​MUTUM NE YA SIYO HATSI, BAYAN YA SIYO, SAI FARASHIN HATSIN YA TASHI, SHIN YA HALASTA YA QARA KUDIN KO KUWA ZAI SAYAR A YANDA YA SAYO?​ ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday, 10 August 2017

​MUTUM NE YA SIYO HATSI, BAYAN YA SIYO, SAI FARASHIN HATSIN YA TASHI, SHIN YA HALASTA YA QARA KUDIN KO KUWA ZAI SAYAR A YANDA YA SAYO?​

​MUTUM NE YA SIYO HATSI, BAYAN YA SIYO, SAI FARASHIN HATSIN YA TASHI, SHIN YA HALASTA YA QARA KUDIN KO KUWA ZAI SAYAR A YANDA YA SAYO?​

​Tambaya​

Assalamu Alaikum warahamatullah

malam,mtum ne ke sana'a irin    su shinkafa,mai,wake da sauransu ,toh  sai ya siyo su a farashin da yake siyarwa,ana haka sai farashi ya hau, toh zai sayar a farashin daa ne kokuwa zai qara ne ya  cigaba da siyarwa?
.
.
​Amsa​


Wa alaikumus salam  Shari'ar musulunci ba ta qayyade ma dan kasuwa nawa zai sayar da kayansa na kasuwanci ba, sai dai Annabin rahama (SAW) ya yi addu'a ga dan kasuwa ya ce: "Allah yayi rahama ga dan kasuwan da zai saro da sauqi, ya sayar da sauqi"
A saboda haka; babu wata tanadaddiyar doka a shari'a da ta iyakance ma dan kasuwa yadda zai saida kayansa da ya saro, sai dai ya tausaya ba tare da ya cutar da kansa ba.
A kan haka; ya ga dama ya cigaba da saida tsohon akan farashin da, har ya qare, sannan ya tada farashin, ko kuma ya canza farashin kafin qarewar tsohon don in yaje sari yanzu zai sayo da tsada.

Imam Ibn Hazm ya fada a cikin"Almuhalla": ​Ba  Wanda ke da ikon qayyade ma dan kasuwa yadda zai sa farashin kayansa; hatta gwamnati​

Amma Shaikhul Islam Ibn Taymiyyah ya ce: ​Idan gwamnati ta fahimci yan kasuwa na wasa da farashi;to ya halasta ta qayyade farashi​

Wallahua'alam.


​Amsawa​✍

​Malam Basheer Lawal Muhammad Zaria​

07/08/2017

Daga ​ZAUREN FIQHUS SUNNAH​
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support