Duniyarfatawa.com™: Tambaya da amsa

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Showing posts with label Tambaya da amsa. Show all posts
Showing posts with label Tambaya da amsa. Show all posts

Tuesday, 7 November 2017

Menene Hukuncin lika Ayatul Kursiyyu Abango da Nufin neman kariya?

*Tambaya ta (219)*

*Menene Hukuncin lika Ayatul Kursiyyu Abango da Nufin neman kariya?*

الحمد لله واحد القهار.

*AMSA:*Lika Ayatul kursiyyu ko qananun alluna ajikin gida ko mota ko shago, ko makaranta ko wajan kasuwa, akwai barna mai yawa acikin hakan, bisa Abunda shari'a ta hana.

@ - Mafi Rinjaye Ana likawa ne dan Ado da gayu, wanda bango ana sanya masa launuka na fenti hakan saiya zama sababi na wulaqanta Alqur'ani.
Wannan yana daka cikin juyar da Alqur'ani daka manufar saukar dashi, daka shiriya da wa'azi kyakkyawa dakuma Ibada da tilawarsa dasauransu..

Alqur'ani Ba'a Saukar dashi danyiwa bango Ado dashi ba, an Saukar dashi dan shiriya ga Mutane, dakuma Bayani.

2- Wasu Suna likawa ne dan Neman tabarruki, Wannan Bidi'ane Tabarruki Mai kyau shine bauta da karanta Alqur'anin, Bawai likashi ajikin bango ko juyashi zuwa jikin Alluna masu Ado ba.

Sannan Yin hakan yasabawa Abunda Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yake akai, da khalifofinsa shiryayyu Allah yakara yarda dasu, dukkan Alkhairi yana cikin binsu, bawai wajan Saba musu ba,

Tarihi yanuna wannan dabi'a taliqa karamin Allo mai dauke da ayatul kursiyyu ko wani Bangare na Alqur'ani ajikin gida ko mota ko kasuwa, ba'a fara yinsa ba sai bayan shudewar  Nagartattun Musulmi sai lokacinda Musulmai suka zama masu rauni a'aqida da ilmi dariko da Addininsu.

Haka nan Lika irin wannan alluna dauke da Alqur'ani hanyace dazatakai Mutum ga shirka, domin Wasu suna qudurta cewa wadannan kananun Alluna da'ake likawa akasuwa ko mota ko gida kariyane ga gidan ko motar daka Wani Sharri, qudurce wannan kuma Shirkane.

Mai bada kariya na Hakika shine Allah, daka cikin dalilan da zaisa kuma yabawa Mutum kariya shine tilawar Alqur'ani ka yin zikirori wadanda Sukazo acikin hadisai Ingantattu, bawai likashi abangon gida ko mota ba.

Adunqule dai bai halatta rubuta ayar Alqur'ani abangon gida ko sanya karamin Allo ajikin mota ko shago ba, koda abangon masallacine bai halatta ba, bidi'ane.

Sanyawa kuma tareda qudurce bayar da wata kariya ga Mutum wannan kam Shirkane.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك نشهد أن لا إله إلا أنت نستغفرك ونتوب إليك.

🖊 *Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai*
*+2347033406106.*
*+2348140925493.*
Share:

Saturday, 14 October 2017

Cikakken bayani akan sallar qasaru, Wasu sunce kwana 3 ce??

*TAMBAYATA (36)*

*INASAN CIKAKKEN BAYANI ASALLAR QASARU WASU SUNCE KWANA UKU NE?*

الحمد لله.

AMSA: ldan Mutum yaqudurci zama agarinda zashi sama da kwana hudu, hukuncinsa shine hukuncin mazaunin gida daka lokacinda yashiga garin dazashi, amma ahanya zaidunga kasaru kafin ya isa zuwa garin, dazarar yashiga garin zaidunga cika sallah bai halatta yai kasaru ba.

Yazo afatawa lajnatul da'imah ( 8/99)

Sukace:Tafiyar daza'ai mata kasaru itace, tafiyar da a'al'ada za'ace kayi tafiya, bacewa za'ai kaje unguwaba wannan tafiyar zakai mata kasaru, gwar-gwadon yanda za'ace tafiya kayi ba inguwa kaje ba, abisa kaddarawa shine sukace kilo mita saba'in, Amma wannan ra'ayin wasu malaman fiqhu ne, indai a yanda aka sani agarinku cewa inakaje gari kaza kayi tafiya, inkaje gari kaza baza'ace tafiya kaiba saidai ace kaje unguwa to bazakaiwa wannan tafiyar kasaru ba, bawai da kilo mita ake tan-tance tafiyar daza'aiwa qasaru da wacce baza'ai mata ba.

Wannan tafiyar duk wani sauki da'akaiwa matafiyi zaka sameshi, kamar shafa akan kuffi wuni da dare na kwana uku, da rage raka'o'in salloli, da hade salloli dashan azumi aramazhaan,

Wannan gawanda bai niyyaci zama agarinda zashiba sama da kwana hudu, amma idan yaniyyaci zama agarin dazashi sama da kwana hudu daka lokacin dayashiga garin garabasar matafiyi tasauka daka kansa, Idan kuma kwana hudun zaiyi cif-cif zaiyi kasaru dasauran rangwamen dake kan matafiyi.

*Matafiyinda yai tafiya amma bai san adadin kwanakin dazaiyiba kuma bai iyakance wani lokaci qayyadadde ba nazamansa agarin dazaije, to zaitayin kasaru koda lokaci maitsawo yazauna agarinda yaje, Babu ban-banci tsakanin tafiya akan jrigi ko kan ruwa ko  akafa*

Sannan yahalatta matafiyi yahada salloli biyu, jam'u taqdem hada azahar da la'asar yayishu farkon lokacin la'asar, ko jam'i taqseer, yahada azahar da la'asar aqarshen lokacin la'asar, haka magariba da isha'i.

Amma abunda yafi shine kada matafiyi yahada sallah sai idan yin kowacce alokacinta zai masa wahala kuma zaisha wuya.

Mu Sani sallar jam'i wajibice akan matafiyi kamar mazaunin gida.

Saboda haka idan mutum yaniyyaci zama agarinda zashi sama da kwana hudu, rangwamen mayafiyi baya kansa dazarar yashiga garin.

Idan kuma bai kulla niyyar zama acanba kobaisan yaushe zai dawo ba, kawai daya gama uzurinsa zai dawo gida, tozaita kasarune koda zaiyi wata agarinda yaje.

Dalili Shine Annabi Sallallahu Alaihi Yai kasaru tsawon kwanaki goma sha uku, sannan kuma malamai sukace: Allah bai iyakance adadi ayyananne ba.
Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.

