*YAYA AKE RABA NAMAN LAYYAR DA ZA'ACI DA WANDA ZA'AI SADAKA DASHI?*
الحمد لله سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.
*AMSA :* An ruwaito Umarni da Sadaka da naman layya acikin hadisai ingantattu, kamar yanda aka ruwaito izinin ci da kuma adanawa,
Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daka Aisha Allah ya qara mata yarda tace: Wasu Mutanen Qauye sunzo madina, lokacin layya azamani Annabi sallallahu Alaihi wasallam, Sai Yace: Ku ajiye naman layya kwana uku, sai kuyi sadaka da Sauran, bayan wata shekarar sai yace: Kuci ku ajiye, na hanaku ajiyewa ya wuce kwana uku saboda baqin da sukazo madina ne.
*Muslim (3643).*
Nawawi yace: acikin Hadisin akwai Umarni da yin sadaka, Abunda yake wajibi ayi sadaka dashi shine abunda sunan sadaka zai gaskatu akansa kawai,
Amma anfiso kayi Sadaka da Mafi yawan naman layyar, mafi karanci shine ka kasa naman gida uku, kayi Sadaka da kashi daya, kayi kyauta da daya, kaci kashi daya.
Wasu sukace: Kaci rabi kai sadaka da rabi, wannan qasa yake wajan kamalar Abunda akeso.
Amma sadaka ta Wadatarwa kawai, abunda sunan sadaka zai gaskatu akansa ya isar.
Cin Naman Layyar Mustahabbine ba dole ba.
Malik Yace: Babu haddi na abunda zakai sadaka dashi na layya, ko wanda zakaci, zaka ciyar da talakawa da mawadata, in kaga dama ka basu danye, inka ga dama ka basu dafaffe ko soyayye.
*Al-kafi (1/424).*
Shafi'iyyah Sukace: Anfi so kayi sadaka da mafi yawan naman, sukace: Mafi qarancin kamala shine kayi sadaka da daya bisa uku, kaci daya bisa uku, kayi Kyauta da Daya bisa uku. ya halatta kaci rabinta, kyauta da wani sashinta shine dole.
*Nailul Audããr (1/145) da Sirajil Wahàaj (563).*
Ahmad yace: Mudai muna bin hadisin Abdullahi bin Abbas Allah yaqara musu yarda, (kaci daya bisa uku, kaciyar da wanda kaga dama da daya Bisa uku, kayiwa miskinai da talakawa sadaka da daya bisa uku). Abu musa Asfahani ya ruwaitoshi acikin waza'if yace: hadisine kyakkyawa, shine maganar ibnu mas'uud da Ibnu Umar ba'a samu wanda ya Saba musu ba cikin sahabbai.
Duba *Al-Mugny (8/632).*
Dalilin Sabani Akan haddin abunda za'ai sadaka dashi shine sassabawar ruwayoyi,
An samu ruwayar da tazo batare data ayyana abunda za'ai sadakar dashi ba kamar hadisin *Buraida* Allah yaqara yarda dashi, Wanda turmuzi ya ruwaito (1430). yace: Hadisine kyakkyawa Ingantacce.
Wasu sunyi aiki dashi cikin sahabbai da wasunsu Allah yaqara yarda dasu.
Wallahu A'alamu.
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.
*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*

0 comments:
Post a Comment