*SHIN WANKAN JUMA'A WAJIBI NE!!!?*
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
*Zauren SA'ADATUL-MUSLIM*
.
الحمد لله رب العالمين والصلاة والسلام على رسول الله صلى الله عليه وسلم، وبعد السلام عليكم ورحمة الله
.
_'Yan uwa abokai ma'abota zauren Sa'adatul-Muslim na whatsapp jiya juma'a mun gabatar da shirin mu karu da juna kuma muka fitar da tattaunawar tamu akan cewa shin wankan juma'a wajibi ne ko kuma ba wajibi bane, kuma alhamdulillah mun samu amspshi daban-daban daga gareku masu fa'idantar wa da kuma soyuwa, ta bangaren maza mun samu amsoshi haka kuma ta bangaren mata mun samu amsoshi muna ma Allah ta'ala godiya da ya kasance mafiya yawan ku sun amsa wannan tambayar dai dai kuma muna rokon Allah ya saka maku da alkhairi, in shaa Allahu yanzu zamu takaita amsar wannan tambaya na cewa shin wankan juma'a wajibi ne ko kuma ba wajibi bane?_
.
_Zance na gaskiya itace dan uwa ko 'yar uwa abinda yafi cancanta a gareku shine kuyi wanka ranar juma'a lallai anaso dukkanin musulmi yayi wanka kafin yatafi masallaci domin yin sallar juma'a akwai hadisai masu yawa da suke nuna falala ga wanda yayi wanka ranar juma'a, amma dai lallai fa an samu sabanin malamai dangane da cewa shin wankan juma'a wajibi ne ko kuma ba wajibi bane, amma zancen da malamai suka rinjaya akansa sosai shine wankan juma'a ba wajibi bane sai dai mustahabbi ne kayi wanka shi yafi,_
.
_Dan uwa idan kaduba littafin Fiqhus-Sunnah zakaga tattaunawar malamai akan wannan matsalar zakaga kaulin da yafi rinjaye shine wankan juma'a ba wajibi bane wannan shine kaulin Imamu Shafi'i da Qurdubiy da Hafiz Ibn Hajar, haka idan kaduba Al-Mughniy na Ibn Qudamah 5009/704 zakaga sa6anin malamai akai amma zancen da yafi rinjaye shine wankan juma'a ba wajibi ne sai dai mustahabi ne wato idan kayi ka kyautata sosai da sosai wannan shine kaulin Imam Tirmidhiy da Auza'i da Imamu Ath'thauriy da Maalik da Shafi'i da Ibn Munzir da Ibn Abdil'barri, da wasu daga cikin magabata, wanda ya duba zaiga hujjoji masu yawa akan hakan in shaa Allah, don haka wankan juma'a ba wajibi bane amma dai dan uwa kayi wanka shu yafi domin kuwa mustahabbi ne,_
.
_'Yan uwa abokan aiki da iyayen mu da kannemu Allah ya sakanka maku da alkhairi, sai kuma wani lokacin idan muka bijiro maku da wata tattaunawar, Alhamdilillah Allah yayi mana jagoranci,_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp
KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.

0 comments:
Post a Comment