*📝Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai.*
*Watsapp Group.*
*+2348123432272.*
*+2348140925493.*
Share:

Friday, 13 October 2017

Hukumce Hukumcen – Sallar Matafiyi Wato Salar “Kasaru Ke Nan”

Hukumce Hukumcen – Sallar Matafiyi
Wato Salar “Kasaru Ke Nan”
T618: Shin wajibcin kasaru a kan matafiyi ya shafi dukkan sallolin farilla ne ko kuma ya shafi wasu daga cikinsu ne kawai…?
A: Wajibcin yin kasaru ya shafi sallolin farilla na ranaku masu raka’oi hudu ne kawai, wadanda su ne sallolin azahar da la’asar da lisha. Ba a yin kasaru wa sallolin magariba da asubahi.
T619: Mene ne sharuddan wajibcin yin kasaru ga matafiyi a salloli masu raka’oi hudu
A: Sharudda guda takwas ne:
(1). Dole ne tafiyar ta zamanto ta kai “farsaki” takwas (kimanin kilomita 45 ko mil 24) tafiya, ko kuma dawowa, ko kuma tafiya da dawowa da sharaɗin kada tafiyan ta gaza farsaki hudu.
(2) Ya zamanto yana da niyyar isa ga wannan haddi na farsaki takwas yayin fita zuwa tafiyar. A saboda haka idan mutum bai yi wannan niyya ba yayin fitar nasa, ko kuma ya yi niyyar kasa da haka to amma bayan isarsa inda ya yi niyya, sai ya sake yin niyyar tafiya wani guri na daban ta yadda daga wajen da yaken zuwa inda zai je na biyu din bai kai gwargwadon da shari’a ta yarda da shi ba wajen kasaru, amma idan da zai hada dukkan tafiyar guda biyu (wato daga gidansa zuwa waje na biyu) za su kai hakan, to a wannan hali ba zai yi kasaru ba saboda rashin niyyar isa haddin kasaru tun daga farko, don haka zai cika sallarsa ne.
(3) Dawwamar wannan niyya (ta cika farsaki takwas) har ya kai wannan haddin. A saboda haka idan da zai sake niyya a tsakiyar tafiyar kafin ya isa ga haddin farsakhi hudu, ko kuma ya fara kokwanto, to daga nan hukuncin kasaru ya fadi a kansa ko da yake sallar kasarun da ya yi kafin nan ta inganta.
(4) Kada ya yi niyyar yanke wannan tafiya tasa ta hanyar wucewa ta garinsu ko kuma niyyar zama a wani guri na tsawon kwanaki goma, ko kuma fiye da haka.
(5) Tafiyar ta kasance ta halas ce a mahangar shari’a. A saboda haka idan tafiyar ta kasance don sabon Allah ce ko kuma ta haram ce, shin ita tafiyar ce ta haramun kamar gudu daga filin yaki, ko kuma manufar tafiyar ce ta haramun kamar yin tafiya don yin sata (fashi), to a irin wannan hali mutum ba zai yi kasaru ba, zai cika sallarsa ne.
(6) Kada matafiyin ya kasance daga cikin irin mutanen da suke tafiya tare da gidajensu ne kamar fulanin da ba su da takamammen muhalli, suna yawo ne duk inda suka sami ruwa da ciyawa sai su zauna a gurin.
(7) Kada tafiya ta kasance aikin mutum kamar direbobi da matuka jirgin ruwa da dai sauransu, haka kuma ya hada har da wanda aikinsa ya ta’allaka ne da yin tafiya wato aikinsa tattare take cikin tafiye-tafiye.
(8) Isa ga “haddin tarakkhus”, abin da ake nufi da ‘haddin tarakkhus’ shi ne wurin da ba zai ji kiran sallar garinsu ba ko kuma ba zai ga ganuwar garinsu ba.
Share:

Thursday, 12 October 2017

Wanda ya wanke gawa mai zaiyi shin dolene shima sai yayi wanka??

*WANDA YA WANKE GAWA MAI ZAIYI SHIN DOLENE SHIMA SAI YAYI WANKA?*

الحمد لله.

AMSA: Abunda yake ingnatacce daka cikin magan-ganun malamai shine wanda yaiwa gawa wanka, wanka ba wajibine akansaba mustahabbine sunnah ne anso yayi in baiyi ba bashida laifi, ba dole bane.

Shine maganar *Abdullahi dan Abbas da Abdullahi dan Umar, da Aisha, da Hasanul Basari da Ibrahimun-naka'iy, da Shafi'i da Ahmad, da Ishaq, da Abussauri, da Ibnu munzir damasu ra'ayi irinnasu, ibnu qudama yarinjaar da hakan*.

Duba *Sunanu Turmizi ( 3/18) da Al-mugni ( 1/134)*

Shaik Albani Allah yajikansa yace: Mustahabbine gawanda yawanke gawa shima yayi wanka saboda fadin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam, ( Wanda yawanke mamaci yai wanka, wanda yadauki mamaci yayi alwala) Abu dauda yafitar dashi *( 2/62-63) da turmuzi ( 2/132 )* kuma wasu hanyoyi na hadisin kyawawane wasu kuma ingantattune abisa sharadin da imamu muslim yake ruwaito hadisi, ibnul qayyem ya koro hanyoyin hadisin acikin *Tahzeebul Sunan* guda goma shadaya sannan yace: wadannan hanyoyin suna nuna lallai hadisin kiyayyene an haddaceshi.

 Albani yace:
Ibnu qaddan ya ingatashi hakama ibnu hazam acikin *Al-muhallah ( 1/250- (2/23-25,) da Alhafiz ibnu hajar acikin Attalkees ( 2/134) yace: Mafi saukin halin hadisin ace kyakkyawane*

zahirin Umarnin yana nuna wajabci, bazamuce wajibi bane saboda hadisai guda biyu wanda sukeda hukuncin hadisi marfu'i.

Nafarko: Shine fadin Abdullahi dan Abbas Allah yakara yarda dasu yace: ( Babu wanka akanku idan kun wanke mamaci, domin matacce acikinku ba najasa bane, yawadatar inkun wanke mamacinku kuwanke hannayenku)

*Hakim yaruwaitoshi ( 1/386) da Baihaqy ( 3/389)*

Sannan daka baya dalilai suka bayyana agareni hadisin mauqufine, bayan natabbar darauninsa abaya acikin sil-sila za'ifah ( 6304).

Nabiyu: fadin Abdullahi Dan Umar Allah yakara musu yarda yace: ( Munkasance muna wanke mamatanmu daka cikinmu akwai wanda yake alwala akwai wanda yake wanka)

Dabarani ya ruwaitoshi *(191) da khadibul bag-dadi acikin tarihinsa ( 5/424) da isnadi ingantacce kamar yanda hafiz yace: imamu Ahmad yai ishara akan hakan, Hakika khadeeb yaruwaito cewa yakebance dansa da rubuta wannan hadisinne, duba Ahkamul jana'iz ( 71-72).*

shine Abunda majalisar malamai dafatawa nakasar saudiyya suka rinjyar *( 1/318) da shaik Usaimeen Allah yajikansa, acikin sharhin mumti'i ( 1/295)*

Dan haka wanda ya wanke gawa  alwala ko wanka zaiyi, suma sunnah ne badole bane inya wanke hannunsama kawai babu komai akansa.

Amma wanke kaya ko riga bashida asali acikin shari'ar musulunci bidi'ane, Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك نشهد أن لا إله إلا أنت نستغفرك ونتوب إليك.

🖊 *Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai*
*WhatsApp Group*
*+2348123432272.*
*+2348140925493.*


Share:

Idan mace tanada janaba sai haila tazo mata, toya zatayi wanka biyu zatayi ko daya???

*TAMBAYA TA (24)*

*IDAN MACE TANADA JANABA SAI HAILA TAZO MATA, TOYA ZATAYI WANKA BIYU ZATAYI KO DAYA?*

الحمد لله.

