A jawabin maraba da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ma yan Najeriya a ranar Litinin 21 ga watan Agusta ya tabo wasu muhimman lamurran da suka shafi kasa.
NAIJ.com ta kalato ma masu karatu wasu muhimman batutuwa guda 7 da shugaban yayi a yau:
1- Babu tababa ga hadin kan Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar ma yan Najeriya a jawabinsa cewa ba za’a raba Najeriya ba, ba a karkashin shugabancisa ba. Buhari yace ba zai yiwu wasu mutane da basu san ciwon kansu ba, su tada rikici, kuma su bar wasu daban da sadaukar da rayukansu don kawo zaman lafiya.
2- Yancin Yan Najeriya
Buhari a jawabinsa ya tabbatar da yancin kowane dan Najeriya, inda yace duk wani dan Najeriya nada ikon gudanar da harkokinsa a ko ina a fadin kasar nan ba tare da tashin hankali ba.
Buhari
3- Korafe korafen yan Najeriya
Shugaban kasa ya jadda cewar har yanzu akwai matsaloli daban daban da suke addaban da dama daga cikin yan Najeriya daga kowane bangare, don haka kowane bangaren kasar nan nada ikon ayyana matsalolinta, tare da lalubo hanyoyin magance su cikin zaman lafiya da juna.
4- Hadin kan yan Najeriya
A cikin jawabin nasa, shugaba Buhari ya nanata muhimman zaman tare a tsakanin yan Najeriya, inda yayi nuni da cewa yawancin Najeriya sun gamsu da tabbacin zaman mu a dukunle, kasa daya al’umma daya shi yafi alheri ba a ware ba.
5- Tsaro
Shugaba Buhari ya umarci hukumomin tsaro da kada su yi kasa a gwiwa a kokarin da suke yi, kuma ya shwarcesu dasu dage tare da jajircewa akan nasarorin da suka samu a watanni 18 da suka gabata.
Buhari ya jadda manufar gwamntinsa na baiwa hukumomin tsaro gudunmuwar da suke bukata don ganin bayan dukkanin wasu kungiyoyin ta’addanci, masu garkuwa da mutane, rikicin kabilanci da matalsar manoma da makiyaya.
6- Manufofin gwamantin sa
Shugaba Buhari bai karkare bayanansa ba har sai daya maimaita manufofin gwamnatinsa, musamman akan matsalolin da suke addabar kasar nan, ciki sun hada da:
- Habbaka tattalin arziki
- Inganta tsaro da tabbatar da zaman lafiya
- Daidaita al’amuran siyasar kasar nan
7- Alwashi
Daga karshe shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dau alwashin ganin ya cika dukkanin manufofin gwamnatinsa, tare da tabbatar da cigabansu.

0 comments:
Post a Comment