July 2017 ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Monday 31 July 2017

*WAYE YA DACE YA YI MA MACE WANKAN GAWA? (fatawowin mata fitowa ta 2)

*WAYE YA DACE YA YI MA MACE WANKAN GAWA?*

Fatawowin Mata fitowa ta 2

*TAMBAYA:*
Waye ya dace ya yi ma mace wanka idan ta mutu?, kuma shin ya halatta Mace kafira wanda ba Musulma ba ta yi mace Musulma wanka idan ta rasu?. Sannan da shigar da ita Kabari sharadi ne dole sai Makusantanta, ko kuwa kowane Musulmi zai iya shigar da ita kabari?. Akwai wasu mutane shin ya halatta a bar su, su shigar da mace kabarinta?.

*AMSA:*
Musantan mace su ne za su yi mata wanka kuma za a yi la'akari da wanda suka fi kusanci daga cikin wanda za su iya kyautata wankan. Kuma ya halatta a wakilta kowace mace wanda za ta iya kyautata wanke ta, koda kuwa ba makusanciyarta ba ce. Haka nan ya halatta miji ya wanke matan shi, ita ta wanke shi.

Dangane da Mace kafira ta wanke Musulma, wannan bai halatta ba, domin wanke mamaci ibada ce, kuma Ibadan wanda ba Musulmi ba, bata inganta.

Dangane da shigar da mace kabarinta, ya halatta wani daga cikin Musulmi ya shigar da ita koda ba makusancinta ba ne, matukar zai kyautata haka.

Amsawa: Al-Lajnatu al-Daa'imah Lil iftaa'i.

A duba littafin فتاوى المرأة المسلمة shafi na 441.

✍🏼 Tattarawa:
*_Umar Shehu Zaria_*

Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
Share:

Masu hikima sunce ?? (fitowa ta 32) dr.mansur ibrahim sokoto

MASU HIKIMA SUN CE

Fitowa ta 32

146. Ba mai tunanin yin cuta sai mai nisan hankali.

147. Kakan ga taron munafukai har ka zaci shawararsudaya ce. Nan kuwa zukatansu daban daban ne.

148. Duk same-samenka na duniya iyakar, amfaninka da su zamanka na duniya, in ba ka tuna lahirarka cikinsu ba.

149. Komai gudun da kayi wa mutuwa, ba shakka za ta cim maka.

150. Idan hankalin mutum ya yi rauni sai ya rika damuwa da abin da bai shafe shi ba, kuma ya fita batun wanda ya shafe shi.

Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi

Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

7/11/1438
31/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

Duniya makaranta !! (fitowa ta 32) dr.mansur ibrahim sokoto

DUNIYA MAKARANTA

Fitowa ta 32

161. Karan dawa yakan sukunya ne idan yana dauke da alheri. Idan yan fanko sai ka gan shi tsaye kyam. Ba kowane mai daga kansa ne ya cancanci jinjina ba.

162. Mumini yakan yi adalci ko yana a cikin fushi. Yakan yi gaskiya ko yana a cikin matsi. Yakan daidaita ko yana a cikin damuwa

163. Idan ka kwantanta kanka da rayuwar mawadaci ka lura ya fi ka, to ka duba yanayin ibadarka ko ka fi shi? Fomin kada ya yi maka bugu biyu; ya ci nan kana kall, a ranar lahira kuma ya shige aljanna ya bar ka.

164. Gurgu na gaskiya shi ne wanda bai zuwa masallaci, makaho na gaskiyashu ne wanda bak duba Alkur'ani.

165. Idan ka dauka cewa, ba ka yin kuskure to wannan si ne kuskurenka na farko. Duk mutum dan tara ne, bai cika goma ba.


Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

7/11/1438
31/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

Masu hikima sunce ?? (fitowa ta 31) dr.mansur ibrahim sokoto

MASU HIKIMA SUN CE

Fitowa ta 31

141. Da al'amurran duniya da lahira na Allah ne.

142. Duk dan Adam Allah ya ba shi zuciya daya ne tak.

143. Mugun nufi bai taba cutar kowa ba sai mai shi.

144. Mai sani da marar sani ba su zama daya daidai.

145. Alheri ba shi da sakamako sai alheri.


Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi

Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

6/11/1438
30/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

Duniya makaranta (fitowa ta 31) dr.mansur ibrahim sokoto

DUNIYA MAKARANTA

Fitowa ta 31

156. Idan ka kyautata ma mutum za ka mallake shi. Idan ka wadatu daga mutum za ka zama tsaran sa. Idan kuwa ka bukatu zuwa ga mutum, to dole sai ka zamo bawansa.

