Menene hukuncin namiji mai biye biyen mata bayan yana da aure iyalinsa tana iya kokarinta wajan bashi hakkinsa ?? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Monday 7 November 2016

Menene hukuncin namiji mai biye biyen mata bayan yana da aure iyalinsa tana iya kokarinta wajan bashi hakkinsa ??

*MENENE HUKUNCIN NAMIJI MAI BIYE BIYEN MATA BAYAN YANA DA AURE IYALINSA TANA IYA KOKARINTA WAJAN BASHI HAKKINSA.?*

الحمد لله والصلاة والسلام على محمد وآله وصحبه وسلم،

Amsa: Lallai wannan mijin bai kyauta ba kuma abun da yake aikatawa hadarine mai girma agareshi anan duniya da kuma lahira, kuma abun bakin cikine yakamata yagane bashi kadai keda hakki akanki ba, kema kina da hakki akansa ya nuna kulawa da kishi dakuma barin abunda duk zaibata miki rai, kozai saki damuwa matukar wannan abun basabon Allah bane.

Shine wanda shari'ar musulunci take kira da dayyus, wato sakarai shasaha wanda baya kishin matarsa ko kannensa mata ya kyalesu sakaka suna abunda sukaga dama, ko kuma baya kishin matarsa kwata kwata, kawai yadauki matarsa amatsayin mai dafa masa abunci ba ruwansa, zaije yaita mu'amala da wasu matayen, wannan sharrine mai girma, domin irin wadannan matayen ne in ba,a samu mai tsoran Allah ba, itama sai tafada wasu dabi'u da ababe marasa kyau, akwai wadanda tsabar lalacewa sune suke baiwa matayan nasu dama cewa suma suna iya yin mu'amala da kowa, hakika matarka tanada daraja da mutunci domin itace suturarka kamar yanda kur'ani yanuna, ba daidai bane kabarta gida kaje kana biyewa wasu akwararo, kuma ya kamata kasani wadannan  wadanda kake biyewa bawani abu sukafi taka matarba, kai takama tafisu kawai saboda su sun tube rigar mutunci suna fito na fito da Allah ne har kake ganin wani abu atare dasu, domin sudin kamar shaddar kasuwa suke kowa zai hausu yaikashi, lallai wanna miji naki yakamata yaji tsoran Allah yatuba yadena, kuma kici gaba da rokon Allah Allah ya shiryar miki dashi, sannan kibi duk wasu hanyoyi na hikima da fasaha kinunar masa abunda yake yana matukar kona miki rai, kuma kitunatar dashi lallai wannan mugun aikine yake, inda hali kihada da abokansa iyayensa da duk wanda kikasan yanajin nauyinsa danya dena wannan dabi,a yadawo gareki, inkinbi duk wadannan hanyoyin bai daina ba, kinemi taimakon Allah kawai araba aurenku Allah ya musanya miki da mai kishinki mai kiyaye addinin Allah madaukakin sarki,

Hadisi yazo daka manzan Allah sallahu Alaihi wasallam, daka abdullahi dan umar Allah  yakara masa yarda yace manzan Allah yace, ( mutane uku Allah yaharamta musu aljannah, wanda ya dawwama yana shan giya har yamutu, dakuma maiyawan sabawa iyayensa, dakuma dayyus sakaran dayake tabbatar da barna acikin iyalinsa baya kishinsu, ) Imamu Ahmad.

Malam haisami yace: acikin mu'ujamul zawa'id acikin hadisin akwai rawin da ba,a ambataba, amma sauran mutanen dasuka ruwaito shi dukansu amintattu ne, Dabarani ya ruwaito daka Ammar bin yasir manzan Allah salallahu Alaihi wasallam yace:

(Mutane uku, bazasu shiga aljannaba har abada, Mace mai kamanceceniya da maza, dakuma wanda yake shan giya har yamutu, da dayyus sokwan da baya damuwa da wanda yake shiga wajan ahlinsa, baya kishinsu.

A bisa wannan duk wanda yai duba da hadisn farko duk da hadisi nabiyu akwai  rauni acikin ruwayarsa, zai fahimci dayyus shine wanda yake kyale barna acikin iyalinsa tana wakana kuma baidamu ba, ko yake bada kofar da kowacce irin barna zata iya faruwa akan iyalinsa, domin duk wanda bai damu da matarsa ba baya kishinta yana bin wasu awaje, hakika yakyale babbar kofa ta faruwar fitina acikin iyalinsa. Sa'annan kuma wadda keda miji irin wannan kuma ta tabbatarda yana wannan biye-biyen matan, ba zargi bane to sai ta fara masa nasiha cikin hikima da kuma rokon Allah ya shiryar mata da mijinta da ci gaba da gyara jikinta sosai ta hanyoyin da suka halatta ( maganar gaskiya da yawan matanmu na arewacin qasarnan suna wasa da gyaran jikinsu ) da yawan mazaje shi yasa shaidan ke samun galaba akansu sai na wajen suke basu sha'awa kuma alhali ba komai suka fi na auren ba kawai su na auren basa gyara jikinsu ne, to idan tabi duk wadannan matakan tayi-tayi yaqi dainawa to sai ta janyo magabata a cikin lamarin, idan yaqi bari to zata iya neman rabuwa dashi Allah ya musanya mata da wani nagari saboda yana iya dauko musu wani ciwo can wajen fasikancin nasa. Allah ya kiyaye!

والله أعلم،

***********************************

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

_*��Tambayoyin*_ _*Musulunci��*_
            _*WhatsApp*_ _*Group*_

Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support