Duniya makaranta !! (fitowa ta 33) dr.mansur ibrahim sokoto ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday 1 August 2017

Duniya makaranta !! (fitowa ta 33) dr.mansur ibrahim sokoto

DUNIYA MAKARANTA

Fitowa ta 33

166. Kada ka bari giramanka ya fadi a kan kalma guda daya da za ka sosa kaikaiyin bakinka da ita. Kada ka bari tuntuben guda ya zubar maka da mutunci.

167. Kada ka sa ranka cewa mutane duk za su so ka. Zukatan mutane a kullum cikin Canji suke; abin da suka so yau, shi suke kii gobe.

168. Kauyanci shi ne ka yi kuri da babbar riga ko fankaceciyar mota ko dankareren gida a birni alhalin iyayyenka na kauye suna cin bushashiyar gurasa.

169. Duk kyawon da kake takama da shi duniya ke cinye shi. Duk kyawon da kake bukata, a lahira an yi tanadin fiye da shi. Me ya sa muke son duniya muna manta lahira?

170. Aiki kadan mai dorewa ya fi yawan surrutu mai wucewa.


Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

8/11/1438
1/8/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support