157. Tuntuben harshe ya fi tuntuben kafa zafi. Na kafa saurin warkewa yake yi, na harshe kuwa illanta mutum yake yi har karshen rayuwarsa.

158. Ilimi ya fi kudi, kuma ya fi mulki. Kai, har lafiya ma ya fi ta. Kudi da mulki da lafiya duk suna gushewa. Amma Ilimi yana nan tare da mai shi ba su rabuwa.

158. Abin al'ajabi da lura: Masallatai suna cika ne bayan isowar liman, amma filayen kwallo suna cika tun kafin zuwan 'yan wasa.

160. Kada lamarin duniya ya dame ka. Duk abin da ke cikin ta na Allah ne. Kada sha'anin arziki ya dame ka. Domin daga wurin Allah yake fitowa. Kada ka samu damuwa a kan gobe, domin a hannun Allah take. Abin da ya kamata ya dame ka shi ne, neman ka samu yardar Allah.


Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

6/11/1438
30/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

(mp3) Waye mu'azu bin jabal ?? Sheikh musa yusuf asadussunnah

* FREE KHUDBAR .*


Mai Taken


*WAYE MU'AZU BIN JABAL.*


Tare da :- *Sheikh Musa Yusuf Asadus-sunnah (Hafizahullah).*


*Daga Masallacin Juma'a na yar kasuwa fake T/wada Kaduna .*

Ranar Juma'a
04/11/1438
28/07/2017

Domin sauko da wannan audio saiku danna wannan blue rubutu dake kasa 👇👇👇

DOWNLOAD AUDIO NOW

AYI SAURARE LAFIYA

ZAKU IYAYIN SHARE ZUWA SOCIAL MEDIA DINKU ANAN👇👇👇
Share:

(mp3) Al-aqitadatu sahiha 08- sheikh musa yusuf asadussunnah

*Karatun Littafin.*


*AL-AQIDATU SAHIHA.*


Darasi na (08).


Tare da :- *Sheikh Musa Yusuf Asadus Sunnah (Hafizahullah)*


*Daga Masallacin Malam Khamis Al-misirry Dake bye pass Kaduna.*


Ranar Alhamis
04/11/1438
27/07/2017

DOMIN SAUKO DA WANNAN AUDIO SAIKU DANNA WANNAN BLUE RUBUTU DAKE KASA👇👇👇

DOWNLOAD AUDIO NOW

Ayi saurare lafiya


Share:

Sunday 30 July 2017

Dalilin ziyara ta gidan Buhari da ke Landan - Reno Omokri

- Reno Omokri ya bayyana dalilinsa na kai ziyara gidan Buhari da ke Landan

- Ya bayyana rashin jin dadinsa na munafurcin mulkin Gwamnatin Buhari

- 'Satar Kudin Gwamnati ba shine kadai Cin Hanci da Rashawa ba' - Omokri

Tsohon hadimin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya bayyana dalilin sa na ziyartar 'Abuja House' da ke Landan inda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake jinya yace 'ziyararsa zuwa gidan don ya bayyana rashin jin dadinsa na munafurcin mulkin Gwamnatin Buhari ne.'

Naij.com a satin nan ta kawo muku labarin Omokri da ya ziyarci gidan da hotunan da ya dauka.


A bidiyon da Reno ya saki yace 'Mulkin Gwamnatin Buhari yafi kowane mulki a tarihin Najeriya munafurci ya kuma fadi dalilan da ya sa ya fadi hakan.'
Dalilin ziyara ta gidan Buhari da ke

Landan - Reno Omokri
'Ya kamata ku san cewa 'Abuja House' ba gidan Shugaba Muhammadu Buhari bane. Ni dan Najeriya ne kuma ina biyan kudin haraji, Gwamnatin zata iya dubawa ta tabbatar da kudinmu ne yake tafiyar da 'Abuja House' din, don haka ina da damar zuwa god an.'

'' ya sake fadi.

'Gwamnatin Buhari tana takamar yaki da cin hanci da rashawa. Buhari ya dauka satar kudin Gwamnati ne kadai cin hanci da rashawa, rashin cika alkawarin da Shugabanni suka dauka lokacin zabe ma cin hanci da rashawa ne.'


