```Assalamu alaikum warahmatullhi wa barakatuhu
Malam ya ake warware sihiri abisa sunnah Annabi (sallallahu alaihi Wa sallam)? Allah yasaka da alkhairi```
_*AMSA:*_
*******
وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،
*1. Hanya ta daya:* Idan za'a iya binciko abinda matsafin (mai sihirin) yayi amfani dashi wajen yin sihirin to sai a nemo shi a qone shi ko lalata shi. Misali idan yayi amfani da gashin kan mutum ko wani abu na jikin mutum ko kayansa ya saka su cikin wani kogo ko wani rami sai a tone abun a qone, shikenan da yardar Allah wannan sihirin zai karye.
*2. Hanya ta biyu:* Idan ansan mai sihirin to za'a iya tilasta shi cewa ya warware sihirin da yayi ko a kashe shi, a tsoratar da shi sosai. To idan ya warware qullin da yayi to in shaa Allah za'a ga sihirin ya warware. Kuma idan ma ya warware hukuma zata iya hukunta shi kamar yadda hadisi ya tabbata cewa Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yace: Hukuncin dan sihiri shine a soke da mashi. Kamar yanda Uwar Muminai Hafsat ta hukunta wata baiwarta 'yar sihiri ta hanyar kisa.
*3. Hanya ta uku:* Karatun Qur'ani (Ruqyah): Ana karantawa wanda aka yiwa sihirin ayoyi na 117 zuwa na 122 na suratul A'araf, ayoyi na 79 zuwa na 81 na suratul Yunus, ayoyi na 65 zuwa ta 70 na suratul Ta-Ha, Ayatul Kursiyyu, Suratul Kafirun, [sai kuma suratul Ikhlas, suratul Falaq, suratul Nas kafa uku uku (3x) ]. Sai kuma a hada da addu'o'in neman waraka da neman sauqi daga wajen Allah madaukakin Sarki kamar yadda sunnah ta tsara.
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺭﺏ ﺍﻟﻨﺎﺱ ، ﺃﺫﻫﺐ ﺍﻟﺒﺄﺱ ﺍﺷﻒ ﺃﻧﺖ ﺍﻟﺸﺎﻓﻲ ، ﻻ ﺷﻔﺎﺀ ﺇﻻ ﺷﻔﺎﺅﻙ ، ﺷﻔﺎﺀ ﻻ ﻳﻐﺎﺩﺭ ﺳﻘﻤﺎ
Da kuma addu'ar da mala'ika Jibril ya karantawa Annabi Sallallahu alaihi wasallam yayinda yayi masa ruqyah.
ﺑﺎﺳﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﺭﻗﻴﻚ ﻣﻦ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻳﺆﺫﻳﻚ ، ﻭﻣﻦ ﺷﺮ ﻛﻞ ﻧﻔﺲ ﺃﻭ ﻋﻴﻦ ﺣﺎﺳﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﺸﻔﻴﻚ ، ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﺭﻗﻴﻚ
Suma wadannan addu'o'in ana karanta su ne kafa uku-uku (3x).
Ko kuma a rinka karanta wadannan surorin, ayoyi da kuma addu'o'in a cikin ruwa masu tsarki a rinka ba wanda aka yiwa sihirin yana sha, yana kuma wanke jikinsa dasu.
*4. Hanya ta hudu:*
Asamu ganyen magarya guda bakwai (7) a daddaqe su a zuba cikin ruwa sai a karanta irin wancan bayanin dake a sama:
Ayoyi na 117 zuwa na 122 na suratul A'araf, ayoyi na 79 zuwa na 81 na suratul Yunus, ayoyi na 65 zuwa ta 70 na suratul Ta-Ha, Ayatul Kursiyyu, Suratul Kafirun, [sai kuma suratul Ikhlas, suratul Falaq, suratul Nas kafa uku uku (3x) ]. Za'a hada da suratul Fatiha. Sai kuma a hada da addu'o'in neman waraka da neman sauqi daga wajen Allah madaukakin Sarki kamar yadda sunnah ta tsara.

Za'a karanta wadannan surorin, ayoyin da kuma addu'o'in a cikin ruwan garin magaryar guda bakwai da aka niqe. Sai a rinka ba wanda aka yiwa sihirin yana sha kuma yana wanke jikinsa dashi.
To in shaa Allah wadannan sune hanyoyin warware sihiri ingangantattu kuma ana samun dacewa da yardar Allah idan anyi amfani dasu.
Shawara:
Yana da kyau, a yawaita karatun Qur'ani mai girma musamman suratul Bakara, saboda muhimmancinta wajan
kore shaidanu, kamar yadda ya tabbata a hadisi, kada kuma a manta da karanta addu'o'in shiga bandaki da na bacci, da azkar na safe da yamma, da kuma tuba daga laifuka.
Allah ya qara tsare mu daga sharrin duk wani shaidanin mutum da aljan.
والله أعلم،
***********************************
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
_*WhatsApp*_ _**_
KARANTA WANNAN
http://www.duniyarfatawa.cf/2017/08/menene-sihiri-kuma-ya-kasu-gida-nawa.html?m=1

0 comments:
Post a Comment