TAMBAYA TA 2161
****************
Assalamu'alaikum Malam muna lafia, ya aiyuka ya Dalibai? Allah yayi mana jagoranci na alheri. Amin.
Malam Dan Allah a taimaka mana da maganin fitsarin kwance, wata diyar yar'uwata ce ta kusa shekara 10 take fama dashi.
Sannan kuma ina barar addu'arka data dalibanka akan Allah ya kawo mani mijin aure mafi alheri. Amin. Jazakallahu Khair. Pls hide my I. D.
AMSA
***
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Ita wannan matsalar ana iya shawo kanta ne ta hanyoyi guda biyu kamar haka :
MAGANI : A nemi kwayoyin habbatus sauda, a rika yiwa yaro hayaki dasu. Kuma yana dan tsugunawa akan hayakin. Sannan kuma a rika gauraya masa habbatus sauda din yana shan cokali guda tare da zuma. Ko kuma ya shafe jikinsa da man Habbatus sauda din wanda akayi tofi acikinsa. In sha Allahu zai dena.
2. ADDU'A : Arika tofa masa wannan addu'ar, ko kuma akoya masa ya rika yinta da kansa, ko kuma a rubuta masa ajikin takarda ya sanya ajikinsa yayin da zai kwanta.
Kamar yadda aka ruwaito daga Abdullahi bn Amru bn Al-As Sahabin Manzon Allah (saww) yana rataya ma 'ya'yansa Qanana wannan addu'ar. Gata nan kamar haka :
"أعوذ بكلمات الله التامات من غضبه وعقابه ومن شر عباده و من همزات الشياطين و أن يحضرون".
'A'udhu bi kalimatil Laahit tammati min ghadhabihee wa 'iqabihee wa min sharri ibadihee wa min hamazatish shayateen wa an yahdhurooni.
FASSARA : Ina neman tsari da cikakkun kalmomin nan na Allah daga fushinsa da Uqubarsa, kuma daga sharrin bayinsa, kuma daga sharrin fizge-fizgen shaitanu, kuma (ina neman tsarinsa) kada su halartoni.
In sha Allahu koda babban mutum ne yake fama da matsalar fitsarin kwance, in dai ya lazimci wadannan abubuwan tare da gaskatawa zai ga biyan bukatarsa.
WALLAHU A'ALAM.
Muna rokon Allah da albarkar sunayensa da siffofinsa da kalmominsa, ya baki Miji nagari. Ya tsare miki mutuncinki da imaninki dake da dukkan dalibanmu da 'yan uwanmu Mata marassa aure. Ameeen.
DAGA ZAUREN FIQHU.
0 comments:
Post a Comment