AMSA: Idan janaba da haila suka hadu akan mace anshar'anta mata tana cikin hailar tai wankan janabar,

Idan hailar ta dauke mata saitai wankan daukewar hailarta.

Wanka daya ya wadatar ga wacce janaba da haila suka hadu akanta, tayi niyyar wankan hailar dajanabar ko wanka daya ta niyyata,

Ibnu qudama rahimahullahu yace: idan abu biyu suka hadu akan mutum wanda suke wajabta wanka, kamar haila da janaba, ko haduwar farji da azzakari dayin inzali, zai niyyar dayane wajan wankansu, Malamai dayawa sun fadi hakan daka cikinsu akwai

*Ada'u da Abu zinad, da rabi'ah da malik, da shafi'i da ishaq,*

Yazo acikin *Al'iqtina'i fi halli Alfazi Abiy shaja'a (1/68)*

Idan wankan janaba da haila suka hadu akan mace niyyar dayansu yawadatar mata kai tsaye,.

Haka idan mutum yafitar damaniyyi samada sau daya, alokuta maban-banta wanka daya yawadatar masa,

Hakika Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yana zagaya dakunan matansa sannan yayi wanka daya Kamar yanda * *Muslim yaruwaito (309)* daka Anas bin Malik Allah yakara masa yarda,

Imamun Nawawi rahimahullahu yace; Idan mutum yai hadasi iri daya ko maban-banta alwala daya tawadatar masa da ijma'in malamai, haka idan mutum yasamu janaba tahanyar jima'i dayawa da mace, koda mata dayawa, ko mafarki ko chakudewa da mata ko maza, wanka daya ya isar masa, daka cikin wadanda  suka ciro ijma'in akwai Abu muhammad bin hazama

*Almaj-Mu'u fatawa ( 1/487)*

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك نشهد أن لا إله إلا أنت نستغفرك ونتوب إليك.

🖊 *Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai*
*WhatsApp Group*
*+2348123432272.*
*+2348140925493.*


Share:

Tuesday, 12 September 2017

AKWAI MASU CEWA ALLAH YANA KO INA, SUNA HUJJA DA FADINSA ( WA HUWA MA'AKUM AINAMA KUNTUM) DA DAI WASU AYOYIN, YAYA ABUN YAKE?

*AKWAI MASU CEWA ALLAH YANA KO INA, SUNA HUJJA DA FADINSA ( WA HUWA MA'AKUM AINAMA KUNTUM) DA DAI WASU AYOYIN, YAYA ABUN YAKE?*

الحمد لله.

*AMSA:* Allah madaukakin Sarki yana Saman Al'arshi, saman Dukkan halittu, a wajan Ahlussunnah Wal-jama'a, Haka dukkan manzanni sukazo da Wannan aqidar, Allah yana Saman Al'arshi.

Kamar Yanda ya fada a cikin Ayoyi maban-banta Masu yawa acikin Alqur'ani mai girma.

Allah ya bayyana Qarara ya dai-daita a saman Al'arshinsa, dai-daituwar da ta dace da girmansa da Daukakarsa, Ba Wani Abun Halitta da yai Kama dashi wajan yanda ya dai-daita.

Babu Wanda yai kama da Allah, ko yake kama dashi,,

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya Tambayi Wata baiwa a ina Allah yake? Tace yana Sama, Yace Ni Wanene tace: Manzan Allah, sai ya cewa: Uban gidanta ka 'yantata tabbas Ita Muminace. Muslim ya ruwaito.

Wannan ya Nuna Allah yana Sama can Saman Bakwai Saman Al'arshi sama madaukakiya.

ISahabbai sun hadu kamar yanda Manzanni Suka hadu, akan Allah yana Sama, Saman Al'arshi.

Duk Wanda yace Allah yana Kowanne waje, ko baya Sama, shi kafirine, Mai Qaryata Allah da Manzansa, da qaryata Ijma'in Ahlussunnah Wal-jama'a, Kamar dariqun bidi'a irinsu *Jahamiyyah da Mu'utazilawa,* da Makamantansu, Wadannan suna cikin Wadanda sukafi kowa kafirci cikin Mutane, saboda Inkarin sunayen Allah da Siffofinsa.

Fadin Allah madaukakin Sarki acikin Suratul Mujadala aya ta (7).

ألم ترى أن الله يعلم مافي السماوات وما في الأرض ما يكون من نجوى ثلاثة إلا هو رابعهم ولا خمسة إلا هو سادسهم، ولا أدنى من ذلك ولا أكثر إلا هو معهم أين ما كانوا، ثم ينبئهم بما عملوا يوم القيامة، إن الله بكل شي ء عليم.

Bata Nufin Irin yanda batattu da 'yan bidi'a suke fassara ta, da yanda suke jefa shubuha da rudu a zuqatan Masu qaramin Sani.

Abunda Ake nufi acikin Ayar shine, Babu wasu mutum uku da zasu zauna suyi zance ko tattaunawa aboye asirri face sai Allah ya zama Na hudunsu, idan Su biyarne ko Qasa da Haka ko sama da haka face Sai Allah ya Zama yana tare dasu, da Ilminsa da Buwayarsa, a duk inda Suka kasance, Babu Abunda zai boyu agareshi na Al'amarinsu, Sannan ranar Alqiyama Ya basu labari akan Abunda Suka aikata, na Alkhairi ko sharri, Sannan yai Musu sakayya dashi, Tabbas Allah Masanine Akan Komai.

Wannan shine Abunda ayar da Ire irenta suke nufi, Bata cin karo da Ayoyi da Ingantattun Hadisan da suka nunar da Allah yana Sama a saman Al'arshi, babu Abunda yake buya agareshi Na ayyukan bayi aduk inda suka aikata Wani abu, yana tare dasu da Ilminsa da Buwayarsa.

Duk Wanda kaji yana jidali da hayaniya akan Abunda ayoyi da Hadisan dai-duwar Allah a saman Al'arshi suka tabbatar, inma tantirin jahile wanda ya gaji bidi'a a nonon uwarsa, ko kuma zindiqine Batacce wanda Allah ya Wulaqantar dashi ta hanyar aukawa wannan bata.

Mai Son Qarin bayani saiya duba Litattafan tafsiri musamman Tafsirin ibnu kaseer qar-qashin wannan aya da Makamantanta, da Kuma litattafan Aqida da Tauhidi.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*
Share:

Wednesday, 30 August 2017

SHIN DA YIN LAYYA DA BIYAN BASHI WANNE YAFI?

*SHIN DA YIN LAYYA DA BIYAN BASHI WANNE YAFI?*

الحمد لله.

*AMSA;* Biyan Bashi shine yafi, kuma shine yake dole sama da yin layya, saboda dalilai Masu Yawa.

1- Biyan Bashi dolene, Layya kuma Sunnah ce Mai qarfi, ba'a gabatar da Sunnah akan wajibi, har a wajan wadanda suke ganin layya wajibice, sunce biyan bashi shine abun gabatarwa akan layya, domin layya a wajan wadanda Sukace dolece, tana Zama tilas ne akan mai iko, Mai bashi kuma ba Mai iko bane.

2- A cikin biyan bashi akwai kubuta daka nauyin dake kan mutum, wajan ayyana layya kuma shagalane da nauyin, babu shakka Sauke nauyi shine yafi sama da shagala dashi.

