Namiji !!! - zauren fiqhu ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Friday 11 August 2017

Namiji !!! - zauren fiqhu


.                          ​​NAMIJI:​​

Wata rana a makarantar manya malamin koyar da sanin halayyar dan Adam ​(Psychology),​ ya shiga aji yace "yau zamu yi wani wasa", "me? wasa".

Malam yace a cikinku wa zai fito gaban allo a fara da Shi?

Sai wata daliba Salma ta fito, Sai malam yace ta dauki alli ​(chalk)​ ta rubuta sunan mutane 30 masu muhimmanci a rayuwarta, Salma ta rubuta dangi, kawaye, abokan karatu da makwaftanta.

Sai malam yace ta goge 3 wadanda basu da muhimmanci sosai a wajenta, Salma ta goge suna 3 na abokan karatunta.

Sai malam yace ta kara goge 5 marasa muhimmanci, Salma ta goge makwaftanta, Malam yayi ta umartarta tana gogewa har sai da ya rage sunaye 4 ka dai sune:-
1. Babarta
2. Babanta
3. Mijinta
4. Ɗanta 1 data haifa.

Gaba dayan dalibai sai suka natsu sun gane cewa wannan ba wasa bane kamar yanda Malam ya fada da farko, yazo musu ne da wani darasi mai muhimmanci.

To! Sai malam ya kalli Salma yace ta kara goge 2 daga sunayen nan da suka rage, wannan zabin fa yana da wuya, Salma tayi jimmm! Hannunta yana rawa ba'a son ranta ba idonta ya cika da kwalla ta goge sunan Babarta da Babanta.

Sai malam yace ta kara goge 1, Sai Salma ta saka kuka ta goge sunan Ɗanta 1 Tilo Sai malam yace ta koma wajenta ta zauna.

Bayan wani ɗan lokaci sai malam yayi tambaya, yace:- " me yasa ta bar mijinta"?

Yace: Iyaye fa sune suka kawo ki duniya suka raine ki har kika girma, Ɗanki kuma ke kika yi cikinsa kika sha wahalar laulayin cikin kika haife shi, kika raine shi, kuma da Iyaye da Da ba zaki iya sake wadansu ba, amma miji ko yaushe zaki iya chanja wani.

Aji akayi shiru ana jiran amsar Salma, Salma cikin nutsuwa da sanyin murya tace:-

"Wata rana iyayena ina tare dasu suka dauke ni suka kaini gidan miji, idan na kawo musu ziyara sai su tambayeni, "lafiya"?

Idan yayi min laifi na taho gida sai su kira shi suyi ta bashi hakuri, suce na tashi na koma gidansa".

Ɗa na kuma wata rana zai barni idan ya girma zai mai da hankali kan sana'arsa da hidimar iyalinsa, Mutum 1 wanda zai kare rayuwarsa tare da ni shine ​MIJINA,​ kuma...... Kafin ta kara magana sai dalibai suka dauki tafi gaba daya saboda ta fadin gaskiyar yanda rayuwa take.

Sai malam yace:- "Gaskiya ne, Allah ya sanya aure a tsakanin Miji da mata ya zama dangantaka ta tsowon rayuwarsu, Ko yaushe ka girmama abokin rayuwarka (Miji ko Mata).

Allah ya sanya Miji da Mata su zama Abu 1 Kamar yanda yazo a cikin Al- qur'ani mai tsarki, Allah yana cewa:- "yana daga cikin ayoyinsa ya halitta muku matayenku daga jikinku, don ku rayu dasu, ya sanya a tsakaninku soyayya da jin kai, hakika a cikin wannan akwai aya ga ma'abota tunani".

Don haka ku (Ma'aurata) ku zaku saka wannan dangantaka ta zama sama da kowace dangantaka a duniyar nan Kafin mutum yayi aure Allah da Manzansa sune a farko sannan dangi, bayan kayi aure Allah da Manzansa suna farko Miji/ Mata sune na 2 Sannan dangi. Ma'aurata ya zama wajibi ku baiwa Aurenku abinci ya girma yayi karfi, abincin kuwa shi ne bin dokokin Allah, Gaskiya, rikon amana, Hakuri, Zaman lafiya Soyayya da Nishadi.

​FATAN ALKHAIRI GA DUK MASU AURE





Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support