​YA HALATTA NA SAYI KARE SABODA GADI A GIDANA ?​ ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday 10 August 2017

​YA HALATTA NA SAYI KARE SABODA GADI A GIDANA ?​


​YA HALATTA NA SAYI KARE SABODA GADI A GIDANA ?​

​Tambaya​

Assalamu alaikum. Dr. Mene ne hukuncin ajiye kare a gida saboda gadi? Allah muke roko ya kara wa Dr lafiya da basira Ameen.

​Amsa​
Wa alaikum assalam, Ya tabbata a hadisin Bukhari da Muslim cewa:  "Mala'iku ba sa shiga gidan da yake akwai hoto ko KARE a ciki.

A wani hadisin mai lamba ta: 2974 da Muslim ya rawaito Annabi s.a.w. yana cewa: "Duk Wanda ya rike KARE, in ba Karen noma ba ko farauta ko kiwo, to Allah zai tauye masa  manyan lada guda biyu a kowacce rana.

Da yawa daga cikin malamai sun yi kiyasin KAREN GADI akan wadancan nau'ukan guda uku da suka gabata, don haka ya halatta musulmi ya riki Kare saboda gadi in har akwai bukatar hakan.

Ba ya halatta a siyar da kare kowanne iri ne, saboda Annabi S.a.w ya hana cin kudin Kare a hadisin da Muslim ya rawaito kuma ya kira Shi da dauda.

Duk da cewa an halatta wadancan nau'ukan guda hudu saboda bukata saidai bai halatta a siyar da su ba, saboda Ka'ida sananniya a wajan malaman Fiqhu wacce take cewa:
ما جوز للحاجة لا يجوز أخذ العوض عليه

Idan mutun yana bukatar daya daga cikin wadanchan nau'uka na karnuka guda huɗu da suke halatta, kuma bai samu wanda zai ba shi kyauta ba,  ya halatta ya siya, Amma zunubin sayarwar yana kan wanda ya sayar tun da shi ne bai bayar ba, kamar yadda Ibnu Hazm ya fada a littafinsa na Muhallah 4/793, Ka'ida tabbatacciya a wajan malamai tana cewa:
ما حرم سدا للذريعة يباح للحاجة أو المصلحة الراجحة

Allah ne mafi sani.

​Amsawa​✍🏼

​Dr. Jamilu Yusuf Zarewa​
16/05/2017

Daga ​ZAUREN FIQHUS SUNNAH​
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support