*ME YAKAMATA WANDA YAKE TUNANIN ACE YAZAMA KIRISTA*
الحمد لله والصلاة والسلام على من لا نبي بعده.
Alal hakika raunin imani shine ke kawo wannna tunani dakuma shedan, abunda yakamata ka dunga yi shine neman tsarin Allah daka shaidan kamar yanda Allah madaukakin sarki yace:
(وإما ينزغنك من الشيطان نزغ فاستعذ بالله إن هو السميع العليم)
Duk lokacin da shaidan yakawo maka wata fizga hari na mummunan aiki ko tunani kanemi tsari da Allah
Yazo acikin hadisi ingantacce manzan Allah salallahu Alaihi wasallam yace: shaidan zai zowa da yanku yadunga rayamar azuciya cewa wanene yahalicci kassai yace Allah wanenene ya halicci sammai yace Allah wanene yahalicci kaza yace Allah karshe sai ya dunga kawo cewa shi Allah kuma waya halicce shi, Annabi yace da kaji haka kacanjawa zuciyarka wani abun daban kanemi tsari daka Allah.
Hakika ni'imar musulunci ni'imace mai girman gaske, dan haka bazai taba yiyuwa shaidan ya kyaleka haka kawai kazauna lafiya ba, sai ya dunga kawo maka hari dare darana
Amma kakiyaye karka sake ka furta hakan inka furta malamai sukace kazama kafirin.
Sannan ka yawaita tuba zuwa ga Allah idan kasan kana tare da mutanen banza ka gaggauta canzasu da mutane nagari, idan kuma gurine kake tasirantuwa dashi ka kaurace masa, ka yawaita karatun alqur'ani da sauraron sa dajin wa'azuzzuka da halartar guraren da duk ake karantar da musulunci.
Sannan ka yawaita addu'ar manzan Allah salallahu Alaihi wasallam.
اللهم يا مقلب القلوب ثبت قلوبي على دينك،
Ya Allah mai jujjuya zukata ka tabbatar da zuciyata akan addininka
In sha'allahu zaka kubuta daka abunda kake ji na sha'war wani addini koma bayan musulunci.
والله أعلم،
***********************************
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
_*Tambayoyin*_ _*Musulunci*_
_*WhatsApp*_ _*Group*_
0 comments:
Post a Comment