Sayyidul istigfar ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday, 3 January 2017

Sayyidul istigfar

*بسم الله الر حمن الر حيم*

*SAYYIDIL ISTIGFARIN*
 (shugan Istigfari)
.
.
.DAGA ZAUREN
*Khulafaur-rashiidun.*
.
Lucture (13)
                          Assalamu alaikum    warahamatullah    innal hamdulillah nahamaduhu wanasta inuhu Wana uzubillahi minash shaidanur rajim.
.
*wassalatu wassalamu ala nabiyyina muhammad (ﷺ) wa'alihi wa sahabihi waman tabi ihsani ila yaumin din,*  godia ya tabbata ga ALLAH ubanigiji ma madukakin sarki daya azurtamu da manzon rahama(ﷺ), wanda yadamu da damuwar mu, meson kowa ya shiga Aljannah, ALLAH  ka sanya muna ciki.
.
*'yan uwa dukkan wani me zunubi, a ranan gobe qiyama se an mar hisabi, koya shaa! ko a kama shi!!, sakamakon kasancewan mu Yan adam masu rauni, hakan yasa kullum muna cikin zunibi!! se ALLAH yace;-*
 "...LALLE ALLAH YANASON MASU TUBA KUMA YANASON MASUTSARKI"   awani gurin yace  ''DA ANBATON ALLAH AKE SAMUN NUTSUWA".
.
Annabi alaihissalam ya koyar da sahabbai istigarai me girma, wanda harta kai ana kiranta da shugaban istigfari.
.
Tabbas badan muna tuba ma ALLAH ba, da tuni an shafar damu daga doron qasa.
.
Kasancewar zunuban mu sunyi mana yawa!!
.
shiyasa nayi tinanin tuna tar damu wannan addu,an dan mu sake hadda ce ta, wato *sayyidil istigfari*
_________________________________________
.
*اللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي لَّا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ، خَلَقْتَنِي وَأَنَا عَبْدُكَ، وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ مَا اسْتَطَعْتُ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ، أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ عَلَيَّ، وَأَبُوءُ بِذَنْبِي فَاغْفِر لِي فَإِنَّهُ لَا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا أَنْتَ*
.
*Allaahumma 'Anta Rabbee laa 'ilaaha 'illaa 'Anta, khalaqtanee wa 'anaa 'abduka, wa 'anaa 'alaa 'ahdika wa wa'dika mas-tata'tu, 'a'oothu bika min sharri maa sana'tu, 'aboo'u laka bini'matika 'alayya, wa 'aboo'u bithanbee faghfir lee fa'innahu laa yaghfiruth-thunooba 'illaa 'Anta.*
_____________________________________________

_*"YA ALLAH kaine ubangiji na, babu abin bautawa da gaskiya SAI kai. Kai ka halicceni, kuma ni bawanka ne, kuma ina kan alqawarin dana yimaka ( na kadaitaka da bauta)  akuma alqawarin d kayimin ( nashigar da wanda baiyimaka shirk ba, gidan Aljannah) gwargwadon ikona. Ina neman tsarin-ka daga sharin abinda na aikata, ina tabbatar da ni'imar ka gare ni, kuma ina tabbatar da zunubi na; ka gafartamini, domin ba bai gafarta zunubi se kai)"*_
.
_(Bukhari 7/150, -Nasa'i, da-Tirmizi.}_
_________________________________________
 Karka 6ata lokacin ka akan ibadan da ba daga Annabi  (ﷺ) take Ba.
dan haka yanada kyau duk abinda zamuyi in ya shafi addini to mu tabbatar munada hujja me kyau.
.
*Manzon ALLAH yace duk wanda ya karanta ta, da safe ba abinda ze hanashi shiga aljanna sedai mutuwa* (in baka shigaba to baka mutu ba, matuqar kana kan aqida ingan tacciya).
.
Haka zalika inka karanta da yamma, *amma duk dahaka anason ka  karantata da kowana lokaCi bayan kayi na safe da yamma.*
.
Sannan daga cikin falalan ta tana kankare zunubi me tsoka  wanda ya guda na tsakanin ka  ALLAH.
.
_Kasani me karatu Allah fa baya yafe lefin wani akan wani idan ka cuci wani to Allah ze bi masa hakkinsa koda kayi wannan Adu,ar bazata hana a tambayeka hakkin wani ba a lahira dan haka ka gyara tsakanin ka da Allah sannan kadawo ka gyara tsakanin ka da mutane._
.
_Sannan akwai wani hadisi shima a cikin bulugul maram inda Annabi   (ﷺ) yace: duk wanda yake karanta *Ayatul kursiyu* da *Kul'huwallahu* qafa uku a ko wace salla ta farilla to babu abinda ze hanaka Shiga Aljanna sedai in baka mutuba._
.
_Bukhari da Muslim ne suka rawai to shi ibn Hibbana ya ingantashi._

*Yan uwa akwai addu'oi dayawa ,idan mundage dayinsu zasu rabamu da fadawa bidi,a dakuma shirka da kuma dena ziyar tan bokaye..*
_______________________________________
     _lucture mu nagaba in sha ALLAHU 👉🏿(KIYI HANKALI DA QAWA YENKI DANGANE DA NEMAN MAGANI)  tsokaci duk wanda yaje wajen boka ko dan duba hakiqa ya kafurta inbaiyi imandashi ba baza,a kar6i sallan sa na kwana 40 ba!!!_
________________________________________
Dan uwanku a musulunci
.
*Muhammad Auwal Abu-Ja'afar*
*Al-potiskumawi*
.
08/03/1438;:;: 08/12/2016
.
→ MasU buqatan kasan cewa damu a whatsapp.
+2347035269582
+2348133238265
 tare da cikakken suna da kuma cikakkiyar sallama. don samun karatuttukan mu a facebook, saikubi, mobile.facebook.com/Khulafaur-Rashiidun-1812718708973541/ Subhanak Allahumma wabi hamdika Nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka
Wana tubu ilaik.
.
Kuna iya samun mu ta wannan addreshin
http://Www.khulafaurrashidun.blogspot.com
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support