*HUKUNCIN SALLAR QASRU-8!!!???*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Taken Lekca........
.
*SALLAR QASRU!!!!??*
.
Wannan shine bayani na takwas****
.
Cigaba***
.
.
_Acikin Alwajiz fi fiqhus sunnah, malam yace malamai sunyi sabani gameda nisanda tafiya zatakai kafin ayi mata qasru, Ibnul Munzir ya hikaito sabanin malamai samada maganganu 20 gameda nisanda tafiya zata kai kafin ayi mata qasru, wato kenan kamar yanda nagaya muku abaya, ita qasru kusan duk wata gaba da zaka dauka nata seka tarar anyi sabani acikinta, toh shiyasa zeyi wahala ayi magana akan sallar qasru batareda kayima wani raddiba***_
.
_Shi kansa Imamu malik acikin muwadda, babi guday yabude akan wannan matsalar ta nisanda tafiya zatakai kafin ayimata qasru, toh amma shima acikin babin zakuga hadisanda yakawo kusan gaba dayansu sunacin karo da juna, wanda imamu malik akarshe kawai seya zabi guda daya daga cikin maganganunda yakawo kawai yace shi kam yafison wannan, wato itace buridi hudu***_
.
_Acikin Mudauwanah kuma imamu Malik cewa yayi kawai dazarar kafita daga garinku toh kawai kafara qasru***_
..
_Imamul qurdubi yakawo ruwayar Harith dan Abu rabi,ah cewa shi alokacinda yayi shiri zeyi tafiya sekawai yaima abokan zamanshi limanci kuma qasru yayi, agidanshi bema fara tafiyarba, shine qurdubi yace: shi yana fassara *(DARABTUM)* da Allah yafada awaccan ayar, da ma,anar *(AZAMTUM)* kamar yanda bayani yagabata abaya***_
.
_Har ila yau qurdubi yakawo fahimtar Imamu mujahid wanda shi yana ganinma matafiyi baze fara qasruba aranarda yayi tafiyar harse dare yayi tukunna sannan zaka fara qasrun***_
.
_muma dai anan bazamu iya yanke hukunciba gaskiya dan sabanin yayi yawa wallahi kuma dukkansu suna karo da juna, ammadai bari muji abindasu Ibn taimiya zasuce kafin musan tudun dafawa***_
.
_Ibn qudama yana cewa idan da zaka hado kakaf sabaninda akayi gameda qasru, katara maganganun wayanda suke cewa sai tafiya takai nisan kaza sannan ake mata qasru, kokuma sai tafiya iri kaza akeyiwa qasru, Ibn qudama yace su kansu zaka samu maganganunsu sunacin karo da juna, ibn qudama yace idan kagama tara maganganun toh zaka samu wanda yake cewa sai ankai wani nisa bashida hujjah, yace: amma hujjah tana wajen wanda yace maka kawai duk tafiya kayi qasru, kuma bai kayyade maka nisaba***_
.
_Ibn qudama acikin mujallad na uku Almugni yace: duk wanda zaice maka se tafiya takai nisan kaza kokuma kwanaki kaza akeyin qasru toh wannan yanaso yarabakane da sunnar Annabi muhammad***_
.
_Ibn Taimiya acikin fatawa yace wannan maganar ta ibn qudama baidace asamu wani mutum yana saba mataba, saboda yace inhar sunnah kakeso toh Allah da manzonshi basuce ga wani adadin tafiyarda zakayiba kafin kayi qasru, kuma basuce sai tafiya iri kaza akeyiwa qasruba, ibn taimiya yace manzon Allah har yamutu baice se tafiya takai nisan kaza kafin ayi qasruba, kuma har yabar duniya baice inka zauna agari kwana kaza kadena yin qasruba***aduba majmu,u fatawa mujallad na 23, yace duk mutuminda yace maka sai tafiya takai nisan kaza akeyin qaaru toh wannan maganar tashi babu ita Alittafin Allah kuma babu ita a sunnar Annabi muhammad***_
.
_Ibn qayyum Aljauziyya acikin zadul ma,ad mujallad na farko shafina 481 shima yace: manzon Allah har yabar duniya baice idan kayi tafiya kwanaki kaza toh kayi azumi, kuma baice inkayi kwanaki kaza kacika sallah, kawai yanda Allah yace acikin qur,ani idan kayi tafiya toh karama azumi awasu ranaku nadaban, baice inkayi kwanaki kaza kacika azumiba, yace amma duk wanda zaice maka ga wasu kwanakinda zakayi qasru toh wannan maganar bata ingantaba kuma bata cikin sunnar Annabi muhammad (s.a.w)***_
.
_Saboda haka abinda yafi dacewa shine mudauki waccan maganar ta Ibn Qudama semu gina hukuncinmu na karshe akanta, yanzu dai kunji irin yanda malamai suka tafka wayannan sabani, toh kuma duk wanda kadauka aciki toh sauran kuma kayi musu raddine fa***_
.
_Misali idan kace mutum baze fara qasruba harse ya wuce gonaki, toh kaga kayi raddima wanda yace kana iya farawa tun kana gida, sannan kuma wanda yace bazaka fara aranarda kayi tafiyarba shima kaimasa raddi, gakuma wanda yace sai kaci mil uku shima kaimasa raddi, ga wanda yace sekaci buridi uku shima kayimai raddi, ga wanda yace gidaje zaka wuce ba gonakiba shima kai masa raddi, gakuma wayanda sukace kwata kwata ba,ayin qasrun sai ahalin tsoro kaga suma kai musu raddi, toh yanzu dan Allah menene mafita yanda zakaima wayannan mutanen adalci batareda kayima kowannensu raddi ba????_
.
_Sannan kuma idan kace mudauki fahimtar malamanda sukace qasru ba,a wuce sati biyu anayi, in mutum yawuce sati biyu sai ya cika sallah, toh kaga semuce wannan maganar taka raddi ce ga mazhabar malikiyya da shafi,iyya dasu imamu laisu da dabari, wayanda sukace kwanaki uku kawai akeyi, kuma raddi kakeyima su imamu Ahmad dasukace salloli 21 kawai akeyi, sannan kuma suma wayanda sukace qasru batada iyaka suma kayi musu raddi****_
.
_Yawaitan wayannan sabanin shine yasa mukace arike waccan maganar ta Ibn Qudama, wato mutattara musu sabaninsu mu ajje musu mukoma mudauki zahirin ayar qur,ani da hadisin manzon Allah (s.a.w)***_
.
_kenan semuce nafarko dai sunnah shine duk sanda kayi tafiya toh kayi qasru koda kuwa tafiyar taka ta sabon Allah ce, saboda Allah da manzonshi basu kebance wata tafiya sukace ita ba,a yinmata qasruba****_
.
_Na biyu kuma koda shekaru nawa zakayi a garinda kaje toh ya halasta kayi qasru harse kadawo, saboda aikin manzon Allah (s.a.w) ya nuna hakan, tunda ayakin tabuka be dena qasruba har seda yadawo gida, hakama zamanshi a makka kwanaki goma a hadisin Anas, awani hadisin kuma kwanaki 19***_
.
.
_Sai abiyomu acikin bayani nagaba zamu cigaba in Allah yaso****_
.
.
_Almajirinku kamar kullun_
.
```Jameel Alhassan Haruna Kabo```
_(Abu khausar)_
.
.
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
https:/t/m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka Wanatubu ilaika

0 comments:
Post a Comment