Wanene ibn Taimiyya (fitowa ta 3) ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Wednesday 16 August 2017

Wanene ibn Taimiyya (fitowa ta 3)

*_WANENE IBN TAIMIYYAH_*
➖➖➖➖3⃣➖➖➖➖
★ Ga masu bukatar page dinmu sai su shiga wannan link din suyi like  https://free.facebook.com/إبن-تيمية-رحمه-الله-136792630155923/?_rdr
.
_Mun tsaya a inda mukace Ibn Taimiyyah nan take ya rurrusa aqidun da suka zame ma musulunci tsutsar goro ta hanyar rubuce-rubucen sa da wa’azozan sa da karantarwar sa ya kece raini a wajen wargaza aqidun Yahudawa dana ‘Yan mishan Yayi fad'a da qungiyoyi mabiyan son zuciya irin mulhidai da zindiqai da ‘yan Shi’ah da wadanda suka wuce wuri a Sufanci. Yayi kira ga koma ma littafin Allah da Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba tare da ta’assubanci ga wani mutum ba ko qungiya ko mazhaba ba._
.
_Sa’annan ya kira sarakuna da talakawa zuwa ga yaqar kafirai wad'anda suka keta hurumin musulmi, musamman dai Tattar. Ya kuma fita yayi yaqi a matsayin daya daga cikin sojoji, Tare da haka kuma Ibnu Taimiyyah ya kafa wata makaranta da Allah ya yawaita almajiranta tun daga wancan zamani har zuwa yau, kuma tana cigaba da bunqasa har a nad'e qasa, Wannan makaranta tasa tana mutunta magabatan Sahabbai da Tabi’ai da wad'anda suka biyo bayansu, da shugabannin mazhabobi, tana kuma la’akari da ra’ayoyansu da fatawoyinsu baki d'aya. Tana kuma rinjayar da nassi ingantacce idan ya zo daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a kan maganar kowa kome darajarsa, Wannan makaranta dai tana da d'aruruwan littafai da dubaiban malamai a cikinta, Dukkanin su suna jingina kansu ga Sunnah da biyar magabata baga shi Ibnu Taimiyyah d'in ba,_
.
*JARABAWA A RAYUWAR IBN TAIMIYYAH*  _Jarabawar Da Ibnu Taimiyyah ya Gamu da Ita Yana da wuya Allah ya d'aukaka wani bawansa ba tare da ya gamu da wasu jarabawoyi ba a rayuwarsa, Wannan ita ce sunnar Allah ga Annabawa da malamai mutanen kirki, Shehun musulunci ya gamu da jarabawoyi da dama a sakamakon jihadinsa na makami da na alqalami wad'anda suka dagula masa jin dad'in rayuwa Zamu fad'i wasu daga cikinsu a taqaice kamar yadda suka zo a tarihinsa daga littattafai da dama_
.
_A shekarar 696H ya gamu da qyashin abokan tafiya, malamai, wad'anda suka d'auki littafinsa Al-Fatwal Hamawiyyah suka kai qararsa dashi a wurin mahukunta Sun bi duk hanyoyin da suke iyawa wajen murd'a maganarsa da bata irin ma’anar da suke so su jingina masa A wannan lokaci sarki Saifuddin Jagan ya goyi bayan Ibnu Taimiyyah, ya kuma husata da wad'anda suka kafa adawa da shi. Don haka wannan jarrabawa ba ta dade ba ta kuranye._
.
_A shekarar 705H lokacin da farin jinin Ibnu Taimiyyah ya gama bayyana, bayan an ga rawar daya taka a yaqin da akayi da Tattar, har kuma ya samu kusanci da hukuma abin daya bashi damar sa a kawar da wasu 6arnace-6arnace Nan take sai qurjin hassada ya sake 6allewa a zukatan wasu malamai daga cikin sufaye. Sai wani malami da ake kira Nasrul Mambiji da wani malami bamalike ana ce masa Ibnu Makhluf suka tafi hedikwatar sarauta da ke qasar Masar suka kai qarar Ibnu Taimiyyah suna tuhumar sa da gur6ata aqidun jama’a. Suka kafa hujja da littafinsa na Al-Aqidatul Wasid'iyyah. Anan ma sarki ya bada umurni aka zaunar dashi tare da manyan malamai inda aka karance littafin nasa, daga qarshe kuma aka barrantar dashi daga sa6a ma magabata. Sai ma a wannan karon ya samu takardar yabo daga Sarkin Musulmi, zamu dakata anan mu hadu a rubutu na gaba_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.

Karku manta da gayyato mana abokananku a wannan shafin mun gode
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support