WANKAN GAWA DA YADDA AKEYINSA.Via: Sunnatun Nabawiyya.DON ALLAH MU KARANTA KUMA MUYI SHARING GA 'YAN UWA DOMIN NAKARANCI YAZAMA MATSALA TA WANNAN AL'UMMA IDAN ANYI MUTUWA SAI KAGA AN RASA MAIYIN WANKA, KO KUMA KAGA MALAMIN DAZAIYI WANKAN YANA TA MULKI SAI LOKACIN DAYAGA DAMA ZAIZO YAYI WANKAN.FALALAR WANKAN GAWA.
-Imam Hakim ya rawaito hadisi wanda Manzon Allah (s.a.w) yake cewa:‘’Duk wanda ya wanke mamaci, kuma ya rufa masa asiri, Allah Zai gafarta masa sau arba’in.’’A wani hadisin kuma Manzon Allah (s.a.w) Yace:”Duk wanda ya wanke mamaci kuma yarufa masa asiri, to Allah zai tufatar dashi daga cikin tufafin Gidan Aljannah Kwarra, (wato Launin Tufafin).SHARUDDAN WANKAN GAWA:Daga cikin sharaddan wankan gawa sune:{1}. Ana bukatar wadanda zasu wanke mamacin su zamanto makusantan sa misali:Iyaye.kanne ko yayyek“ya”yansa da sauransu).{2}. Ana bukatar maza su jibinci wanke maza, suma mata su jibinci wanke mata (sai dai Miji zai iya wanke Matarsa hakama Mace zata iya wanke Mijinta).{3}. Ba sharadi bane lallai sai anyi amfani da ruwan zafi.YADDA AKE YIN WANKAN GAWAAna yin wankan gawa mara-mara ne misali:Sau Uku (3) koBiyar(5) koBakwai(7) koTara(9)).Hakan ya tabbata daga Manzon Allah (s.a.w) a cikin hadisin Ummu Adiya (R.A).Wadanda zasu yiwa mamaci wanka su zasuyi la’akari suga wanka nawa yadace suyi masa.Da farko dai kafin a fara wankan da akwai abubuwa guda Uku (3) da za’a fara yiwa mamacin.Sune kamar haka:{1}. Za’a cire masa suturar da take jikinsa, amma za’a sami dan kyalle a rufe masa al’aurarsa.{2}. Bayan anyi abu na sama, sai kuma ayi masa tsarki, na bangaren mafuta biyu.(Bawali da Gayadi).{3}. Idan macece , za’a tsefe kitson da yake kanta, a wanke kan, sannan ayi Lallabi uku a kan ( wato Kalba guda Uku).Sai a kwantar da Kalbar tayi bayan kan nata.Idan namiji mai kitso ne sai a warware kitson gaba daya.YADDA AKE WANKA SAU UKU (3)Idan masu yiwa mamaci wanka sun zabi suyi masa wanka sau uku, to bayan sun gama abubuwan da suke sama saisu farawankan.Da farko dai zasu tanadi ruwa kashi Uku (3), kowanne ruwa za'ayi wanka daya dashi.(RUWAN FARKO)Wannan wankan za'ayi wa mamacine wanka irin Wankan Janaba.Da farko za’a fara yiwa mamaci alwalane, kamar irin alwalar Sallah, sai dai wajen kuskurar baki da shakarhanci za’a shafa masa ruwane kawai a bakin da hancin.Bayan anyi masa alwala, sai kuma azuba ruwa a kansa a wanke masa har sau uku, sannan kuma a wanke tsagin jikinsa na dama sannan na hagu.(RUWA NA BIYU)Bayan anyi masa wanka na sama wato na Janaba, sai kuma asami Sabulu ko Magarya ko Kanwa, a wanke mamacin dashi.Wato za’a sami Soso da Sabulu a cuda jikinsa sosai (Kamar dai yadda ake wanka irin na Soso da Sabulu, saidai za’a iya amfani da Magarya ko Kanwa a maimakon Sabulun).Bayan angama cuda shi sai a dauraye Kumfar da wannan ruwan.(RUWA NA UKU)Bayan anyi masa wanka na sama, wato na Soso da Sabulu, to sai kuma a sami ruwa na karshe wato na Uku a zuba Turare mai kamshi(Sosai) a ciki, sannan sai a wanke mamaci da shi.Amfi son ayi amfani da Turaren Kafur, to amma idan ba’a same shiba to za’a iya amfani da duk wani Turare mai kamshi sosai.Bayan angama wankan Turaren, sai a tsane jikin mamacin asa masa Likkafani.YADDA AKE YIN WANKA BIYAR (5), KO BAKWAI (7),KO TARA (9).Idan masu yiwa mamaci wanka sun zabi suyi masa wankabiyar (5), ko bakwai(7), ko tara(9).To wanka na biyu(2) wato na Soso da Sabulu shi zasuyi ta maimaitawa.Amma dolene na Janaba shine a Farko, sannan na Turare shine a karshe.MISALIN YADDA ZA AYI WANKAN SAU BIYAR(5).{1}. Na farko shine na Janaba{2}. Na biyu shine na Soso da Sabulu{3}. Na Uku shine na Soso da Sabulu{4}. Na Hudu shine na Soso da Sabulu{5}. Na Biyar shine na Turare.Allah kasa mucika da imani.Dan Allah kudinga yin like da comment ko kuma kuyi share dinsa domin 'yan uwanku su amfana.
0 comments:
Post a Comment