3- Bashi Haqqin bayine, Layyah haqqice ga Allah da Mawadaci, A wannan hali za'a gabatar da hakkin bayine

4- Ci gaba da Zaman bashi akan mutum akwai hadari babba, saboda tsoran kada sai ranar alqiyama za'a biya da kyawawan ayyukan mutum.

Acikin haka akwai hadari domin a wannan halin mutum yana cikin tsananin buqatar kyakkyawan aiki koda dayane.

Da Wannan zai bayyana gareka cewa biyan bashi yafi sama da yin layya, saidai idan bashi yana da lokaci maitsawo, ta yanda wanda ake bin bashi yana da mafi rinjayen zaton zai iya biyan bashin alokacin da aka deba masa, idan yayi layya, ko ya ranci abunda zai iya biya koda alokacin bai biyaba, Babu laifi akansa ya yanka layya gwar-gwadon Abunda Allah ya buda masa, zai samu lada da Sakamako Awajan Allah.

Kamar yanda bayani yazo acikin littafin Sharhin Mumti'i (8/455).

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*


Share:

WACCE DABBA CE TAFI FALALA WAJAN YIN LAYYA DA ITA?

*WACCE DABBA CE TAFI FALALA WAJAN YIN LAYYA DA ITA?*

الحمد لله سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA :* Dabbar datafi falala wajan layya Itace (Raqumi) Sannan (Saniya) Sannan (Tunkiya) Sannan Tarayyah wajan yanka (Saniya) haka Abu Hanifa da Shafi'i sukace.

Saboda fadin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ( Wanda yaje masallacin juma'a da Wuri asa'ar farko, Kamar ya gabatar da Sadakar ( Raqumi ne) Wanda yaje asa'a ta biyu kamar ya gabatar da ( Saniya) ne, Wanda yaje a sa'a ta uku kamar ya gabatar da (da rago mai qaho ) ne, Wanda yaje a sa'a tahudu kamar ya gabatar da ( Kaza)ne, Wanda yaje Asa'a ta biyar kamar ya gabatar da ( Kwai) ne,

*Bukhari (881) da Muslim (850).*

Domin yankane da'ake neman kusancin Allah dashi, sai raquma tafi falala kamar hadaya, yi da Rago yafi falala akan mutane su hadu suyi da (Raqumi) domin Zubar jini shine manufa a layya, Wanda yake shi kadai zai samu kusancin Allah da zubar dashi baki daya, A cikin tumaki da awaki rago shine yafi falala, domin dashi Annabi Sallallahu Alaihu wasallam yayi layya, saboda yafi kyawun nama.

*Duba Al-Mugni (13/366).*

Kamar Yanda yazo a *fatawa Lajnah (11/398).*

Abunda ake hujja dashi cikin hadisin shine yanda aka samu fifikon kusantar Allah tsakanin (Raqumi da Saniya) da (Tumaki da Awaki) Saboda raqumi yafi kudi da yawa da nama da amfani, Haka Malaman mazhabobi ukun nan sukace: *Abu hanifa, da Shafi'i, da Ahmad*.

Imamu Malki yace: Abunda yafi falala wajan layya shine ragon daya shekara daya, sanann Saniya, sannan Raqumi.

Domin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yayi layya da raguna guda biyu, shi kuwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam baya aikata abu sai wanda yake yafi falala.

Amsa akan wannan sai ace: Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya zabi ragone don sauqaqawa Al'ummarsa, domin suna koyi dashi, Bayaso ya taqurawa Al'ummarsa, haqiqa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya bayyana falalar raqumi akan Saniya.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*



Share:

MENENE HUKUNCIN YANKAN LAYYA DA HANNUN HAGU?

*MENENE HUKUNCIN YANKA LAYYA DA HANNUN HAGU?*

الحمد لله سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA :* Mustahabbine Mutum ya yanka dabba da hannun dama, domin yafi hutar da dabba, Yanda mafi yawan Mutane suna Amfani da hannun dama ne.

Yanka da Hannun hagu Sabanine na Wanne yafi falala, wanne yafi hutar da dabba, Saidai idan da hannun Hagune mutum zai iya yanka hakan shine yafi falala Agareshi, sama da ya yanka da dama.

Ba Sharadi bane wajan yanka ya Zama da hannun dama, ya Halatta yankawa da Hannun dama Dana hagu.

Domin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yace: ( Wanda ya zubar da jini ya Ambaci sunan Allah kuci).

Bai iyakance da Hannun hagu ko dama ba, saidai babu kokwanto da Hannun dama yafi falala, domin Hannun dama yafi qarfi, idan ko yafi Qarfi da shine Abun yankawar zaifi jin Sauqi.

Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yayi Umarni da Sauqaqawa Abun yanka inda yace: ( Allah ya Wajabta Kyautatawa Akan kowane Abu, idan zakuyi kisa ku kyautata kisan, idan zakuyi yanka ku kyautata yanka, Dayanku ya Wasa Wuqarsa, ya hutar da Abun yankansa.)

Idan Mutum bahagone yankawa da hagu shine yafi falala awajansa, .

Babu Laifi dan Mutum ya yankan layyarsa da hannun hagu.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*


Share:

MENENE HUKUNCIN WANDA BAYA IYA HALATAR YANKA LAYYARSA,?

*MENENE HUKUNCIN WANDA BAYA IYA HALATAR YANKA LAYYARSA,?*

الحمد لله سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA :* Abunda yafi shine mutum ya halarci yanka layyarsa da kansa, idan bazai iyaba, babu laifi wani yaje ya shaida masa yankan layyar tasa.

Domin Wakilci wajan halattar yanka layya ya halatta babu Sabani tsakanin Malamai,

Halartar yanka layya mustahabbine ba dole ba.

Ibnu Qudama yace: Idan ya yanka layyar da hannunsa haka shine yafi, domin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya yanka layyarsa da hannunsa.

Idan Kuma ya wakilta wani ya halatta, saboda Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya Wakilta Aliyu ya qarasa yanka Masa hadayarsa, wannan Babu Sabani akansa, An so ya halarci yanka layyar sa.

*Al-Mugny (13/389-390)*

Ladan layya idan bayarwa kayi ayi maka, dukkan wanda ka Niyyata acikinta zai samu ladan, koda baka halarci yanka taba, saboda fadin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ( Dukkan Ayyuka Saida Niyyah, kowanne mutum akwai Abunda ya niyyata.

Wallahu A'alamu

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*


Share:

SHIN DALILAN YIN LAYYA DALILAINE NA WAJABCI KO MUSTAHABBANCI?

*SHIN DALILAN LAYYA DALILAINE NA WAJABCI KO MUSTAHABBANCI?*

الحمد لله سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA :* A wannan mas'alar akwai Sabani Shahararre tsakanin Malamai, Mafi yawan Malamai suna ganin Sunnatuwar layya ne ba wajabcin taba.

Hanafiyyah da Imamu Ahmad a wata ruwaya da Shaikul
Ibnu taimiyyah ya zaba sun tafi akan wajabcin layya akan mawadaci.

Ibnu qudama yace: mafi yawan malamai suna ganin layya sunnah ce mai qarfi ba dole bace, .

