Duniya makaranta !! (fitowa ta 35) dr.mansur ibrahim sokoto ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday 5 August 2017

Duniya makaranta !! (fitowa ta 35) dr.mansur ibrahim sokoto

DUNIYA MAKARANTA

Fitowa ta 35

176. Shan toka da tsare gida sukan sa a kosa da kai. Yawan raha da sakin jiki kan jawo maka wulakanci. Ka lizimci tsakiya a komai, shi ne alheri.

177. Gaskiya ta fi tasiri idan aka sha wahala a kan ta. Sirri ya fi dadin ji idan aka inganta boye shi.

178. A kan pillow Sarki yake kwana. Haka shi ma talaka. Amma babu wanda zai ji dadin bacci sai wanda yake da kwanciyar hankali.

179. Mutakabbiri kamar mutum ne a kololuwar dutse; yana kallon mutane a kasa, suna kallon sa dan karami.

180. Ba dole ne ka fadi duk abin da ka sani ba, amma yana da kyau ka san duk abin da kake fadi.

Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

10/11/1438
3/8/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support