*HUKUNCIN MATAR DA TA YI AURE KAFIN A SAKETA*
*TAMBAYA :*
Assalamu alaikum Malam. Mace ce aka aurar tana 'yar-shekara 14 ga wanda bata so, to sai mijin yayi tafiya har tsawon wata hudu (4) To sai matar tasa aka rubuta mata saki tace ya saketa, bayan ya dawo yace bai saketa ba, amma ba'a yarda ba. Da ta kare idda tayi aure da wani har suka haihu, daga baya kuma suka rabu, kuma yanzu ta ga musifu suna ta samunta, sai take tunanin ko wancan abin ne da tayi. Tana neman fatawa, ina hukuncin ta, da yaran data haifa da miji na biyu?
*AMSA:*
Wa alaikum assalam
Malam amsar wannan tambaya yana da mutukar wahala, saidai na nemi taimakon wasu daga cikin malamaina, ga abin da na samo :
*1.* Abin da ta yi mummuna ne a shari'ar musulunci saboda ta yi aure cikin aure.
*2.* Zaman da su ka yi da mijinta na biyu, a matsayin mazinaciya take, saboda haka duk kwanciyar da suka yi da wannan mijin na ta zina ne.
*3.* Yaran da su ka Haifa da mijnta na biyu, 'ya'yansa ne, tun da bai san abin da ya faru ba a baya.
*4.* Har yanzu igiyar aurenta ba ta warware ba tsakaninta da mijinta na farko, saboda haka har yanzu ita matarsa ce saidai in ya sake ta.
*5.* Mijinta na farko, zai iya dawowa da ita, ba tare da sake daura aure ba, saidai dole sai bayan ta tuba, domin ita a matsayin mazinaciyya take, kuma Allah ya hana auren mazinaciya.
*6.* Ya wajaba a gare ta ta yawaita istigfari saboda girman zunubin da ta aikata.
*7.* Zai yi kyau su je wajan Alkali wanda ya san shari'ar musulunci, domin ya yi musu hukunci.
Allah ne mafi sani.
*Amsawa*✍🏻
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
30/6/2014

0 comments:
Post a Comment