*YAYA HUKUNCIN SALLAR WANDA YASHA RAKE BAI KUSKURE BAKIN SABA*
الحمد لله الذي شرفنا بالإسلام وجعلنا خير أمة أخرجت للناس، صلى الله على محمد وآله وصحبه وسلم،
Amsa: cin wani abu ko sha, ko taba wani abu, ko sun batar mace, ko tabata dan sha'awa, baya karya alwala, balle yai tasiri a sallar mutum dan haka babu komai ga wanda yaci ko yasha yai sallah batare da ya kuskure bakin saba, saifa idan abunda yaci naman rakumine to wannan dole sai ka kuskure bakinka da nassin hadisin Manzan Allah salallahu Alaihi wasallam wannan ya tabbata.
Amma kuma kuskure baki bayan kaci ko kasha sunnah ne kuma abun sone, saboda dalilai da suka tabbatar da hakan,.
Daka Abdullahi dan Abbas Allah yakara musu yarda, Manzan Allah sallahu Alaihi wasallam ( ya sha nono sai yabukaci akawo masa ruwa ya kuskure bakinsa bayan yayi alwala, sai yace yana da naso, ma'ana ragowar dandanon nazama abaki,
Imamul nawawi yace: acikin wannan hadisin akwai mustahabbanci kuskure baki bayan anci ko an sha, bayan alwala, saboda abunda yaci ko yasha rogowarsa zai iya rage masa abaki,
Da kuma hadisin nu'uman wanda manzan Allah a yakin khaibar bayan sunje wani gari "suhaba'i" can wani garine dake gangaren khaibar, yai umarni akawo musu wani abunci ba,a samu ba sai assaweeq sai sukaci bayan la,asar sai sukazo yin sallar magriba, sai Annabi ya kuskure bakinsa sai sahabbai ma suka kuskure bakinsu,
acikin wannan hadisi akwai mustahabbanci kuskure baki idan akaci ko aka asha bayan alwala, duk cewa abuncin saweeq bashi da naso, amma dan ragowarsa dake tsakanin hakora da sauran guraren nabaki su zauna abakinsa.
والله أعلم،
***********************************
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
_*Tambayoyin*_ _*Musulunci*_
_*WhatsApp*_ _*Group*_
0 comments:
Post a Comment