Alkaki da Ruwan Zuma - Dr.mansur ibrahim sokoto ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Monday 8 January 2018

Alkaki da Ruwan Zuma - Dr.mansur ibrahim sokoto



ALKAKI DA RUWAN ZUMA

Fitowa ta 001

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinqai
Godiya ta tabbata ga Allah. Tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta.
Gabatarwa
Da yawa daga cikin mutane suna tsammanin malaman Sunna da suka ce
a kame baki daga kutsawa a cikin rikittan da suka faru a tsakanin iyayenmu
Musulmin farko sun faxi haka ne don suna son a voye gaskiya. Wannan kuwa
kuskure ne babba.
Tarihin magabata, musamman ma dai almajiran Manzon Allah Sallallahu
Alaihi wa Sallam na da banbanci da sauran tarihin mutane baki xaya. Dalili kuwa
shi ne, ba zaka iya raba tarihinsu ba da na maigidansu wanda shi ne Allah ya
xora ma alhakin tarbiyyar su da shiryar da su zuwa ga gaskiya.
Dalili na biyu kuma shi ne kasancewar su mutanen da Allah ya zava kuma
ya fifita su albarkacin zamowar su tare da amintaccen Allah; masu ba shi
shawara, masu taimakon sa, masu bin sa sallah, masu ba shi zakka, masu
tanyon sa jihadi, masu ba shi aure, masu maqwautaka da shi, kuma waxanda
tarihi ya tabbatar sun fifita shi a kan kowa da kowa. Kai, har ma sun kashe
iyayensu da danginsu a wajen kariyar sa. Haka ma duk abin da suka mallaka na
duniya sun sadaukar da shi domin wannan farin masoyi da basu tava haxa kowa
da shi ba.
Wannan magana ba na-ji-na-ji ba ce, maganar Allah ce. Mutum har ya kan
yi mamakin irin yadda wannan lamari zai shige ma wasu duhu alhalin ga shi nan
varo varo a wurare cikin Alqur'ani da ba su qirguwa.
Sahabbai mutane ne kamar kowa ta fuskar cewa suna iya yin kuskure ko
laifi. Amma banbancinsu da sauran mutane shi ne, suna da tsarkin zuciya da
shaidar Alqur'ani. Ba ni zaton wannan magana ta buqaci a kafa mata hujja, sai fa ga wanda ba shi da wata masaniya sam sam game da Alqur'ani. Don haka idan
sun yi kuskure to, sun samu yafewar Allah da tabbacin su yardaddu ne, 'yan
aljanna.1
 Wannan shi ne dalilin da ya sa malaman Sunna suka fifita kame baki
daga faxin abin da ya gudana a tsakanin Sahabbai domin bakin rijiya ba wurin
wasar makaho ne ba. Wanda kuwa duk ya shagaltu da neman kurakuransu da
ayubbansu zai wayi gari yana raina su ko ya qyamace su alhalin Allah ya umurce
shi da darajanta su da qaunar su da yi ma su addu'a. Ka ga a nan shi ne ya faxa
ruwa. Daga cikin abin da ke nuna mana cewa, ba wai nufin malamai shi ne a
voye gaskiya ba, zamu ga ai duk tarihin nan da suka ce mu kame baki daga ce-
ce-ku-ce a kan sa su suka rubuta shi, ba su voye komai daga cikinsa ba,
sawa'un mai daxi da maras daxi, na gaskiya da na qarya. Sun hikaito mana ko
wanne a matsayin ruwaya da aka faxa kuma sun kawo wanda ya faxe ta.
Dalili na uku da ya sanya malaman Sunna sukar wannan matsayi shi ne
la'akari da suka yi da yadda tarihi ya gauraya da ra'ayoyi da son zuciya na
Daikaiku da na qungiyoyi wadanda ba su jin ciwon fesa qarya don cimma wata
manufa, ko aibanta wani ko gwarzanta shi. Ga shi kuma tarihi bai samu irin
hidimar da Hadisin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya samu ba na
cikakkiyar kulawa da tantancewa tare da banbanta ingantacce daga wanda ba
shi ba.
Bugu da qari kuma sai marubuta iri iri suka bayyana kowa da irin fassarar
da yake yi ma abin da ya auku. A dalilin haka, sai aka yi ta yi ma wasu riwayoyi
gyaran fuska, wasu aka sauya su, aka karkata alhairansu suka koma sharri,
wasu kuma aka qara masu matsayi suka kai inda ba su cancanta ba.

Duba alal misali: Suratul Hashri: 8-10 da Suratul Fathi: 18 da Suratul Mujadala: 22 da
Suratut Taubah: 100.

Littafin: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

Mu gamu a darasi na 2

25/4/1439
15/12/2017​

» Zauren Minbarin Malamai+2347037477743
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support