LABARIN UMMU WARAQAH (RA) ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday, 19 August 2017

LABARIN UMMU WARAQAH (RA)

LABARIN UMMU WARAQAH (RA) 
**********************************
Akwai wata dattijuwa daga cikin Matan Sahabbai ana kiranta da suna Ummu Waraqah. Tana da ilimi sosai dan tun azamanin Manzon Allah (saww) ta haddace Alqur'ani mai girma. 

Watarana tazo tace ma Manzon Allah (saww) cewa tana so yayi mata izini ta samu ladani ya rika yin kiran sallah agidanta. Tana yiwa mutanen gidanta limancin sallar taraweehi. Ita ce Mace ta farko wacce tayi ma Mata limanci. 

Ta kasance ita mace ce mai son neman kusanci da Allah ta kowacce fuska. Ga kuma yawan ibadah da tsaiwar dare da nafilfin sallah da Azumi. 

Bayan Manzon Allah (saww) ya dawo daga Yaqin badar, sai Ummu Waraqah (ra) tazo wajensa tace masa "Ya Rasulallahi ina so kayi mun izini in rika binka wajen Yaqi. Ina yin jinyar wadanda suka ji rauni. Watakil Allah ya azurtani da samun Mutuwar Shahadah".

Sai Manzon Allah (saww) yace mata "Kiyi hakuri ki zauna agidanki. Lallai Allah zai azurtaki da samun shahadah".

Tun daga wannan ranar sai sunanta ya chanza abakin sahabbai, Suna kiranta da suna "SHAHEEDAH" (Wato Shahidiyah) tunda sunji bisharar samun shahadarta daga bakin Manzon Allah (saww).

Shi kansa (saww) ya kasance yakan ziyarceta. Idan zai tafi yakan ce ma Sahabbansa "KU TASHI MU ZIYARCI SHAHIDIYA".

Ummu Waraqah tana da wasu Bayi guda biyu da suke yi mata hidima. Watarana ta kirasu tayi musu karamci tace musu "Duk ran da na mutu to kun zama 'Yantattu".

To shikenan watarana a zamanin Khalifancin Sayyiduna Umar bn Al-Khattab (ta) Ummu Waraqah tana cikin barci sai bayin nata suka zo suka danne mata Wuya da katifarta har sai da suka kasheta, sannan suka fita suka tsere. 

Yayin da Sayyiduna Umar bn Khattab (ra) yaji labarin rasuwarta, sai yayi Kabbara sannan yace : "Kasheta sukayi! Lallai Manzon Allah (saww) yayi gaskiya!"

Sannan ya sanar da cewa duk wanda ya gansu ya kamo masa su. Nan da nan kuwa aka kamosu aka kawosu gabansa. Sai yayi umurni aka ratayesu. 

Sune farkon wadanda aka ratayesu a Musulunci. 

Imamu Ahmad da Abu Dawud da Baihaqiy duk sun ruwaito.

Ya Allah ka Qara yardarka bisa Hafizah Sahabiya, Ummu Waraqah tare da dukkan Sahabban Annabinka (saww) Maza da Mata. Aameeen. 

Daga Zauren Fiqhu (18-02-2017 20-05-1438).

DON GIRMAN ALLAH (SWT) KADA WANI YA GOGE KOMAI ACIKIN RUBUTUN NAN.

Don samun wasu Fa'idodin ku rika ziyartar babban shafinmu www.zaurenfiqhu.com ko kuma shafinmu na facebook www.facebook.com/zaurenfiqhu ko shafinmu na Twitter @zaurenfiqhu




Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support