An ruwaito haka daka *Abubakar da Umar da Bilal, da Abi mas'uud Al-badary* Allah yaqara yarda dasu.

Haka *Suwaid bin gafala da sa,'eed bin Musayyeeb da Al-qama da Aswad, da Ada'u da Shafi'i, da Ishaq, da Abu Saur, da Ibnu Munzir* sukace.

Rabi'ah da Malik da Saury da Auza'iy da Lais, da Abu hanifa, sukace: Dolece .

Saboda hadisin da Abu huraira Allah yaqara yarda dashi yace: Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Wanda yake da Wadata baiyi layya ba, kada ya Kusanci masallacin mu).

Daka Miknaf bin Sulaim, Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( yaku Mutane akan dukkan mutanen gida, kowacce shekara akwai layya, da yankan watan rajab na jahiliyyah.).

Darul Qudny ya ruwaito hadisi da isnadi daka ibnu Abbas daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: abubuwa uku wajibine akaina, akan ku kuma nafila ne, wutiri, da Yankan layya, da raka'atanul fajri.

Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Wanda yai nufin zaiyi layya, kada ya aske gashinsa ko farcensa,) Ya Alaqanta ta da Iko  wajibi ba'a jinginashi da iko, .

*Al-mugny (11/95).*

Dalilan dukkan Bangarori biyu na Malamai suna da yawa, saidai dukkansa basu kubuta daka matsala a isnadojinsu ba, ko daka jayayya wajan kafa hujja dasu ba, .

Wadanda Sukace dolece, suna kafa hujja da hadisin Abu huraira ( Wanda yake da wadata yaqi yin layya kada ya kusancinmu masallacinmu) ibnu Majah.

Malaman hadisi basu sallama ingacin maganar daka Annabi ba, sunyi masa hukunci da cewa maganar Abu hurairace ,bata Annabi ba, .

Baihaqi acikin Sunan dinsa (9/260) yace: Labari yazomin Abu isah Atturmuzi yace: Hadisine sahihi, yace: Ja'afar bin rabi'ah ya ruwaitoshi da waninsa daka Abdurrahaman Al-a'araj, daka Abu huraira.

Ibnu hajar yace: ibnu majah ya fitar dashi da Ahmad, mazajensa Amintattune, saidai anyi sabani wajan shin maganar Annabi ce,.

*Fatahul bary (12/98)..*

Wasu sun rinjayar da cewa hadisine mauqufi, kamar Ibnu Abdul barri da Abdul haq acikin Ahkamul wusdaah (4/127) da Munzry acikin Targeeb wattarheeb, da Ibnu Abdul hady acikin tanqeeh (2/498) duba Hashiyar Masu tahqiqin sunanu Ibnu majah (4/303).

Hadisi na Biyu, shine hadisin Abu ramlah daka miknaf bin sulaim Marfu'an, Abu dauda ya ruwaitoshi (2788) da Turmuzy (1596) da Ibnu majah (3125).

Wasu Malamai sun raunatashi saboda jahalar Abu ramlah, sunansa Ãmir, Al-kidaby yace: Hadisine mai rauni, Abu ramlah ba'a sanshi ba, *Ma'alimul Sunan (2/226).*

Zaila'iy yace: Abdul haq yace: Isnadinsa mai raunine, Ibun qaddaãn yace: illarsa shine jahalar abi ramlah, sunansa Amir ba'a sanshi ba saida wannan, ibnu Auun ya ruwaitoshi daka gareshi.Duba *Nasburrayah (4/211).*

Wadanda Sukace: Mustahabbice sun kafa hujjah da dalilai masu yawa, Mafi muhimmancin sune guda biyu.

Hadisin Ibnu Abbas Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Abubuwa uku Wajibaine akaina, akanku kuma Nafilane, *Wutiri, da Yankan layya, da Sallar walaha.)*

Ahmad ya ruwaitoshi (2050) da Baihaqy (2/467).

Hadisin Malamai na da da yanzu sun raunatashi.

Ibnu hajar yace: An ruwaitoshi daka Abiy janaba  Al-kalbi daka ikrimah, Abu janaba za'ifine, mudallasine, yana yin An-ana.

Malamai Sun raunata hadisin kamar *Ahmad da Baihaqy, da Ibnu Salah, da Ibnul jauzy, da Nawawi* da wasunsu.

*Talkeesul Habeer (2/45- 258).*

Hadisi na Biyu: Hadisin Ummu salamah Annabi Sallalahu Alaihi wasallam yace: ( Idan Goman farko na zhul-hijjah ya shiga wanda yake san yin layya, kada ya yanke farcensa ko gashinsa ko fatarsa) *Muslim (1977).*

Imamu Shafi'i yace: Wannan daliline akan layya ba dole bace, Duba *Al-majmu'u (8/386).*

Hadisan da suke nuna Wajabcin layya akwai matsala akansu, duk da wasu malamai sun kyautata wasunsu.

Haka hadisan da suka nassanta Mustahabbanci, ta bangaren isnadi sunfi tsananin rauni.

Abunda yake qar-fafa rashin Shar'antuwar layya sune Abu biyu:

@- Barranta Ta tun asali, matuqar wani dalili kubutacce daka cin karo bai zo ba, to lallai Asali shine rashin wajabci.

Kamar yanda Bin baaz ya bayyana acikin *fatawa dinsa (18/36).*

@- Zantukan sahabbai ingantattu da aka ruwaito daka Sahabbai, ya inganta daka *Abubakar da Umar* da wasunsu sun kasance basa layya, don tsoran kada Wasu mutane su dauka dole ce.

Kamar yanda Baihaqi ya ruwaito  acikin *Ma'arifatu Sunan  Wal-Ãsãar (14/16)  Ka sake duba Sunanul Kubra (9/444) .*

Nawawi acikin *Al-Maj-Mu'u (8/383)* yace: Zantukan da aka ambata daka Abubakar da Umar, Baihaqi ya ruwaitosu da Isnadi kyakyyawa.

Haitami yace: Dabarani ya ruwaitoshi acikin Kabeer mazajensa Ingantattune. Duba

*Mu'ujamul zawa'id (4/18) Albani ya Ingantashi acikin Irwa'u (4/354)..*

Mas'alar dai akwai sabani Abun lura tsakanin malamai.

Wanda sukace: Mustahabbice shine Abunda dalilinsu yafi bayyana agaremu.

Mesan Qarin bayanai saiya duba *Ahkamul Az-hiyyah Wal-zakah na Shaiek Usaimeen, Da Al-Mufassaal fy Ahkamul Azhiyyah.*

Wallau A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*


Share:

YAYA AKE RABA NAMAN LAYYAR DA ZA'ACI DA WANDA ZA'AI SADAKA DASHI?

*YAYA AKE RABA NAMAN LAYYAR DA ZA'ACI DA WANDA ZA'AI SADAKA DASHI?*

الحمد لله سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA :* An ruwaito Umarni da Sadaka da naman layya acikin hadisai ingantattu, kamar yanda aka ruwaito izinin ci da kuma adanawa,

Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daka Aisha Allah ya qara mata yarda tace: Wasu Mutanen Qauye sunzo madina, lokacin layya azamani  Annabi sallallahu Alaihi wasallam, Sai Yace: Ku ajiye naman layya kwana uku, sai kuyi sadaka da Sauran, bayan wata shekarar sai yace: Kuci ku ajiye, na hanaku ajiyewa ya wuce kwana uku saboda baqin da sukazo madina ne.

