HATTARA DAI KOREN MACIJI ACIKIN CIYAWA! Zauren fiqhu ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday, 31 August 2017

HATTARA DAI KOREN MACIJI ACIKIN CIYAWA! Zauren fiqhu

HATTARA DAI KOREN MACIJI ACIKIN CIYAWA!
***********************************************
Daga cikin dukkan ni'imomin da Allah yake yiwa bayinsa, bayan imani dashi da kuma Soyayyar Annabinsa (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) babu kamar Ilimi da kuma aiki dashi.

Babban abun farin ciki ne yadda awannan zamanin zaka ga Qananan yara sun haddace Alqur'ani, sun haddace litattafai na hadisai, sun haddace Seerah nai yawa, Kuma daidai gwargwado ana bada himma wajen ibadah.

To amma inda gizo yake saqar shine wajen aiki da abinda aka koya, da kuma kyautata dabi'u acikin kowacce Mu'amala.

Zaka ga Matashi mai ilimi, mai kyawawan tufafi, kullum yana masallaci, ga siffah irin ta masu tsoron Allah. Amma zuciyarsa "Wayam" babu cikakken tsoron Allah ko muraqabah da Ubangijinsa.

Kwanan nan wata baiwar Allah take koka min wata matsala da taso ta afka!. Domin ita dai yarinya ce mai kulawa da addini, ga kuma ilimi daidai gwargwado. Kuma burinta ta samu mutum mai addini mai tsoron Allah amatsayin miji gareta.

Kwatsam sai wasu Malamai suka zo Makarantarsu sukayi musu Lekchochi akan addini. Har ma wani daga cikin Maluman ya kyalla ido ya ganta yace yana so. Ya karbi lambar wayarta kullum yayi mata Text. Ayoyin Alqur'ani da hadisai da sauransu.

Ana haka har dai yaje gidan su yarinyar yayi gaisuwa, Ya nemi izinin iyayenta game da neman aurenta.. Kuma suka amince masa (Saboda la'akari da siffofinsa).

Amma tun aranar da ya koma gida sai ya turo mata text mai tada hankal kamar haka "DARLING, TUNDA NAZO GIDANKU NAYI GAISUWA AI MUN ZAMA DAYA". ( A karshen maganar dai yace wai yana so ta amince su rika yin chatting irin wanda zai sa mutum yayi wanka!!).

Ta nuna masa ita bata gane me yake nufi ba.. Sai yace wai shi sha'awa ce ke damunsa, don haka yake neman agajinta, ta rika yi masa hotuna tana tura masa, ko kuma su rika yin "SEX CHAT".

Tun daga ranar taji kamar zazzabi ya rufeta, ta gujeshi ta goge lambar wayarsa ma. Kuam tace masa har abada kar ya sake kulata..

To wallahi irin haka tana yawan faruwa atsakanin matasa. Kuma Allah ne ka'dai  yasan yawan 'Yan matan da suka rasa Budircinsu ta dalilin irin wadannan Shaitanun Samarin (KURA DA FATAR RAGO).

Duk yadda kike son saurayi, kada soyayyarsa tasa ki biye masa ku rika sa'ba ma Allah. Idan kikayi haka kinci amanar Allah da Manzonsa (saww) kuma kinci amanar Mahaifanki da 'yan uwanki da danginki (Kin shigo musu da alfasha cikin zuriyarsu).

'Yan Mata kuyi hankali da irin wadannan samarin domin kuwa sunfi hatsari, Kuma sun fi wuyar ganewa fiye da "KOREN MACIJI ACIKIN CIYAWA".

Kiyi hankali kada saurayi ya mayar dake "KARUWAR GIDA". Ya kwashe miki albarkar rayuwarki! Ya janyo miki asarar duniya da lahira, da zubewar mutunci agun Allah da bayinsa.

NASIHA CE DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (29-08-2017 07-12-1438).


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support