Tuesday, 20 November 2018
Zan Iya Auran Wanda Ba Shi Da Uba ? - Dr Jamilu Yusuf Zarewa
Tambaya
Assalamu Alaikum, Don Allah Malam, wata dalibata ce ke neman shawara kan auren wani mutumin kirki, amma baida uba !!!
Wane irin kalubale ku ke hange a kanta, a yanzu da nan gaba?
Me ye mafi alkhairi a gare ta?
Jazakumullahu bikhairin Malam. Bissalam
Amsa
Wa alaikum assalam
Mutukar ta yarda da addininsa da kuma dabi'unsa tana iya auransa kamar yadda hadisin Tirmizi ya tabbatar.
Kasancewar an haife shi ba ta hanyar aure ba, ba laifinsa ba ne, Allah ba ya dorawa wani laifin wani.
In dai shegantuwarsa ba ta shahara a tsakanin mutane ba, ta yadda nan gaba za'a dinga aibanta abin da kuka haifa tare, kina iya auransa, tun da mutumin kirki ne.
Duk da cewa ya halatta a shariance ki auri wanda ba'a san mahaifinsa ba, saidai idan kika ji tsoran tozarta zuriyarki, to ana barin halal don kunya, kamar yadda Hausawa suke fadi kuma dalilin sharia ya tabbatar.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
17/11/2018
0 comments:
Post a Comment