*Muslim (3643).*

Nawawi yace: acikin Hadisin akwai Umarni da yin sadaka, Abunda yake wajibi ayi sadaka dashi shine abunda sunan sadaka zai gaskatu akansa kawai,

Amma anfiso kayi Sadaka da Mafi yawan naman layyar, mafi karanci shine ka kasa naman gida uku, kayi Sadaka da kashi daya, kayi kyauta da daya, kaci kashi daya.

Wasu sukace: Kaci rabi kai sadaka da rabi, wannan qasa yake wajan kamalar Abunda akeso.

Amma sadaka ta Wadatarwa kawai, abunda sunan sadaka zai gaskatu akansa ya isar.

Cin Naman Layyar Mustahabbine ba dole ba.

Malik Yace: Babu haddi na abunda zakai sadaka dashi na layya, ko wanda zakaci, zaka ciyar da talakawa da mawadata, in kaga dama ka basu danye, inka ga dama ka basu dafaffe ko soyayye.

*Al-kafi (1/424).*

Shafi'iyyah Sukace: Anfi so kayi sadaka da mafi yawan naman, sukace: Mafi qarancin kamala shine kayi sadaka da daya bisa uku, kaci daya bisa uku, kayi Kyauta da Daya bisa uku. ya halatta kaci rabinta, kyauta da wani sashinta shine dole.

*Nailul Audããr (1/145) da Sirajil Wahàaj (563).*

Ahmad yace: Mudai muna bin hadisin Abdullahi bin Abbas Allah yaqara musu yarda, (kaci daya bisa uku, kaciyar da wanda kaga dama da daya Bisa uku, kayiwa miskinai da talakawa sadaka da daya bisa uku).  Abu musa Asfahani ya ruwaitoshi acikin waza'if yace: hadisine kyakkyawa, shine maganar ibnu mas'uud da Ibnu Umar ba'a samu wanda ya Saba musu ba cikin sahabbai.

Duba *Al-Mugny (8/632).*

Dalilin Sabani Akan haddin abunda za'ai sadaka dashi shine sassabawar ruwayoyi,

An samu ruwayar da tazo batare data ayyana abunda za'ai sadakar dashi ba kamar hadisin *Buraida* Allah yaqara yarda dashi, Wanda turmuzi ya ruwaito (1430). yace: Hadisine kyakkyawa Ingantacce.

Wasu sunyi aiki dashi cikin sahabbai da wasunsu Allah yaqara yarda dasu.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*



Share:

SHIN LAYYA WAJIBICE AKAN MAI AIKIN HAJJI?

*SHIN LAYYA WAJIBICE AKAN MAI AIKIN HAJJI?*

الحمد لله سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA :*Malamai Sunyi sabani akan hukuncin layya akan mai aikin hajji, wasu sukace mustahabbice akan mai aikin hajji, wasu sukace babu layya akan mai aikin hajji..

Wadanda sukace babu layya akan mai aikin hajji sunyi sabani akan sababin rashin shar'antuwarta akansa abisa magan-ganu guda biyu:

Nafarko: Sukace mai hajji babu Sallar idi akansa, yankansa kuma shine hadayar tamattu'i, ko Qirani.

Na Biyu : Mai hajji matafiyine, layya kuma an shar'antawa mazaunin gidane, wannan shine maganar Abu hanifa, awajansa mai aikin hajji, idan dan cikin makkah ne shi ba matafiyi bane,  layya ta wajaba akansa.

Hanafiyyah sukace: Wajibice akan matafiyi da Mazaunin gida,  kamar yanda yazo  acikin *Al-Mabsuud (6/171).*

Yazo acikin *"Jauhara (5/285-286)"* Layya ba wajibi bace akan mai hajji matafiyi, amma wanda yake mazaunin makkah wajibice akansa koda zaiyi hajji.

Malikiyyah sukace: Babu layya akan mai hajji, saboda kasancewarsa mai hajji, ba saboda kasancewar sa matafiyi ba. Kamar yanda yazo acikin *Mudawwanah ( 4/101).*

Shafi'iyyah sukace: Layya Mustahabbice akan mai hajji

Imamu Shafi'i yace: Layya Mustahabbice akan mai hajji mazaunin makkah, da wanda ke kai kawo tsakanin gari zuwa gari, da Mazaunin gida,  da wajibice akan wasu banda wasu, da akan mai hajji zatafi zama dole, domin yankane, mai hajji kuma akwai yanka akansa, saidai bai halatta a wajabtawa mutane abuba saida hujja, babu ban-banci tsakaninsu.

*Al'Ummu (2/348).*

Ibnu hazam yace: Layya ga Mai hajji mustahabbice kamar yanda take akan wanda baije hajji ba, .

Wasu sunce babu layya akan mai hajji, Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya kwadaitar akan yin layyah, bai halatta a hana mai hajji falala da samun kusanci ga Allah ba, batare da wani nassi akan hakan ba.

*Al-Muhalla ta Ibnu hazam (5/314-315).*

Hanabila sukace:Layya ta halatta gamai aikin hajji.

Kamar yanda ibnu qudama acikin *Al-mugny (7/180)* Ya fada.

Hadisi yazo daka Aisha Allah yaqara mata yarda Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya yiwa matansa layya a mina ahajjin bankwana.

*Bukhari (5239) da Muslim (1211)* suka ruqaito.

Wasu malamai sunyi raddin hujja da wannan hadisin kamar ibnul qayyeem sukace: Abunda ake nufi da layya a hadisin shine hadaya.

Duba *zhadul Ma'adi (2/262-267)..*

Shaikul Islam da ibnul qayyeem sun zabi maganar masu cewa babu layya akan mai aikin hajji,.

Duba *Al'iqna'a (1/409) da Al-Insaaf (4/110)* Shaik Usaimeen ya rinjyar da wannan zancen..

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*


Share:

MENENE HUKUNCIN YIN LAYYA DA DABBA MAI CIKI?

*MENENE HUKUNCIN LAYYA DA DABBA MAI CIKI?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Malamai Sunyi Sabani akan yin layya da dabba mai ciki, jamhur din malamai sun tafi akan halaccin yin layya da dabba mai ciki, basu Ambaci dabba mai ciki, acikin aibukan da suke hana ayi layya da dabba ba,

Shafi'iyyah sun sabawa Jamhur sukace: Bai halatta yin layya da dabba mai ciki ba,

Yazo: acikin *Mausu'ah fiqhiyyah (16/281).*

Malamai Basu Ambaci dabba mai ciki cikin aibukan da suke hana ayi layya da dabba ba, sabanin shafi'iyyah, inda suka bayyana rashin halaccin yin layya da dabba mai ciki, saboda ciki yana bata ciki, nama ya zama lababbe,.

Ingantacciyar magana shine: Ya halatta ayi layya da ita, idan babu wani abun dazai hana ayi da ita na daban,.

Jaririn da aka Samu acikin dabbar layya, idan an sameshi araye za'a wankeshi aci,

Ibnu qudama yace: idan an sameshi rayayye rayuwa tabbatacciya, daza'a iya tsaftaceshi ba'a tsaftace shi ba, harya mutu, toba tsafta tacce bane, Ahmad yace: idan ya fito araye dole, a tsaftaceshi, domin wani rai ne daban.

