YANDA YA DACE MUSULMI YA FUSKANCI KWANAKI GOMA (10) NA FARKON WATAN DHUL-HIJJAH ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Wednesday, 16 August 2017

YANDA YA DACE MUSULMI YA FUSKANCI KWANAKI GOMA (10) NA FARKON WATAN DHUL-HIJJAH

*YANDA YA DACE MUSULMI YA FUSKANCI KWANAKI GOMA (10) NA FARKON WATAN DHUL-HIJJAH*

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah. Tsira da aminci su kara tabbata ga Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, Alayensa da Sahabbansa da dukkan wanda ya biyo bayan su da kyautatawa.

Bayan haka, duba da yanda kwanaki goma na farkon watan Dhul-Hijja suke da matukar muhimmanci, amma mafi yawa daga cikin mutane sun rafkana ga barin cin gajiyan su, ya sanya na ga dacewar in yi tsokaci a takaice dangane da wadannan kwanaki.

Dukkan abun da aka samu na daidai a cikin wannan Rubutu nawa daga Allah ne, abun da kuma aka samu na kuskure daga gare ni ne da Shaidan, Allah Ta'ala da ManzonSa sun barranta daga gare shi.

Da me ya kamata Musulmi ya fuskanci wannan wata da shi?.

1. *TUBA ZUWA GA ALLAH* saboda zunubi shi ne kofa mafi girma da yake sanya Allah Ta'ala Ya azabtar da bawa.

Allah Ta'ala Ya yana cewa: *_"Kuma wata musiba da take samun ku face sai sakamakon abun da hannuwanku suka sana'anta"_*. Suratu al-Shuura aya ta 30.

Babban dalilin da zai sa mu fara wannan wata da tuba shi ne, barna da tasirin da zunubai suke yi a rayuwar mutum. Daga ciki:

Na farko: Zunubai suna haramta ma mutum samun ilimi mai amfani. Domin shi ilimi haske ne da Allah Ta'ala Yake sanyawa a zuciyar mai shi, kuma zunubai suna kawar da wannan hasken.

Na biyu: Zunubai suna sanya talauci su hana bawa samun arziki.

Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: *_Lallai ana haramta bawa arziki saboda wani zunubi da ya aikata_*. Imamu Ahmad ya riwaito a cikin al-Musnad 5/282.

Na uku: Duhu da da mutum zai rinka ji a zucirya shi.

Abdullahi Bn Abbas, Radhiyallahu Anhu, ya ce:  *_"Lallai kyawawan ayyuka suna sanya ma mutum hasken fuska da hasken zuci da yalwan arziki da karfin jiki da soyayya daga bayin Allah, kamar yadda sabon Allah yake fuska zuciya ya yi duhu da duhun zuciya da raunin jiki da tawayan arziki da kiyayya daga mutane"_*.

Na hudu: Zunubai suna sanya daraja da mutuncin mutum ya zube a wurin Allah.

Allah Ta'ala Ya na cewa: *_"Dukkan wanda Allah Ya wulakantar, to ba shi da wani mai girmamawa_*. Suratul Hajji aya ta 18

Na biyar: Idan mutum yana aikata zunubai zai wayi gari baya ganin girman zunuban, wannan kuma alama ce ta tabewa da halaka.

Na shida: Idan mutum yana aikata zunubai za a wayi gari sun lullube zuciyar shi har ta yi tsatsa ta koma bata iya daukan wa'azi da shiriya.

2. *NEMAN TAIMAKON ALLAH A WADANNAN KWANAKI*: Wadannan kwanaki ya dace dukkan musulmi ya dage wurin neman taimakon Allah domin ganin ya ribace su yanda ya kamata.

Allah Ta'ala Ya na cewa: *_"Kuma wadanda suka yi kokari ga neman yardanMu, lallai Muna shiryar da su ga hanyoyinMu, kuma lallai Allah Tabbas Yana tare da masu kyautatawa"_*.  Suratul 'Ankabut aya ta 69.

*ME YA SA AKA FIFITA YINNAI GOMA NA FARKON WATAN DHUL-HIJJAH AKAN WASUNSU???*

Mu hadu a fitowa ta 2 in sha Allahu Ta'ala

✍🏼Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*
15/08/2017.

Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

Kada kumanta da gayyato mana abokananku Zuwa wannan shafin Mun gode.
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support