HASKEN BASIRAR MUMINAI :
Basirar hangen nesa (WATO FIRASA) Wani haske ne wanda Allah Madaukakin Sarki yakan sanya acikin Zukatan Zababbun Bayinsa muminai. Albarkacin wannan hasken, duk abinda suka fa'da sai kaga ya kasance. Domin kuwa Annabi (saww) da kansa yayi shaidar haka inda yake cewa :
"KUJI TSORON FIRASAR MUMINI. DOMIN SHI YANA KALLO NE DA HASKEN ALLAH".
Hasken Firasah ba ya shiga zuciyar mutum har sai an tsaftace zuciyar daga bakin cikin duniya, kuma an tsarkaketa daga dauɗar nan ta sa'bon Allah, da Gurbatattun halaye, har ma da wasu halattatyun abubuwan don tsantseni.
Daga nan sai Madubin zuciyar ya zama wankakke yadda zai iya karbar kowanne irin hasken gaskiya.
Misalin masu irin wannan baiwar daga cikin Sahabbai da Magabata, akwai Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (ra) ya kasance yana cewa : "Babu wani wanda zai tambayeni game da wani abu fache sao na gane shin Shi din Malami ne ko ba Malami bane".
Watarana Imamush Shafi'iy da Imam Muhammad bn Hassan (Allah shi Qara musu rahama) suan zaune acikin Filin kusa da Ka'abah, sai ga wani mutum atsaye abakin kofar shigowa Masallacin.
Sai daya daga cikinsu yace : "Ian ganin Wancan Mutumin Kafinta ne". Sai dayansu kuma yace "A'a Makeri ne".
Daga jin haka sai wani daga cikin mutanen dake wajen yaje ya tambayi Mutumin game da haka. Sai yace : "Da chan ni Kafinta ne. Yanzu kuma ni Makeri ne".
Haka Sayyiduna Umar bn Al-Khattab (ra) ya kasance da zarar ya kalli mutum, yakan iya bada labari game dashi. Kuma idan aka tambayi mutumin sai a tarar kamar yadda Sayyiduna Umar 'din ya fa'da.
Duk wanda yake so ya samu haske da baiwa irin na Manyan Bayin Allah Salihai, to sai ya gyara zuciyarsa kuma yayi aiki irin nasu. Domin komai yawan ayyuka ba zasu amfanar dakai sosai ba, sai bisa gwargwadon yadda zuciyarka ta gyaru.
Zauren Fiqhu (04-11-1438 28-07-2017)

0 comments:
Post a Comment