*YANDA YA DACE MUSULMI YA FUSKANCI KWANAKI GOMA (10) NA FARKON WATAN DHUL-HIJJAH*
Fitowa ta 4
*RANAR ARAFA*
2. Rana ce wanda a cikin ta Allah Ta'ala Ya ke yawan 'yanta bayi daga wuta kuma Ya ke ma Mala'iku alfahari da wanda suke tsaye a filin Arafa.
An karbo daga Nana A'isha, Radhiyallahu anhaa, ta ce: Lallai Manzon Allah, Sallallahu' alaihi wa sallama, ya ce: *_"Babu wata rana da Allah Yake yawan 'yanta bawa daga wuta kamar ranar Arafa. Kuma Yana kusantowa Ya yi alfahari ga Mala'iku yana cewa: Me wadannan mutane suke nufi?"_*. Muslim ne ya ruwaito 1348.
3. Azumtar azumin ranar Arafa yana kankare zunubin shekaru biyu.
An karbo hadisi daga Abiy Qatadah al-Ansaariy, Radhiyallahu Anhu, ya ce: An tambayi Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, dangane da azumtar ranar Arafa, sai ya ce: *_"Ina tsammani daga Allah, yana kankare zunuban shekaran kafin ta da wanda ke biye mata"_*. Muslim ne ya ruwaito 1162.
4. Mafi alherin addu'a ita ce addu'ar ranar Arafa.
Daga 'Amru Bn Shu'aib daga Mahaifinsa: Lallai Manzon Allah, Sallallahu' alaihi wa sallama, ya ce: *_"Mafi alherin addu'a ita ce addu'ar ranar Arafa, kuma mafi alherin abun da na fada Ni da sauran Annabawa da suka zo kafin ni shi ne: Laaa ilaaha illaaLallah wahdaHu Laaa Shariyka laHu, Lahul Mulk wa Lahul Hamd wa Huwa 'Alaa Kulli shai'in Qadiyr"_*. Tirmizi ya ruwaito 3585, Sheikh Muhammad Nasirudden Albani, ya ce hadisi ne Hasan.
*DABI'UN MAGABATA A RANAR ARAFA*
Abdullahi Bn al-Mubaarak, Rahimahullah, ya zo wurin Sufyaanu al-Thauriy, Rahimahullah, a yammacin ranar Arafa sai ya tarar da shi gurfane a akan guiwansa a filin arafa alhalin idanuwan shi suna zubar da hawaye, sai Abdullahi ya ce ma Sufyan al-Thauriy: wane ne mafi munin dabi'a a cikin wannan taron jama'a?, sai ya ce masa: shi ne mutumin da yake tsammanin Allah ba Zai gafarta masa ba. A duba littafin Ladaa'iful Ma'aarif 285-288.
*WASU AYYUKA NE AKA FI SO MUTUM YA AIKATA A WADANNAN KWANAKI GOMA???*
Mu hadu a fitowa ta 5 in sha Allahu Ta'ala
✍🏼Dan uwanku a Musulunci:
*_Umar Shehu Zaria_*
18/08/2017.
Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

0 comments:
Post a Comment