yana yin azumin nafila irin na Annabi Dauda Alayhis-Salam wato yau yayi azumi gobe yasha ruwa jibi ma sai ya dauka azumi, haka dai zaiyi tayi a rayuwarsa to wannan ya halasta a gareshi yayi azumi a ranar juma'a idan ranar daukan azuminsa yayi dai dai da wannan ranar,_
.
_Sannan kuma ya halasta idan ana bin mutum azumi na ramadan ko kuma na bakance ko na rantsuwa ya halasta yayi a ranar juma'a idan ya nufaci aikata hakan, domin kadai mu abinda muke magana akai shine hani dangane da ke6ance yin azumin nafila a ranar juma'a, hadisi ya tabbata daga Ahmad dan Mansoor Al-Maruuziy yace Salmata dan Sulaiman ya bamu labari yace Abdillahi dan Mubarak ya bamu labari yace Abdillahi dan Muhammad dan Umar dan Aliyu daga Mahaifin sa yace, lallai Kuraiba Maula Ibn Abbas ya bashi labari cewa, lallai Ibn Abbas da wasu mutane daga cikin sahabban Manzon Allah saw sun aike ni wajen Ummu-Salamah cewa intambaye ta dangane da wad'anne ranaku ne Annabi saw yake yawaita azumi acikin su? Sai tace yana yawaita azumi ranar asabar da lahadi yace sai na dawo zuwa wajensu sai na basu labari dangane da amsar data bani, lallai su sun nuna kamar suna inkarin haka, sai Ibn Abbas da sauran sahabbai suka tashi gaba dayansu sai suka tafi wajen ta sai sukace, lallai mu mun aiko dan sako zuwa gareki acikin amsar da kika bashi kin ce wai kaza da kaza (wato suka ambata mata amsar data bayar) shin da gaske amsar da kika bayar kenan (wato cewa Annabi yana yawaita yin azumi ranar asabar da lahadi)? Sai tace yayi gaskiya lallai Manzon Allah saw yana yawaita yin azumi ranar asabar da lahadi, domin kuwa lallai wad'annan ranakun sun kasance ranar Idi ne ga mushrikai (Wato ranar asabar yahudawa Ahlil Kitab suna girmama wannan rana, su kuma nasara wato Christoci suna girmama ranar lahadi,) to kuma lallai ni inaso na sa6a masu, (tunda dai su suna cin kwalliya da ado da girke-girken ababe da wake-wake da shirka da kafirci suna ciye-ciye, to lallai ni in yin azumi ne domin na sa6a masu akan abinda suke akai na 6arna), (Wannan hadisi ne ingantacce wanda Ibn Khuzaimah ya kawo shi acikin Sahihu Ibn Khuzaimah mujalladi na 3 shafi na 318,)_
.
_Don haka dan uwa na Sunnah be ka dika yin azumin nafila ranar asabar da lahadi, domin yin koyi da manzon Allah, kuma kasani haka dabi'ar Manzon Allah saw yake dukkanin abinda ya kasance yahudawa sunayi acikin wannan duniyar to Annabi duk yanda zaiyi ya sa6a masu sai yayi domin kada yayi kamacece niya da baahude ko bana sare, shin kai haka kake!? Allah shi gafarta mana, lallai zaman lafiya ga dan Adam shin koyi da Annabi saw Allah yasa mudace,_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp
KARKU MANTA DA GAYYATO MANA DA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.
0 comments:
Post a Comment