DAN UWA NA YA MUTU ANA BINSHI AZUMIN RAMADAN SABODA RASHIN LAFIYA ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Monday, 14 August 2017

DAN UWA NA YA MUTU ANA BINSHI AZUMIN RAMADAN SABODA RASHIN LAFIYA

```DAN UWA NA YA MUTU ANA BINSHI AZUMIN RAMADAN SABODA RASHIN LAFIYA```
〰〰〰〰〰〰〰〰〰〰
_*Zauren SA'ASATUL-MUSLIM*_
.
_TAMBAYA:- السلام عليكم ورحمة الله Malam inada tambaya kamar haka Dan uwanane yadade Yana jinya amma wannan axumin da ya wuce jikin ya matsa baiyi ko daya ba yau Allah yayi mai rasuwa malam yanxu axumin da bayyi ba xa'a rama masa ko xa'a ciyar masa  Allah yakarawa malam lfy da wadatan xuci_
.
_AMSA:- وعليكم السلام ورحمة الله  Amin godiya muke da wannan addu'ar kuma muna addu'ar Allah ta'ala yayi masa rahama Allah yasa al'jannah ta kasance makoma a gareshi Allah yasanya mutuwa ta zama hutu a gareshi mu kuma idan mutuwa tazo mana Allah yasa mu mutu muna masu imani acikin zukatan mu,_
.
_Dan gane da wanda ya mutu alhali baiyi azumin ramadan ba saboda rashin lafiya ko kuma yana a halin tafiya, to asali dama Allah ta'ala bai wajabta masu yin azumi ba matukar wadannan dalilan sun tabbata akansu domin Allah cewa yayi "Wanda ya kasance daga cikin ku majinyaci ko kuma yana a halin tafiya to ya ciko su acikin wasu kwanakin na daban"  kenan Allah ya dauke ma wanda yake jinya yin azumi  acikin watan ramadan azumi har sai mutum ya warke,_
.
_To shi kuma wannan dan uwa naki Allah yajikansa yayi jinya acikin watan ramadan kuma saboda yana tunanin zai warke sai bai ciyar ba yana jira idan ya warke sai ya rama (Allahu Akbar) kawai sai Allah ta'ala ya aiko da mala'ika aka amshi ranshi wato bai rama wannan azumi ba to yanzu abinda zakuyi shine,_
.
_Zaku ciyar masa ne ba azumi zakuyi ba domin anyi sa6ani na malamai amma zancen da yazo yace kuyi masa azumi gaskiya bashi da wani karfi ciyarwa kadai zakuyi masa in shaa Allah,_
.
_Ibnu Qud'amah rahimahullah acikin Al'mughni ya kawo wannan a matsala ta 2084 yace,  "Abinda yake wajibi a gareku shine zaku ciyar da miskini a kowwace rana, wannan shine zantukan malamai akan wannan matsala, kuma an samu ruwaya daga Ummuna Ai'sha da Ibn Abbas Allah ya kara masu yarda, da Imam Malik da Laithi da Au'za'i da Imamus Thauri da Shafi'i da Hasan dan Hayya da Ibn Ulayyah da Abus Thaur duk sunce ciyarwa za'ayi (Al-Mughni 5009/1111)_
.
_Amma wannan ya takaita ne akan azumin ramadan kadai, wanda kuwa yayi bakance na azumi har ya mutu baiyi wannan azumin ba to wannan azumi wajibi ne waliyyansa su rama masa, wannan shine kaulin Shafi'i rahimahullah da Ibn Abbas radiyallahu Anhuma"  (Al-Mughni 5009/1111) Allah yasa mudace_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp


Karku manta da gayyato mana abokananku Mun gode





Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support