Meye hukuncin matane biyu su kwana a bargo daya ?? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday, 5 August 2017

Meye hukuncin matane biyu su kwana a bargo daya ??

​​​Assalamu alaikum
Meye hukuncin mutane biyu su kwana a bargo daya.??​​​



​​AMSA:​​
*******

وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،


Amsar wannan tambaya tana a karkashin wannan hadisi na ​Abdullai ibn Amr ibn al-Aas (radiyallahu anhu).​

​​​عن ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺑﻦ ﺍﻟﻌﺎﺹ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ : ﻗَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ: ﻣُﺮُﻭﺍ ﺃَﻭْﻟَﺎﺩَﻛُﻢْ ﺑِﺎﻟﺼَّﻠَﺎﺓِ ﻭَﻫُﻢْ ﺃَﺑْﻨَﺎﺀُ ﺳَﺒْﻊِ ﺳِﻨِﻴﻦَ ﻭَﺍﺿْﺮِﺑُﻮﻫُﻢْ ﻋَﻠَﻴْﻬَﺎ ﻭَﻫُﻢْ ﺃَﺑْﻨَﺎﺀُ ﻋَﺸْﺮٍ ﻭَﻓَﺮِّﻗُﻮﺍ ﺑَﻴْﻨَﻬُﻢْ ﻓِﻲ ﺍﻟْﻤَﻀَﺎﺟِﻊِ.​​​
​​(ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ‏(495)​​ ​ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ "ﺻﺤﻴﺢ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ"​

​An karbo daga ​Abdullai ibn Amr ibn al-Aas (radiyallahu anhu)​ yace; ​Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam)​ yace; Ku umarci 'ya'yanku da suyi sallah idan sunkai shekara bakwai. Kuma Ku dakesu Idan sunkai shekara goma (basa yin sallah), kuma ku rarraba su a makwancinsu (a raba musu shinfida idan sun kai shekara goma).​
​​​(Abu Dawuda,  495). Albani ya inganta shi a Sahih Abi Dawuda.​​​


​​​ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﻮﻭﻱ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ:
ﻻ ﻳﺠﻮﺯ ﺃﻥ ﻳﻀﺎﺟﻊ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﻭﻻ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻭﺍﺣﺪ ﻓﻲ ﺟﺎﻧﺐ ﻣﻦ ﺍﻟﻔﺮﺍﺵ ، ﻭﺇﺫﺍ ﺑﻠﻎ ﺍﻟﺼﺒﻲ ﺃﻭ ﺍﻟﺼﺒﻴﺔ ﻋﺸﺮ ﺳﻨﻴﻦ ﻭﺟﺐ ﺍﻟﺘﻔﺮﻳﻖ ﺑﻴﻨﻪ ﻭﺑﻴﻦ ﺃﻣﻪ ﻭﺃﺑﻴﻪ ﻭﺃﺧﺘﻪ ﻭﺃﺧﻴﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﻀﺠﻊ.​​​
​​"ﺭﻭﺿﺔ ﺍﻟﻄﺎﻟﺒﻴﻦ ‏(7/28)"​​

​Imam Nawawi (rahimahullah)​ yace:
Baya halatta ga namiji ya kwanta tareda namiji (a shimfida guda), ko kuma mace ta kwanta tareda mace (a shimfida guda), koda dayansu yana a gefe daya na shimfidar. Idan yaro ko yarinya suka kai shekara goma, ya zama wajibi a raba yaron (a shimfida) tsakaninsa da tsakanin Mamarsa, Babansa, yar uwarsa (kanwa ko yayarsa), da dan uwansa a wajen barci. (Dole ne ya rika kwana a shifidarsa shikadai).
​​Rawdatul taalibeen, 7/28).​​


Saboda haka bai halatta mutum biyu su kwana a shimfida guda idan shekarunsu sun kai goma (10).
🔒Namiji bazai kwanta shimfida daya da wani namiji ba.
🔒Namiji bazai kwana da wata mace wacce ba matarsa ba a shimfida daya. Wannan haramun ne.
🔒Mace bazata kwana da wata mace ba a shimfida daya.
🔒Mace bazata kwana a shimfida daya da wani namiji wanda ba mijinta ba.



والله أعلم،

***********************************


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


​​🌙Tambayoyin​​ ​​Musulunci🌙​​
            ​​WhatsApp​​ ​​Group​​
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support