*Al-Mugny (9/321).*

Idan aka samu jariri acikin dabbar layya matacce, jamhur din malamai sukace: Za'aci namansa, domin ya tsarkaka da tsarka kuwar uwarsa,

*Abu dauda ya ruwaito (2828) da Turmuzi (1476) ibnu majah ya ingantashi (3199) da Ahmad (10950).*

Daka Abu sa'idin daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Tsarkakuwar jariri, tsarkakar Uwarsa ne) Albani ya ingantashi *acikin Sahihul jami'i (3431).*

Wannan kamar yanda mukace shine mazhabar jamhur din malamai. sabanin Hanafiyyah.

Shaikul Islam ibnu taimiyyah acikin *maj-mu'u fatawa (26/307)* Yace:

Layya da dabba mai ciki ya halatta, idan aka samu danta ya mutu, tsarkinsa shine tsarkin uwarsa, awajan shafi'iyyah da Ahmad, da Wasunsu, yayi gashi ko baiyi gashi ba.

Idan aka sameshi araye, za'a yankashi.

Awajan malikiyyah : idan yayi gashi, ya halatta, idan baiyi gashi ba, bai halatta aci ba.

Awajan Abu Hanifa : baya halatta aci harsai an tsarkake shi bayan fitowarsa.

Saidai Wasu malamai Sun karhanta cin naman jaririn dabba ta fuskar lafiya.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*

KARKA MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.


Share:

MENENE HUKUNCIN CINYE NAMAN LAYYA DUKA, KO SADAKA DASHI GABA DAYA?

*MENENE HUKUNCIN CINYE NAMAN LAYYA DUKA, KO SADAKA DASHI GABA DAYA?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Nassoshi Na shari'a sunyi nuni akan wajabcin yin sadaka da Wani abu na naman layyah, koda kadanne, Allah madaukakin sarki yace:

( Kuci daka naman layyarku, ku ciyar da Talakan daya kame bai roqa ba, da talakan daya roqa saboda buqata, saboda haka Allah ya Yassare muku ita danku zama masu godiya) Suraul Hajji aya ta (36).

Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Kuci naman layya, ku ajiye, kuyi sadaka) *Muslim (1971).*

Malaman da Sukace yin sadaka da Naman layya wajibine sune: *Shafi'iyyah da Hanabila,* Itace sahihiyar Magana Azahirin nassosin shari'a.

Wajibine sadaka da wani abu na naman wanda sunan sadaka zai gaskatu akansa, domin manufa shine yalwatawa miskinai,

Abisa Wannan idan mutum ya cinye naman layyar sa, duka wajibine ya siya yayi sadakar,

*Rauzatul dhalibeen da Umdatul mufteen (3/223).*

Kamar yanda Marudy ya fada acikin *"Al'insaaf (6/491)*.

Kamar yanda Buhty yafada acikin *kashshaful Qina'i (7/444).*

Kamar Yanda Shaik Usaimeen ya bayyana acikin *Maj-mu'u fatawa dinsa (25/132)*

Malamai Sunyi Sabani akan wajabcin cin wani abu daka cikin Naman layya,

Jamhur din malamai suna ganin cin wani Abu na naman layya mustahabbine, ba dole bane, wannan shine fatawar Manyan Mazhabobinnan guda hudu.

Wasu sun tafi akan wajabcin cin wani Abu daka cikin naman layya koda kadanne, saboda zahirin nassosin shari'a da sukai Umarni akai.

Nawawi yace:Cin naman layya mustahabbine ba dole bane, shine mazhabar mu da Malamai gaba daya, sai Abunda aka hakaito daka wasu magabata na wajabcin cin naman, saboda zahirin hadisin dayai Umarni aci wani abu daka layya, da fadin Allah madaukakin Sarki ( Kuci daka naman layya) Jamhur din malamai sun dora wannan umarni akan halacci da Mustahabbanci,

*Sharhin Sahihu Muslim (13/131).*

Ibnu qudama yace: da Mutum zaiyi sadaka da naman layya gaba daya, ko mafi yawan naman, ya halatta.

*Al-mugni (13/380)*.

Idan ka yanka raguna da yawa, ko wanne saika debi wani abu daka namansa kayi Sadaka dashi.

da Zaka yanka raguna goma ko akuyoyi ko tumaki, ko wanne daka cikinsu saika debi namansa kayi Sadaka dashi, mustahabbine kowacce dabba kaci wani Abu na naman dukkan dabbobin daka yanka.

Domin kowacce layya cin gashin kanta take..

Shi yasa da Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya soke abun hadayarsa saiyai umarni a debo masa wani kaso daka naman kowacce raquma.

Jabir dan Abdullahi Allah ya qara musu yarda yace: Sai muka nufi Abbatuwa Annabi ya Soke raquma talatin da Uku da hannunsa, sai ya bawa Aliyu ya yanka Abunda yai Saura.

Sannan yai Umarni akawo masa daka naman kowacce sai aka sanya atukunya aka dafa masa yaci namansu, yasha romonsu.

*Mualim (1218).*

Wannan yana nuna kowacce dabbar layya da'aka yanka tana da hukunci nata ita kadai.

saboda hakane yai Umarni akawo masa wani Abu daka kowacce taguwa.

Nawawi yace: acikin wannan akwai mustahabbancin cin hadayar nafila, da layyya.

Malamai Sukace: cin naman kowacce dabba daka yanka sunnah ne, cin yanka daya na kowacce dabba akwai wadatarwa, ka sanya atukunya don kowacce ya zama akwai romon nata naman.

*Sharhin Muslim (8/192).*

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*


Share:

ME AKE FADA YAYIN YANKA DABBAR LAYYA?

*ME AKE FADA YAYIN YANKA LAYYA?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Wanda zai yanka layya sunnah yayin yanka layyar shine yace; *Bismillahi, Wallahu Akbar, Allahumma haza minka walaka, Haza Anniy,* Idan Wani zaka yankawa layyar sai kace ( *Haza An fulan,* ka Ambaci Sunansa).

*(Allahumma Taqabbal Min Fulan, Wa Ãli fulan,)* saika Ambaci Sunansa.

Abunda yake dole, shine *Bismillah* Abunda ya qaru akai sunnah ne, ba dole bane.

*Bukhari ya ruwaito hadisi (5565) da Muslim (1966)* Daka Anas Allah ya qara masa yarda yace: Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yayi layya da raguna guda biyu kosassu, ya Ambaci Sunan Allah, yai kabbara ya yanka su).

Kamar yanda *Muslim ya ruwaito (1967)* irinsa daka Aisha Allah yaqara mata yarda.

Yasa ta kawo masa wuqar dazai yanka ragunan layyarsa sai yace: *( Allahumma Taqabbal Min muhammad Wa Ãli muhammad Wa min Ummati Muhammad)*

Turmuzi ya ruwaito hadisi (1521) daka jabir bin Abdullahi Allah yaqara yarda dashi yace: ( Na halarci layyar Annabi Sallallahu Alaihi wasallam a wajan sallar idi, lokacinda ya gama khudubarsa sai ya sauko daka minbarinsa aka kawo masa rago ya yanka shi da hannunsa, yace; *( Bismillahi, Wallahu Akbar, Haza Anniy, wa Amman lam yuzahhi min Ummaty,)*

Albani ya Inganta shi acikin Sahihu Turmuzi.

