Buhari zai yiwa 'yan Najeriya jawabi a ranar Litinin ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday, 19 August 2017

Buhari zai yiwa 'yan Najeriya jawabi a ranar Litinin

Ana sa rai da cewar shugaba Buhari zai yiwa kasa Najeriya jawabai a ranar Litinin daidai da 21 ga watan Agusta da misalin karfe 7:00 na safe .
A yau asabar 19 ga watan Agusta, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo gida Najeriya bayan fiye da kwananki 100 da ya shafe a birnin Landan yana jinya.

Buhari zai yiwa 'yan Najeriya jawabi a ranar Litinin

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa da manema labarai a safiyar yau Asabar kuma zai yiwa al'umma kasa baki daya jawabi a ranar Litinin 21 ga watan Agusta da misalin karfe 7:00 na safe.


Shugaba Buhari ya bar kasar nan ne a ranar 7 ga watan Mayu, inda ya mika ragamar shugabancin Najeriya a hannun mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin mukaddashi.
Adesina ya ce, ana sa ran zai dawo kasar nan a yau Asabar kuma zuwa safiyar ranar Litinin 21 ga watan Agusta da misalin karfe 7:00 zai yiwa 'yan Najeriya jawabai.
Ya kara da cewa, shugaba Buhari yana miko gaisuwa da kuma godiya ga duk 'yan Najeriya da suka dukufa wajen yi ma sa addu'a akan ya samu waraka tun daga lokacin da ya kwanta jinya.
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support