MENENE HUKUNCIN CINYE NAMAN LAYYA DUKA, KO SADAKA DASHI GABA DAYA? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Wednesday 30 August 2017

MENENE HUKUNCIN CINYE NAMAN LAYYA DUKA, KO SADAKA DASHI GABA DAYA?

*MENENE HUKUNCIN CINYE NAMAN LAYYA DUKA, KO SADAKA DASHI GABA DAYA?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Nassoshi Na shari'a sunyi nuni akan wajabcin yin sadaka da Wani abu na naman layyah, koda kadanne, Allah madaukakin sarki yace:

( Kuci daka naman layyarku, ku ciyar da Talakan daya kame bai roqa ba, da talakan daya roqa saboda buqata, saboda haka Allah ya Yassare muku ita danku zama masu godiya) Suraul Hajji aya ta (36).

Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Kuci naman layya, ku ajiye, kuyi sadaka) *Muslim (1971).*

Malaman da Sukace yin sadaka da Naman layya wajibine sune: *Shafi'iyyah da Hanabila,* Itace sahihiyar Magana Azahirin nassosin shari'a.

Wajibine sadaka da wani abu na naman wanda sunan sadaka zai gaskatu akansa, domin manufa shine yalwatawa miskinai,

Abisa Wannan idan mutum ya cinye naman layyar sa, duka wajibine ya siya yayi sadakar,

*Rauzatul dhalibeen da Umdatul mufteen (3/223).*

Kamar yanda Marudy ya fada acikin *"Al'insaaf (6/491)*.

Kamar yanda Buhty yafada acikin *kashshaful Qina'i (7/444).*

Kamar Yanda Shaik Usaimeen ya bayyana acikin *Maj-mu'u fatawa dinsa (25/132)*

Malamai Sunyi Sabani akan wajabcin cin wani abu daka cikin Naman layya,

Jamhur din malamai suna ganin cin wani Abu na naman layya mustahabbine, ba dole bane, wannan shine fatawar Manyan Mazhabobinnan guda hudu.

Wasu sun tafi akan wajabcin cin wani Abu daka cikin naman layya koda kadanne, saboda zahirin nassosin shari'a da sukai Umarni akai.

Nawawi yace:Cin naman layya mustahabbine ba dole bane, shine mazhabar mu da Malamai gaba daya, sai Abunda aka hakaito daka wasu magabata na wajabcin cin naman, saboda zahirin hadisin dayai Umarni aci wani abu daka layya, da fadin Allah madaukakin Sarki ( Kuci daka naman layya) Jamhur din malamai sun dora wannan umarni akan halacci da Mustahabbanci,

*Sharhin Sahihu Muslim (13/131).*

Ibnu qudama yace: da Mutum zaiyi sadaka da naman layya gaba daya, ko mafi yawan naman, ya halatta.

*Al-mugni (13/380)*.

Idan ka yanka raguna da yawa, ko wanne saika debi wani abu daka namansa kayi Sadaka dashi.

da Zaka yanka raguna goma ko akuyoyi ko tumaki, ko wanne daka cikinsu saika debi namansa kayi Sadaka dashi, mustahabbine kowacce dabba kaci wani Abu na naman dukkan dabbobin daka yanka.

Domin kowacce layya cin gashin kanta take..

Shi yasa da Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya soke abun hadayarsa saiyai umarni a debo masa wani kaso daka naman kowacce raquma.

Jabir dan Abdullahi Allah ya qara musu yarda yace: Sai muka nufi Abbatuwa Annabi ya Soke raquma talatin da Uku da hannunsa, sai ya bawa Aliyu ya yanka Abunda yai Saura.

Sannan yai Umarni akawo masa daka naman kowacce sai aka sanya atukunya aka dafa masa yaci namansu, yasha romonsu.

*Mualim (1218).*

Wannan yana nuna kowacce dabbar layya da'aka yanka tana da hukunci nata ita kadai.

saboda hakane yai Umarni akawo masa wani Abu daka kowacce taguwa.

Nawawi yace: acikin wannan akwai mustahabbancin cin hadayar nafila, da layyya.

Malamai Sukace: cin naman kowacce dabba daka yanka sunnah ne, cin yanka daya na kowacce dabba akwai wadatarwa, ka sanya atukunya don kowacce ya zama akwai romon nata naman.

*Sharhin Muslim (8/192).*

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support