Qarin ( Allahumma haza minka walaka) Yazo awasu qarin ruwayoyi.

Duba *Irwa'ul galeel (1138) (1152).*

Allahumma Haza minka walaka, Ai wannan layyar arziqinkace ya Allah, zumuncine daka gareka izuwa gareni, walaka) dankai kadai nayita.

Duba *Sharhin Mumti'i (7/492)*

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*


Share:

SHIN DOLENE SAI MUSULMI ZAI YANKA DABBAR LAYYA?

*SHIN DOLENE SAI MUSULMI ZAI YANKA DABBAR LAYYA?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Sharadine a yanka layya da niyyar layyace za'ayi,  idan mutum ya yanka da niyyar yaci nama layyar batai ba.

Imamun Nawawi Rahimahullahu yace: Niyya sharadice ta Ingantuwar layya.

*Al-Maj-mu'u (8/380).*

Bai Halatta ka wakilta kirista kafiri wajan yanka layya ba, tare da cewa yankan kirista halal ne aci, saidai saboda yankan layya ibadace, bai halatta ka wakilta kirista ba.

Saboda kirista bashi daka cikin Masu wannan ibadar da neman kusancin Allah, domin kafirine, ba'a karbar ibadarsa, idan bata halatta akaran kansa ba, bai halatta yayiwa wani ba,

Amma Da Mutum zai wakilta kirista ya yanka masa layya dan yaci nama babu laifi.

*Sharhin Mumti'i na Shaiek Usaimeen (7/494).*

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*

Share:

Tuesday, 29 August 2017

SHIN YA HALATTA MUTUM YACI BASHI DAN YIN LAYYA?

*SHIN YA HALATTA MUTUM YACI BASHI DAN YIN LAYYA?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Layya ba Dole bace, Saboda ba'a ruwaito dalilai na Shari'a akan Wajabcinta ba, Masu cewa wajibice dalilansu raunane.

*Maj-mu'u fatawa bin baaz (18/36)*

Wadanda sukace: wajibice sun shardanta sai in kana da wadata

*Duba Hashiyatu Ibnu Abideen (9/452).*

Da Masu cewa dolece da Masu cewa sunnah ce, Ba wajibi bane karbar bashi dan siyan Abun layya, domin ba dole bace.

Anso Mutum ya nemi Bashin ya sai Abun layya idan yana da tabbas din zai iya biya, kamar Ma'aikaci sai ya karbi bashin Abun layya kafin ya karbi Albashinsa Aqarshen wata. idan yasan yanada Taurin bashi ko bashi da halin biya, Abunda yafi masa kada yaci bashin.

Domin zaka shagaltar da kanka cikin nauyin bashi akan abunda ba tilas ne ba.

Shaikul Islam Ibnu taimiyyah rahimahullahu yace: Idan kana da Halin biyan bashi saika nemi bashi dan kayi layya, Wannan Abune mai kyau, Amma ba dolene ka aikata hakan ba.

*Maj-mu'u fatawa (26/305).*

Tareda cewa yana cikin masu cewa wajibice.

Ala Ayyi halin dai idan kanada halin da zaka iya biyan bashi ya halatta ka nema dan kayi layya.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.


Share:

MENENE AKA HANA GA WANDA YAKE SON YIN LAYYA YA AIKATA?

*MENENE AKA HANA WANDA YAKE SAN YIN LAYYA YA AIKATA?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Idan Watan zul-hijjah ya kama, haramunne akan Namiji ko mace da ya kesan yin layya, ya yanke farcensa ko sumarsa.

Saboda hadisin da *Muslim ya ruwaito (1977)* daka Ummu Salama Allah yaqara mata yarda daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Idan Kuka ga Watan zul-hijja, kuma dayanku yana san Yin layya, ya kame  daka yanke farcensa ko Aske gashinsa)

Imamun Nawawi Rahimahullahu yace: Malamai Sunyi Sabani akan wanda watan zul-hijjah ya kama yana san yin layya.

*Sa'eed da Ibnu Musayyib da Rabi'ah da Ahmad da Ishaq da Dauda da Wasu MalamanvSahafi'iyyah* sukace: Haramunne mutum yacire komai na gashinsa, da farcensa, harsai yayi layya, shafi'i yace: Makaruhine karhanci na Kamala, ba Haramun bane.

Sharhin Muslim.

Mace ya Halatta ta Tsefe gashin kanta, ta Wankeshi, Saidai kada ta Tajeshi, Abunda ya zuba na gashinta yayin tsefewa da Wankewa Baya cutarwa akan layyarta.

*Fatawa bin Baaz (18/47).*

Ya Halatta Wanda yake da Niyyar layya ya gyara tufafinsa ko yasa turare ko yin jima'i.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.



Share:

SHIN YA HALATTA YIWA WANDA YA MUTU LAYYA?

*SHIN YA HALATTA YIWA WANDA YA MUTU LAYYA?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Asali layya an shar'anta ta ga wanda yake rayayye, Kamar yanda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam da Shabbansa suka kasance sunaiwa kansu da iyalansu layya, abunda wasu suke dauka na kebance layya ga wanda ya mutu bashi da Asali.

Yiwa Wadanda ya Mutu layya kashi uku ne:-

Nafarko: Yiwa mamaci layya amma yabi cikin rayayyu, mislai, Ka niyyaci layya ga kanka da iyalanka, rayayyu da Matattu.

Wannan ya halatta, asalin Wannan shine layyar Annabi Sallallahu Alaihi wasallam da iyalan gidansa daka cikinsu akwai wadanda suka mutu

Na Biyu: Yiwa mamaci Layya saboda yabar wasiyyar Ayi masa, za'ai masa don zartar da wasiyyar sa, ( Wannan dolene) saidai idan mutum yakasa, Saboda fadin Allah madaukakin Sarki ( Duk Wanda ya canja Abunda mamaci yai wasici dashi na Alkhairi, zunubin yana kan wanda ya canja wasiyyar, Lallai Allah mai jine mai ganine)

Na Uku: Yiwa mamaci layya dan kyautatawa, kamar yiwa iyaye layyah, Wannan ya halatta.

Malaman Hanabila Sukace: ladan zai isa garesu kuma zasu Amfana dashi, qiyasi akan yi musu sadaka.

Saidai Bama ganin kebance yiwa mamaci layya yana daka cikin Sunnah.

Domin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam bai yiwa kowa layya daka cikin wadanda suka mutu ba a kebance, baiyiwa Ammunsa Hamza layya ba, wanda yana cikin manyan Makusantansa.

Baiyiwa 'ya'yansa wadanda suka mutu a rayuwarsaba, baiyiwa Matarsa khadija ba, tana daka cikin matan da yafi so, kuma ba'a ruwaito daka Sahabbansa ba.

Yana daka cikin Kus-kure abunda wasu suke aikatawa, yiwa mamaci layya farkon shekarar da ya mutu, suna kiranta da layyar rami) suna qudurce babu wanda ya halatta yai tarayya dashi acikin ladanta, ko suyiwa mamatansu layya saboda wasiyyarsu, amma basa yiwa kansu da iyalansu layya,

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.


Share:

Archive

Unordered List

Support