jagoran mahajjaci 01 ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday, 8 August 2017

jagoran mahajjaci 01

​Jagoran Mahajjaci (01)​

​Bismillahir Rahmanir Rahim​

Yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijinmu madaukaki.
Salati da sallama su kara tabbata ga fiyayyen Manzo, da kuma Iyalansa da Sahabbansa masu karamci.

​Bayan haka​;

Abinda a kullum zai rika zuwa muku, shine hadisan ​Hajji da umrah; ta fiskar Sifofinsu da  Falalolinsu, da ambato duk abinda ke ta'allake da su; na sharrudai da farillai da ladduba, da mustahabbai, da Mikaatai, da mahazuran da aka yi hani akansu daga zarar mahajjaci ya yi haramarsa ta hajji da umrah, da hadisai kan yinin Arafah da falalarsa, da layya da hukunce-hukuncensa. Sai hadisan falalar Madina da ladabin ziyartarta, da sauran abinda ya yi alaka da hakan​

Da fatan Allah ya azurta mu da ikhlasi cikin zance da aiki, amin; saboda ya zo cikin hadisin Umar (R. A); cewa:

 عن عُمَر بْن الْخَطَّابِ رضي الله تعالى عنه، قال:

سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ:

​«إِنَّمَا الأَعْمَالُ بِالنِّيَّاتِ، وَإِنَّمَا لكل امْرِئٍ مَا نَوَى، فَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ فَهِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ، وَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُه لدُنْيَا يُصِيبُهَا، أَوِ امْرَأَةٍ يَنْكِحُهَا فَهِجْرَتُهُ إِلَى مَا هَاجَرَ إِلَيْهِ»​.

ـــــــــــــــــــــــــ
أخرجه البخاريّ [1]، ومسلم [1907].
ـــــــــــــــــــــــــ

​Fassara​

An ruwaito daga Umar dan Al-khaddabi -Allah ya kara yarda a gare shi-, ya ce:

Na ji Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- yana cewa:

​"Lallai ayyuka su kan inganta ne da niyya, kuma lallai kowane mutum yana samun sakamakon abinda yayi niyya; Wanda hijirarsa ta kasance saboda Allah ne da ManzonSa to sakamakon hijirarsa tana ga Allah da ManzonSa. Wanda kuma hijirarsa ta kasance saboda wata duniyar da zai same ta, ko don wata matar da zai aure ta, to sakamakon hijirarsa yana ga abinda yayi hijira dominsa"​.

ـــــــــــــــــــــــــ
Bukhariy [1] ya ruawaito shi, da Muslim [1907].
ـــــــــــــــــــــــــ

​تأدية الحج، من الخمس التي بني عليها الإسلام​
​AIKIN HAJJI YANA DAGA GINSHIKAI BIYAR, WADANDA AKA GINA MUSULUNCI AKANSU​

 ​1/​ عَن عبد الله بْن عمر رضي الله عنهما، قَالَ:
سمعتُ رَسُول اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يقول:

​«بُنِيَ الإِسْلامُ عَلَى خَمْسٍ، شَهَادَةِ أَنْ لا إِلَهَ إِلا اللَّهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَإِقَامِ الصَّلاةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ، وَصَوْمِ شَهْرِ رَمَضَانَ، وَحَجَّ الْبَيْتِ»​.

ـــــــــــــــــــــــــ
أخرجه البخاري [8]، ومسلم [16].
ـــــــــــــــــــــــــ

​Fassara​

An ruwaito daga Abdullahi dan Umar -Allah ya kara yarda a gare su- ya ce:

Na ji Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- yana cewa:

​"An gina Musulunci akan abu guda biyar; Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Muhammadu manzon Allah ne, da tsayar da sallah, da bada zakka, da yin hajjin wannan dakin, da azumin watan Ramadana"​.

ـــــــــــــــــــــــــ
Bukhariy [8] ya ruwaito shi, da Muslim [16].
ـــــــــــــــــــــــــ

​2/​ وورد ذكر ​العمرة​ في إحدى روايات حديث سؤال جبريل، فاجاب الرسول عليه الصلاة والسلام، بقوله عن الْإِسْلام:
​"الإسْلامُ: أَنْ تَشْهَدَ أَنْ لا إِلَهَ إِلا اللَّهُ وَأَنَّ مُحَمَّداً رَسُولُ اللَّهِ، وَتُقِيمَ الصَّلاةَ، وَتُؤْتِيَ الزَّكَاةَ، وَتَحُجّ وَتَعْتَمِر، وَتَغْتَسِل مِنْ الْجَنَابَة، وَأَنْ تُتِمّ الْوُضُوء، وَتَصُومَ رَمَضَان"​

وَقَالَ فِيه:ِ "فَإِذَا فَعَلْت ذَلِكَ فَأَنَا مُسْلِم؟
قَالَ: ​نَعَمْ"​.

ـــــــــــــــــــــــــ
أخرج هذه الرواية ابن خزيمة، والدارقطني في السنن، ثم قال: ​إسناد ثابت صحيح، أخرجه مسلم بهذا الإسناد​. وصححه الشيخ الألباني.
ـــــــــــــــــــــــــ

​Fassara​

Ambaton ​umrah​ kuma, ya zo ne cikin  hadisin tambayar Jibrilu akan Musulunci, da yadda Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya amsa masa, a riwayar Ibnu-Khuzaimah da Ibnu-hibbana da Ad-darakydniy, da fadinsa:
​Musulunci: shi ne, ka shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma annabi Muhammadu manzon Allah ne, ka tsayar da sallah, ka bada zakka, ka yi hajji ka yi umrah, kuma ka rika wankan janaba, kana cika alwala, da azumin watan Ramadhana"​.

Sai ya ce: Shin idan na aikata hakan, Ni musulmi ne?
Sai ya ce: ​"E"​.

ـــــــــــــــــــــــــ
Ibnu-Kuzaimah a cikin "sahihinsa" ya fitar da wannan riwayar, da Ibnu-hibbana da Ad-Darakudniy a cikin "sunan", kuma ya ce: ​isnadin hadisin tabbatacce ne ingantacce, Muslim ya ruwaito hadisin da wannan isnadin​. Kuma Albaniy ya inganta shi.
ـــــــــــــــــــــــــ

​Tsokaci​
ـــــــــــــــ
Wadannan hadisan suna nuna;
​(1)​ Wajabcin niyya, da kasancewar ibadun hajji da umrah da wasunsu, basa inganta, kuma basa zama karbabbu a wurin Allah ta'alah, face da niyya.

​(2)​ Muhimmancin hajji, da matsayinsa a musulunci, da kasancewarsa daya daga cikin ginshikai ko filoli masu karfi guda biyar (5) wadanda aka gina Musulunci akansu.

​(3)​ Umrah wajiba ce a dayan zantuka biyu na malamai, kuma ambatonta ya zo a cikin hadisin da ke bayanin hakikanin musulunci.

​Allah Shi ne mafi sani​

Daga: ​ZAUREN FIQHUS SUNNAH​
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support