LABARIN WASU MAKAFI GUDA BIYU. ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Friday 25 August 2017

LABARIN WASU MAKAFI GUDA BIYU.

LABARIN WASU MAKAFI GUDA BIYU
**************************************
Akwai wasu Makafi guda biyu azamanin daular Abbasiyyah. Sai sukayi shawara atsakaninsu cewa suje su zauna akan hanyar da Matar Sarkin Garin take wucewa, saboda sun riga sun san cewa tana da kyauta da karamci. Suna kwadayin cewa idan tazo wucewa zata yi musu kyauta mai yawa.

'Daya daga cikinsu yana yin bararsa yana cewa "Ya Allah ka bani daga Falalarka". Shi kuma dayan saboda Tsananin kwadayi yana cewa "Ya Allah ka azurtani daga falalar Ummu Ja'afar (wato sunan Matar Sarkin kenan).

Kullum matar sarki tana wucewa ta kusa dasu tana jin abinda suke fa'da, don haka wannan da yake roko daga Falalar Allah sai take aika masa kullum da Sadakar DIRHAMI BIYU (Kimanin kamar Naira #1,200).

Shi kuma wanda yake rokon cewa Allah ya bashi daga falalar Ummu Ja'afar, sai take aika masa da Dankwaleliyar Kaza wacce aka soya, kuma ta sanya masa Dinare Goma acikin tsakiyar Kazar (Kimanin Naira #280,000).

Shi wannan da take aiko masa Kazar, ya kasance kullum idan ta aiko masa sai ya sayar ma abokin zaman nasa akan Dirhami biyu. (Ba tare da sanin cewar akwai Makudan kudade acikinta ba).

Haka suke ta yi har tsawon kwanaki goma a jere. Rannan dai Matar Sarki (Ummu Ja'afar) tazo wucewa kamar yadda ta saba, Sai ta tsaya ta tambayi wannan dake yin roko daga falalarta cewa : "Shin har yanzu Allah bai wadatar da kai daga falalar tawa bane?".

Sai yace "Ina falalar taki take?". Sai tace "Ai na aiko maka da Dinare dari (100) acikin kwana goma".

Sai Makahon yace "A'a, Kaza ce kike aiko min kullum. Ni kuwa nake sayar da ita ga abokin zamana akan dirhami biyu".

Da taji haka sai abun ya bata dariya. Tace "Kai ka roka daga Falalarmu don haka sai Allah bai baka ba. Shi kuwa Wancan ya roka ne daga Falalar Allah don haka sai Allah din ya bashi kuma ya wadatashi".

- Duk wanda ya dogara ga wani Mutum ko Wasu Mutane, to sai ya hadu da Qaskanci.

- Duk wanda ya dogara da wata dukiya wacce yake Taqama da ita, to wataran zata Qare, ta tafi ta barshi. Ko kuma shi ya tafi ya barta ta Qare ahannun magadansa.

- Duk wanda ya dogara akan Iliminsa kadai, yana ganin kamar yafi kowa, to lallai ya 'bata.

- Duk wanda ya dogara akan son zuciyarsa, to lallai sai ya karkace daga kan hanyar gaskiya.

- Amma duk wanda ya dogara ga Allah ba zai Qaskanta ba, ba zai Talauta ba, Ba zai 'bata ba, Kuma ba zai karkace daga hanyar gaskiya ba.

Domin hakika Allah mai karamci ne, mai baiwa ne, Mai jibintar lamarin bayinsa ne.

Ya Allah gareka muk dogara, Kai kadai muke bautawa, kai kadai muke roko, Kuma kai kadai muke neman taimakonka.

Wannan nasiha ce daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP 17-07-2016.

Ya 'dan uwa Musulmi, wanne darasi ka dauka daga wannan nasihar?.
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support