Monday, 24 June 2019
Home »
» BADA KUDIN KASHEWA, BA WAJIBI BA NE AKAN MIJI !- Dr Jamilu Yusuf zarewa
BADA KUDIN KASHEWA, BA WAJIBI BA NE AKAN MIJI !- Dr Jamilu Yusuf zarewa
*Tambaya*
Assalamualaikum malam, Dan Allah ga wata tambaya ataimaka Mana da amsar ta, wata aminiya tace take so a taimaka mata, ita dai ta kasance mijin ta yana da Hali sosai kuma kullum Yana Mata duk laluranta wadanda Allah ya daura mishi a kanshi, to Amma ba ya daukan kudi haka kawai ya ba ta, to shine ita kuma sai tayi ma mijin karyan cewa wasu masu neman taimako sun zo da lalura sun ce Dan Allah ya taimaka musu, to idan ya bayar se ta rike, kokuma idan masu neman taimakon na gaskiya suka zo in ta fada mishi in ya ba ta se ta cire wani Abu aciki ta ba su sauran, shine ta keso taji wannan kudin da ta ke ci, menene matsayin hakan?
*Amsa*
Wa'alaikumus Salam, In ta yi haka ta ci haramun, ta kuma yi Algus, Annabi S.A.W. yana cewa "Wanda ya yi Algus ba ya cikinmu" kamar yadda Muslim ya rawaito.
Allah da Manzonsa ba su wajabtawa miji ya bawa matarsa kudin kashewa ba, abin da aka wajabta masa shi ne Ci da ita da Shayar da ita, yi mata Sutura, da yi mata duk abin da rayuwarta ba za ta ta fi ba sai da shi gwargwadon halinsa, kamar yadda ayar suratu Addalak da hadisai ingantattu suka tabbatar.
Bada EXtra kudi ba wajibi ba ne, tare da cewa kyautatawa iyali abu ne mai kyau, Annabi (S.A.W) yana cewa "Mafi alkairinku shi ne Wanda ya fi kyautatawa iyalansa", wannan sai yake nuna cewa: Mijin da yake bada kudin kashewa ya fi wanda ba ya bayarwa.
Babu bukatar ta bi ta hanyar Algus, idan ta lallabi mijinta, ta yi masa biyayya, za ta same shi a hannunta.
Allah ne mafi sani
*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*
24/01/2019
0 comments:
Post a Comment