'Gwamnatinsa ta jibge Jirgin Gwamnati a filin jirgin Landan yana jan kudinnmu a kullum. Saboda mutum daya Jirgin ya kwashe sama da kwana 80 a ajiye. Akwai ma’aikata da yawa da ba a biya su albashi ba, kudin zaman da jirgin yake ci zai iya biyan ma’aikata 2,000 albashi.'

'Najeriya tana daya daga cikin Kasashen da kananan yara basa zuwa makaranta a duk duniya sama da yara miliyan 12 musamman daga Arewacin Kasar. Yawan yaran da basa zuwa makaranta ya ninka yawan mutanen da ke Togo sau biyu.'

'Gwamnatin Buhari bata gina makaranta ko daya ba, amma Gwamnatin Jonathan ta gina makarantun almajirai a Arewa duk da Jonathan ba daga Arewa yake ba. Kudin da jirgin yake ci zai isa a gina makaranta, ko Gwamnatin zata iya sa a dawo da jirgin Najeriya.'
Share:

Masu hikima sunce ?? (fitowa ta 30) dr.mansur ibrahim sokoto

MASU HIKIMA SUN CE

Fitowa ta 30

136. Idan ka zama mai girman kai mutane za su watse su bar ka

137. Idan Allah ya taimake ka ba mai kayar da kai. In ko ya kayar da kai to, ba mai tayar da kai.

138. Aikin da mutum ya yi da shi za'a yi masa sakayya. Iyakar manzoya fadi sako, a karba ko bada a karba.

139. Kada ka hana hannunka mika alheri, kada kuma ka yi ta mikawa har ka zama ba ka da ahin da za ka mika.

140. A duniya kowa ka gani yan aiki, to yana yi ne iya fahimtarsa. Duk wanda kake ganin sa a karkace shi a wurin sa daidai yake.


Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi

Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

5/11/1438
29/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

Duniya makaranta !! ( fitotwa ta 30) dr.mansur ibahim sokoto

DUNIYA MAKARANTA

Fitowa ta 30

151. Wanda fuskar mata take ba shi sha'awa mata daya ba ta isar sa. Amma wanda kyakkyawan hali yake so daya ma sai ishe shi.

152. Idan kana cikin damuwa ka jira samun sauki daga wurin Allah, wannan jiran da kake yi ibada ne. Domin kyautata zato ne ga Allah. Wanda ya kyautata ma Allah zato kuwa lallai ne Allah zai ishe shi.

153. Duk lokacin da fitila ta yi sama haskenta ya fi yaduwa. Idan Allah ya daukaka ka, yi kokari ka zamo fitila mai kawar da duhu da damuwa daga mutane.

154. Urwatu bn Zubair, ya gamu da jarrabawar ciwon Cancer a kafarsa. Da magani ya gagara sai aka yanke shawara akan cire masa kafar ga baki daya. Amma a wannan dare bai fasa karanta abin da ya saba yi na Alkur'ani da Zikiran Ubangiji ba. Duhu gani, sau nawa ne karamar matsala ta durkushe ka daga ibada?

155. Kyawon hankali ya rika tunani. Kyawon harshe ya rika faadin gaskiya. Kyawon budurwa kunya. Kyawon Yaro biyayya.

Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

5/11/1438
29/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

Saturday 29 July 2017

Abu daya da zai sa Shugaba Buhari ya ajiye mulki - Dele Momodu

- Dele Momodu yace kadddara ce kurum za ta sa Buhari yayi murabus

- Marubucin yace kujerar Shugaban kasar Najeriya ba ta wasa bace

- Momodu yace a Najeriya ba a saba ganin Shugaba ya ajiye mulki ba

Fitaccen Marubucin nan Dele Momodu yace kadddara ce kurum za ta sa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi murabus. Momodu yace a Najeriya ba a saba ganin Shugaba ya ajiye mulki ba


Shugaba Buhari bayan ya dawo gida kwanaki
Dele Momodu yace mu daina yaudarar kan mu amma a Najeriya ba mu saba jin Shugaba ya bar kujerar sa ba. Haka kuma yace bugu da kari kujerar Shugaba kasar Najeriya tana cikin manyan kujerun Duniya don haka ba abu ne mai sauki ajiye mulkin ba.

Shugaba Buhari tare da Dele Momodu a fadar Villa

Har wa yau Dele ya yabawa irin kokarin Shugaban kasar da ya kyale Mataimakin sa ya rika aiki a matsayin Mukaddashin sa duk zarar da ba ya kasar. Momodu yace a Duniya ma an yi Shugabannin da su kayi mulki daga kan gadajen su a dalilin rashin lafiya.

