HUKUNCIN 'YAN KASUWA MASU QARIN FARASHI
TAMBAYA TA 2011
********************
As-salamu Alaikum malam mai zauren fiqhu godiya da Fatan Alkhairi A gareka Allah yakara daukaka ga wannan zauren Naka,
Malam ina son nayi tambaya ce Akan yanayi ta kasuwanci domin ni ina kasuwanci ne ina saye da sayarwa sai Naji ance abinda Nike sayarwa ya samu karin kudi Daga kasuwa ko Daga kamfani shin ya halitta nima nayiwa nawa ababan da Nike sayarwar karin kudi domin in zanje kasuwa sai nayi cikon kudi ba zan tsameshi kamar yadda Nike sayarwa in banyi karin kudin ba, Allah yabada ikon amsa
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Irin wannan abinda kake tambaya akansa, bai halatta ba. Abinda ake so ga dan kasuwa shine ya zamanto Mai gaskiya mai son gaskiya, kuma mai aiki da gaskiya acikin dukkan harkokinsa.
Abu Sa'eed Alkhudriy (rta) yace Manzon Allah (saww) yace : "DAN KASUWA MAI GASKIYA, MAI AMANA, YANA TARE DA ANNABAWA DA SIDDIQAI DA SHAHIDAI (ARANAR ALQIYAMAH KENAN).
(Imam Tirmidhiy ne ya ruwaitoshi acikin kitabul buyu'i kuma ya ingantashi).
Wani hadisin kuma daga Isma'il bn Ubaid bn Rifa'ah, daga babansa daga Kakansa (rta) yace Ya fita zuwa wajen Sallah tare da Manzon Allah (saww) sai Manzon Allah (saww) yaga mutane suna ta cinikayya atsakaninsu.
Sai yace "YA KU TARON ATTAJIRAI!!". Sai suka amsa kiransa, suka 'daga kayuwansu da idanuwansu gareshi. Sai yace :
"HAKIKA SU 'YAN KASUWA ZA'A TASHESU NE ARANAR ALQIYAMAH AMATSAYIN FAJIRAI. SAI DAI WANDA YAJI TSORON ALLAH, YAYI BIYAYYA, KUMA YAYI GASKIYA".
(Tirmidhiy ne ya ruwaitoshi).
Don haka abinda yafi gareka shine ka saukaka ka bayyanar da gaskiya. Duk lokacin da ka koma domin sayowa, idan ka samu anyi Qarin kudi kaima sai ka Qara. Amma idan ka tarar anyi ragi kaima sai ka rage.
Annabi (saww) yayi addu'a yace : "ALLAH YAJI QAN MUTUM MAI SAUKAKAWA IDAN ZAI SAYI ABU, MAI SAUKAKAWA IDAN ZAI SAYAR.... ".
Idan kayi haka in sha Allah zaka shiga cikin addu'ar Manzon Allah (saww). Kuma zaka samu albarka mai yawa acikin kasuwancinka.
WALLAHU A'ALAM.
ZAUREN FIQHU
0 comments:
Post a Comment