SHIN DALILAN YIN LAYYA DALILAINE NA WAJABCI KO MUSTAHABBANCI? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Wednesday, 30 August 2017

SHIN DALILAN YIN LAYYA DALILAINE NA WAJABCI KO MUSTAHABBANCI?

*SHIN DALILAN LAYYA DALILAINE NA WAJABCI KO MUSTAHABBANCI?*

الحمد لله سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA :* A wannan mas'alar akwai Sabani Shahararre tsakanin Malamai, Mafi yawan Malamai suna ganin Sunnatuwar layya ne ba wajabcin taba.

Hanafiyyah da Imamu Ahmad a wata ruwaya da Shaikul
Ibnu taimiyyah ya zaba sun tafi akan wajabcin layya akan mawadaci.

Ibnu qudama yace: mafi yawan malamai suna ganin layya sunnah ce mai qarfi ba dole bace, .

An ruwaito haka daka *Abubakar da Umar da Bilal, da Abi mas'uud Al-badary* Allah yaqara yarda dasu.

Haka *Suwaid bin gafala da sa,'eed bin Musayyeeb da Al-qama da Aswad, da Ada'u da Shafi'i, da Ishaq, da Abu Saur, da Ibnu Munzir* sukace.

Rabi'ah da Malik da Saury da Auza'iy da Lais, da Abu hanifa, sukace: Dolece .

Saboda hadisin da Abu huraira Allah yaqara yarda dashi yace: Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Wanda yake da Wadata baiyi layya ba, kada ya Kusanci masallacin mu).

Daka Miknaf bin Sulaim, Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( yaku Mutane akan dukkan mutanen gida, kowacce shekara akwai layya, da yankan watan rajab na jahiliyyah.).

Darul Qudny ya ruwaito hadisi da isnadi daka ibnu Abbas daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: abubuwa uku wajibine akaina, akan ku kuma nafila ne, wutiri, da Yankan layya, da raka'atanul fajri.

Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Wanda yai nufin zaiyi layya, kada ya aske gashinsa ko farcensa,) Ya Alaqanta ta da Iko  wajibi ba'a jinginashi da iko, .

*Al-mugny (11/95).*

Dalilan dukkan Bangarori biyu na Malamai suna da yawa, saidai dukkansa basu kubuta daka matsala a isnadojinsu ba, ko daka jayayya wajan kafa hujja dasu ba, .

Wadanda Sukace dolece, suna kafa hujja da hadisin Abu huraira ( Wanda yake da wadata yaqi yin layya kada ya kusancinmu masallacinmu) ibnu Majah.

Malaman hadisi basu sallama ingacin maganar daka Annabi ba, sunyi masa hukunci da cewa maganar Abu hurairace ,bata Annabi ba, .

Baihaqi acikin Sunan dinsa (9/260) yace: Labari yazomin Abu isah Atturmuzi yace: Hadisine sahihi, yace: Ja'afar bin rabi'ah ya ruwaitoshi da waninsa daka Abdurrahaman Al-a'araj, daka Abu huraira.

Ibnu hajar yace: ibnu majah ya fitar dashi da Ahmad, mazajensa Amintattune, saidai anyi sabani wajan shin maganar Annabi ce,.

*Fatahul bary (12/98)..*

Wasu sun rinjayar da cewa hadisine mauqufi, kamar Ibnu Abdul barri da Abdul haq acikin Ahkamul wusdaah (4/127) da Munzry acikin Targeeb wattarheeb, da Ibnu Abdul hady acikin tanqeeh (2/498) duba Hashiyar Masu tahqiqin sunanu Ibnu majah (4/303).

Hadisi na Biyu, shine hadisin Abu ramlah daka miknaf bin sulaim Marfu'an, Abu dauda ya ruwaitoshi (2788) da Turmuzy (1596) da Ibnu majah (3125).

Wasu Malamai sun raunatashi saboda jahalar Abu ramlah, sunansa Ãmir, Al-kidaby yace: Hadisine mai rauni, Abu ramlah ba'a sanshi ba, *Ma'alimul Sunan (2/226).*

Zaila'iy yace: Abdul haq yace: Isnadinsa mai raunine, Ibun qaddaãn yace: illarsa shine jahalar abi ramlah, sunansa Amir ba'a sanshi ba saida wannan, ibnu Auun ya ruwaitoshi daka gareshi.Duba *Nasburrayah (4/211).*

Wadanda Sukace: Mustahabbice sun kafa hujjah da dalilai masu yawa, Mafi muhimmancin sune guda biyu.

Hadisin Ibnu Abbas Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Abubuwa uku Wajibaine akaina, akanku kuma Nafilane, *Wutiri, da Yankan layya, da Sallar walaha.)*

Ahmad ya ruwaitoshi (2050) da Baihaqy (2/467).

Hadisin Malamai na da da yanzu sun raunatashi.

Ibnu hajar yace: An ruwaitoshi daka Abiy janaba  Al-kalbi daka ikrimah, Abu janaba za'ifine, mudallasine, yana yin An-ana.

Malamai Sun raunata hadisin kamar *Ahmad da Baihaqy, da Ibnu Salah, da Ibnul jauzy, da Nawawi* da wasunsu.

*Talkeesul Habeer (2/45- 258).*

Hadisi na Biyu: Hadisin Ummu salamah Annabi Sallalahu Alaihi wasallam yace: ( Idan Goman farko na zhul-hijjah ya shiga wanda yake san yin layya, kada ya yanke farcensa ko gashinsa ko fatarsa) *Muslim (1977).*

Imamu Shafi'i yace: Wannan daliline akan layya ba dole bace, Duba *Al-majmu'u (8/386).*

Hadisan da suke nuna Wajabcin layya akwai matsala akansu, duk da wasu malamai sun kyautata wasunsu.

Haka hadisan da suka nassanta Mustahabbanci, ta bangaren isnadi sunfi tsananin rauni.

Abunda yake qar-fafa rashin Shar'antuwar layya sune Abu biyu:

@- Barranta Ta tun asali, matuqar wani dalili kubutacce daka cin karo bai zo ba, to lallai Asali shine rashin wajabci.

Kamar yanda Bin baaz ya bayyana acikin *fatawa dinsa (18/36).*

@- Zantukan sahabbai ingantattu da aka ruwaito daka Sahabbai, ya inganta daka *Abubakar da Umar* da wasunsu sun kasance basa layya, don tsoran kada Wasu mutane su dauka dole ce.

Kamar yanda Baihaqi ya ruwaito  acikin *Ma'arifatu Sunan  Wal-Ãsãar (14/16)  Ka sake duba Sunanul Kubra (9/444) .*

Nawawi acikin *Al-Maj-Mu'u (8/383)* yace: Zantukan da aka ambata daka Abubakar da Umar, Baihaqi ya ruwaitosu da Isnadi kyakyyawa.

Haitami yace: Dabarani ya ruwaitoshi acikin Kabeer mazajensa Ingantattune. Duba

*Mu'ujamul zawa'id (4/18) Albani ya Ingantashi acikin Irwa'u (4/354)..*

Mas'alar dai akwai sabani Abun lura tsakanin malamai.

Wanda sukace: Mustahabbice shine Abunda dalilinsu yafi bayyana agaremu.

Mesan Qarin bayanai saiya duba *Ahkamul Az-hiyyah Wal-zakah na Shaiek Usaimeen, Da Al-Mufassaal fy Ahkamul Azhiyyah.*

Wallau A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support