Kwanan nan dai Femi Adesina yace Likitocin Shugaba kasar ne kurum za su iya bayyana lokacin da zai dawo kasar.
Share:

YA DAMKE SHAITAN (L. A) Zauren fiqhu

YA DAMKE SHAITAN (L. A)
***************************
Sayyiduna Abud Darda'i (ra) yace : "Manzon Allah (saww) ya mike yana sallah sai muka ji shi yana cewa:
"A'udhu bil Lahi minka" (Ina neman tsarin Allah daga sharrinka). Sai da ya fa'da sau uku. Sannan yace "INA TSINE MAKA DA CIKAKKIYAR TSINUWAR ALLAH". Ya fa'da har sau uku. Kuma ya bude hannunsa kamar yana kokarin damke wani abu.
Yayin da ya idar da sallar sai muka ce "Ya Ma'aikin Allah, hakika munji kana fa'din wani abu acikin sallah, wanda bamu ta'ba jin ka fa'di irinsa kafinsa ba. Kuma mun ga ka bude hannunka".
Sai Manzon Allah (saww) yace: "HAKIKA IBLEES MAKIYIN ALLAH, YAZO DA GARWASHIN WUTA ZAI SANYASHI A FUSKATA, SAI NACE MASA "INA NEMAN TSARIN ALLAH DAGA GAREKA" HAR SAU UKU, SANNAN NACE "INA TSINE MAKA DA TSINUWAR ALLAH CIKAKKIYA".
AMMA DUK DA HAKA BAI JA DA BAYA BA. HAR SAU UKU. SANNAN SAI NAYI NUFIN IN DAMKESHI.
WALLAHI BA DON ADDU'AR 'DAN UWANMU (ANNABI) SULAIMAN (AS) BA, DA SAI SHI (IBLEES DIN) YA WAYI GARI A DAURE, YARAN MUTANEN MADEENA SUNA WASA DASHI".
Imamu Muslim ne ya fitar da hadisin acikin Kitabul Masajid, Juzu'i na 1 shafi na 385.
DARASI
********
Darussan dake cikin wannan Mu'ujizar sun hada da :
1. Taurin kai da rashin mutunci irin na Iblees. Ku dubi yadda Manzon Allah (saww) ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa amma bai ja da baya ba.. Sannan ya tsine masa har sau uku amma bai ja da baya ba.
Wannan yana nuna mana cewar lallai Iblees (L. A) ba Qaramin shu'umi bane. Ya Allah ka kiyayemu daga sharrinsa.
2. Halaccin neman tsari daga sharrin shaitan yayin da kake cikin sallah, idan wani waswasi mai Qarfi ya bijiro maka. (musamman ga wadanda suke fama da matsalar shafar aljanu).
3. Fifikon Annabi Muhammadu (saww) a saman dukkan Annabawa (as). Domin babu wani Annabin da ya ta'ba damkar Iblees da hannunsa in ba Annabi Muhammadu ba (saww).
Ko shi Annabi Sulaiman (as) Allah ya hore masa shaitanun suna yin hidima agareshi. Amma bai ta'ba damkar shaitan da hannunsa ba.
4. Tawadhu'u irin na Annabi Muhammadu (saww) ku dubi yadda ya hakura ya saki shaitan din saboda tunawa da addu'ar wani 'dan uwansa daga cikin Annabawan Allah (as).
Ya Allah ka ninninka salati da girmamawa da aminci bisa Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa gwargwadon adadin kalmominka da dawwamar mulkinka Ya Rahman.
DAGA ZAUREN FIQHU
Share:

Ba na wani barcin kirki Inji Hamshakin Attajiri Dangote

- Aliko Dangote ya bayyana yadda ya samu arzikin sa

- Attajirin yace ya zage ne ba dare ba rana da nema

- Dangote yace a rana bai fi ya runtsa na dan lokaci kadan ba

Mai kudin Najeriya sa Afrika Aliko Dangote ya bayyana yadda ya samu arzikin sa a Duniya. Attajirin yace ya zage ne ba dare ba rana wajen nema.


Ka ji yadda Aliko Dangote ya samu duniya
Aliko Dangote yace a kowace rana ya kan yi aiki har na sa'a 18. Tun karfe 8:30 na safe Dangote yake shiga Ofis kuma ba zai fito ba sai bayan awa 18. Wannan dai ya bi jikin sa don kuwa bai fi yayi barci awa uku tak a raba ba.

