MENENE HUKUNCIN YIN LAYYA DA DABBA MAI CIKI? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Wednesday 30 August 2017

MENENE HUKUNCIN YIN LAYYA DA DABBA MAI CIKI?

*MENENE HUKUNCIN LAYYA DA DABBA MAI CIKI?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Malamai Sunyi Sabani akan yin layya da dabba mai ciki, jamhur din malamai sun tafi akan halaccin yin layya da dabba mai ciki, basu Ambaci dabba mai ciki, acikin aibukan da suke hana ayi layya da dabba ba,

Shafi'iyyah sun sabawa Jamhur sukace: Bai halatta yin layya da dabba mai ciki ba,

Yazo: acikin *Mausu'ah fiqhiyyah (16/281).*

Malamai Basu Ambaci dabba mai ciki cikin aibukan da suke hana ayi layya da dabba ba, sabanin shafi'iyyah, inda suka bayyana rashin halaccin yin layya da dabba mai ciki, saboda ciki yana bata ciki, nama ya zama lababbe,.

Ingantacciyar magana shine: Ya halatta ayi layya da ita, idan babu wani abun dazai hana ayi da ita na daban,.

Jaririn da aka Samu acikin dabbar layya, idan an sameshi araye za'a wankeshi aci,

Ibnu qudama yace: idan an sameshi rayayye rayuwa tabbatacciya, daza'a iya tsaftaceshi ba'a tsaftace shi ba, harya mutu, toba tsafta tacce bane, Ahmad yace: idan ya fito araye dole, a tsaftaceshi, domin wani rai ne daban.

*Al-Mugny (9/321).*

Idan aka samu jariri acikin dabbar layya matacce, jamhur din malamai sukace: Za'aci namansa, domin ya tsarkaka da tsarka kuwar uwarsa,

*Abu dauda ya ruwaito (2828) da Turmuzi (1476) ibnu majah ya ingantashi (3199) da Ahmad (10950).*

Daka Abu sa'idin daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Tsarkakuwar jariri, tsarkakar Uwarsa ne) Albani ya ingantashi *acikin Sahihul jami'i (3431).*

Wannan kamar yanda mukace shine mazhabar jamhur din malamai. sabanin Hanafiyyah.

Shaikul Islam ibnu taimiyyah acikin *maj-mu'u fatawa (26/307)* Yace:

Layya da dabba mai ciki ya halatta, idan aka samu danta ya mutu, tsarkinsa shine tsarkin uwarsa, awajan shafi'iyyah da Ahmad, da Wasunsu, yayi gashi ko baiyi gashi ba.

Idan aka sameshi araye, za'a yankashi.

Awajan malikiyyah : idan yayi gashi, ya halatta, idan baiyi gashi ba, bai halatta aci ba.

Awajan Abu Hanifa : baya halatta aci harsai an tsarkake shi bayan fitowarsa.

Saidai Wasu malamai Sun karhanta cin naman jaririn dabba ta fuskar lafiya.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*

KARKA MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support