Monday, 24 June 2019
Home »
» FATAWAN RABON GADO (193) - Dr Jamilu Yusuf Zarewa
FATAWAN RABON GADO (193) - Dr Jamilu Yusuf Zarewa
*Tambaya*
Assalamu Alaikum
Mallam tambaya ta akan rabon gado ne.
Mutum ne ya mutu,ba Mata,ba yaya,ba iyaye sai kakarsa wacce ta haifi mahaifinsa da Dan uwa wadda suke uba daya sai wadanda suke uwa daya. To mallam ya rabon gadonsa zai kasance?
Hafizakallah.
*Amsa*
Wa alaikum assalam , za'a raba gida (6), a bawa kakarsa kashi daya, 'yan uwan da suka hada uwa kashi biyu, ragowar sai a bawa dan'uwansa li'abbi.
Allah ne mafi sani
*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*
06/01/2019
0 comments:
Post a Comment