​BABU BAMBANCI TSAKANIN WIWI DA GIYA A HARAMCI​ ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Sunday, 6 August 2017

​BABU BAMBANCI TSAKANIN WIWI DA GIYA A HARAMCI​

​BABU BAMBANCI TSAKANIN WIWI DA GIYA A HARAMCI​


​Tambaya​

Assalamu Alakum.
Malam ina da tambaya kamar haka,shin tabar wiwi tana daukan dukkanin hukunce hukuncen da suka hau kan giya (barasa)ko kuwa akwai banbanci.Dafatan zanga amsan wannan tambaya a Zauren Fiqhu.nagode.


​Amsa​
Wa alaikum assalam,

 mutukar ta amsa sunanta na WIWI kuma tana bugarwa, tabbas za ta dauki dukkan hukunce-hukuncen giya na haramci.
Annabi s.a.w. yana cewa "Dukkan abin da yake sanya Maye giya NE,  kuma dukkan giya haramun ce" kamar yadda Nasa'i  ya rawaito a hadisi ingantacce,  wannan sai ya nuna haramcin shan WIWI da duk abin da yake sanya maye.

Allah ne mafi Sani.

​Amsawa​✍🏻

​DR. JAMILU YUSUF ZAREWA​

05/08/2017

Daga ​ZAUREN FIQHUS SUNNAH​
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support