- An yanke maki da jami'a da manyan makarantu zasu dauka domin a saka yara a makaranta
- Dalibai sun dade suna jiran wannan maki mai kankanta
- Maki 120 ne aka kayyade ga jami'a, 100 ga kwaleji da poly
An fidda sakamakon jarrabawar JAMB tun watan Afrilu, sai dai ba'a yanke maki mafi kankanta ba a wancan lokacin, sai yau hukumar ta JAMB ta fidda.
Ta dai yanke maki 110 a matsayin maki mafi karanci ga kwalejin kimiyya da fasaha, da poly-poly, sannan maki 120 ga jami'oin jihohi da tarayya.
YANZUNNAN: Hukumar JAMB ta fidda mafi kankantar maki da jami'o'i zasu yanke domin
shiga jami'a da manyan makarantu a bana
Wannan na nufin duk dalibi da yaci wannan maki ko sama yana iya saka rai zai fara karatun jami'a a bana. Hukumar kuma tace bazata hana jami'o'i da Kwaleji kayyade ko kara yawan makin ba, domin kara wa makarantunsu tagomashi da yara masu hazaka.
Mafi akasarin yaran da suka zauna wa jarrabawar sun ci jarrabawar da maki da yafi 150. Hakan na nuin yara zasu fara karatu a makarantu cikin sauki.
A baya kam ba'a samun shiga jami'a cikin sauki, wanda kuma hakan ya kashe wa samari da yawa jiki wajen neman ilimin boko, sun koma zaman banza da shaye-shaye.
KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.

0 comments:
Post a Comment