TUFAFIN MANZON ALLAH (SAWW).
************************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
Salatin Allah da Amincinsa su tabbata ga Jagoran Annabawa da Manzanni Shugabanmu Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa inuwar al'ummah, da Sahabbansa Madaukaka.
Yau muna tare da Daliban Zauren Fiqhu 1-3 kuma in sha Allahu zamu yi takaitaccen bayani ne game da siffar tufafin Ma'aikin Allah (saww) kafin nan gaba ka'dan mu fadada bayanai in sha Allahu.
Tunda magana za'ayi akan tufafinsa (saww) dole mu fara da hadisan cikin gida. Wato hadisin da Abu Dawud da Tirmidhiy suka ruwaito daga Nana Ummu Salamah (rta) tana cewa :
"YA KASANCE RIGA ITA CE MAFI SOYUWAR TUFAFI AWAJEN MANZON ALLAH (SAWW)".
(Sunanu Abi Dawud hadisi na 4025, Sunanut Tirmidhiy hadisi na 1762).
Abu Juhaifah (ra) yace "Naga Bilalu (ra) yana kiran sallah yana jujjuyawa, Bakinsa yana bin nan da chan, Yatsunsa suna cikin kunnensa. Kuma Manzon Allah (saww) yana sanye da wata kar Alkyabba wacce aka yita daga jemammiyar fata...".
(Bukhary hadisi na 5476, Muslim hadisi na 2079).
Kuma hadisai ingantattu sun tabbatar mana da cewa Annabi (saww) yakan sanya tufafi irin na gida, kuma yakan sanya irin wanda ake kawowa daga sauran garuruwan Larabawa kamar su Sham, Yemen da sauransu. Hakanan yakan sanya irin wadanda ake kawowa daga Qasashen Rum ma.
Kuma duk da cewa yana sanya tufafi koraye ko jajaye, to amma fararen tufafi ne suka fi soyuwa agareshi kamar yadda hadisai da dama suka zo da Umurni daga gareshi (saww) :
Hadisi daga Sayyiduna Samurah bn Jundub (ra) yace Manzon Allah (saww) yace "INA KWADAITAR DAKU WANNAN TUFAFI FARARE. RAYAYYUNKU SU RIKA SANYASHI, KUMA KU RIKA YIWA MAMATANKU LIKKAFANI DASHI. DOMIN YANA DAGA MAFI ALKHAIRIN TUFAFINKU".
(Mustadrak na Hakim hadisi na 7375).
Hakanan akwai hadisin Ibnu Abbas (ra) yace Manzon Allah (saww) yace : "KU RIKA SANYA FARARE DAGA TUFAFINKU DOMIN ITA CE MAFI ALKHAIRIN TUFAFINKU, KUMA KU YIWA MAMATANKU LIKKAFANI DASHI".
(Mustadrak na Hakim hadisi na 1308. Sunanut Tirmidhiy hadisi na 994. Mukhtarus Sihah juzu'i na 1 shafi na 167).
Abu Eisa (Imam Tirmidhiy) yace "(Fararen tufafi) din nan shine abu mafi soyuwa awajen Ma'abota ilimi.
Ibnul Mubarak kuma yace "Abinda yafi soyuwa agareni shine ayi ma mutum likkafani da tufafin da ya kasance yana yin sallah dasu".
Imamu Ahmad da Is'haq (rah) sun ce mafi soyuwar tufafi agaremu shine ayiwa mutum likkafani da fari, Domin anfi so a kyautata likkafanin mutum".
Akwai riwayoyi daga Annabi (saww) game da sanya fararen tufafi a Muhimman ranakun Eidi ko Juma'ah. Hakanan a mafiya yawan lokutansa tafi sanya fararen tufafi din tun daga rawani har riga da kwarjalle da alkyabba.
Kuma daga cikin tufafinsa yakan yafa Mayafi akan kafadunsa, kuma yakan sanya kwarjalle (Wani abu ne kamar zani). Kuma yana yin rawani. Yakan saku jelar rawanin atsakanin kafadunsa. Wani lokacin kuma ya sakeshi ta gaba.
Yakan sanya farin rawani ko baqi awasu lokutan. Kuma yakan sanya tufafi wadanda aka ci bakinsu da dibaji ko sauran kayan ado (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam).
Annabi (saww) yana da tufafin da yakan sanya a muhimman lokuta Musamman lokacin da Qabilun larabawa daban daban suke zuwa. Kuma shi ba ya sanya tufafi masu jan Qasa.
Anan zamu tsaya sai a karatu na gaba zamu yi bayani akan Takalman Ma'aiki (saww) da fatan Allah shi Qara mana sonshi da Qaunarsho da biyayya da girmamawa agareshi. Ameen.
An gabatar da karatun ne a Zauren Fiqhu Whatsapp 1,2,3, da 4 ranar 14-08-2017 22-11-1438.
0 comments:
Post a Comment