Hamshakin Attajirin Afrika Dangote

Dangote yace ya kan tashi tun karfe 5:00 na asuba bayan yayi sallah sai ya shiga atisaye inda yake motsa jiki da tafiya ta kilomita 10. Mike Adenuga ya taba ba Dangote shawara yanzu ya kamata fa ya rika runtsawa don shekaru sun zo.

Duk Afrika dai babu wanda ya kama hanyar arzikin Dangote wanda ya mallaki sama da Dala Biliyan 16. Dangote na da ma'aikata sama da 26,000 a harkar noma, abinci, mai, kayan gini dsr.
Share:

Friday 28 July 2017

Mata 'yan majalisar wakilai sun dakatar da zaben canza kundin tsarin mulki

-Canaza kudin tsarin zai ba mata zabi zama yan garin da suke so

-Na'uran yin zaben ya samu matsala

-Matan sunyi zan-zanga dan nuna amincewan su da sakamakon zaben

Mata yan majalisa wakilai sun dakatar da zaben canza kundin tsarin mulki na 1999

'Yan majalisar sun nuna rashin amincewa sakamakon zaben da akayi akan zama "dan kasa da kuma dan jiha " ga mata


Mata 'yan majalisar wakilan sun dakatar da zaben gyara kundin tsarin mulkin
Kudirin zai canza sashe 25 na kundin tsarin mulkin kasar da zai ba matan aure zabin zama yan garin da suke so ta hanyar haihuwa ko ta hanyar aure da manufar samun mukami ko yin zabe.
Share:

Reps ta toshe wa majalisar dattijai haryar da zata hana Shugaban Nijeriya iko

Majalisar Wakilai a ranar Alhamis ta zabe wata magana da zai raunana iko na shugaban kasar a kan aiwatar da canji na kundin tsarin mulki, da kafa harsashin ginin al'umma ta shari'a da tsarin.

Duka benayen, majalisar dattijai da wakilai, sun kammala kada kuri'a a kan canji na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ta hanyar "takardar kudi don cigaba da canza kayan abinci na kundin tsarin mulki na tarayyar Nijeriya (canji ta hudu), 1999."

Duka gida biyun sun amince da kyautatuwa 33 sassan na kundin tsarin mulki dangane da rahotannin da ad-gadi kwamitoci a kan bayanin tsarin mulki tare da majalisar dattijai sun amince da 29, House kuma suka amince da 24.


Duk da yake benen gidan ya fara da kuma kammala da kyautatuwa a ranar Laraba, ƙananan majalisar dattawan sun kammala aikin a ranar Alhamis.


Reps ta toshe wa majalisar dattijai haryar da zata hana Shugaban Nijeriya iko
Dukansu bẽnãye na da iko a karkashin sashe na 9 na gyara aikin daftarin kundin tsarin mulki.

Duk da yake majalisar dattijai na bukatar kuri'u72 , wakiltar kashi biyu cikin uku, ya amince da kyautatuwa da wani sashe na daftarin aiki, kuri'u 240 da ake bukata na manufar majalisar.

Ya furta cewa, "majalisar dokokin na iya amfani da dokar gyara kundin tsarin mulki a lokacin da tayi shawara na gyara tsarin mulki da goyan bayan kashi biyu daga uku yawancin duk membobin kowane jam'iyya da kuma aka amince da ƙuduri na akalla 24 na majalisar jihohin."
Share:

Boko Haram sun dawo Sambisa, an sanya masu bam sau 108 – Sojin sama

- Rundunar sojin sama ta ce ýan taáddan Boko Haram sun dawo dajin sambisa dake jihar Borno bayan jirgin yakin ta ya tayar da maboyar ýar taáddan sau 108

- Rundunar sojin saman ta bayyana cewa tsakanin shekarar nan ta 2017 ayyukan ýan taáddan ya fara komawa dajin Sambisa

- An kaddamar da cewa akwai burbushin ayyukan Boko Haram a yankin Sambisa baki daya, musamman a Parisu

A ranar Alhamis, 27 ga watan Yulin, rundunar sojin sama da bayyana cewa ýan taáddan Boko Haram sun dawo dajin sambisa dake jihar Borno.


Rundunar sojin saman ta bayyana cewa ýan taáddan Boko Haram sun dawo dajin sambisa dake jihar Borno bayan jirgn yakin ta ya tayar da maboyar ýar taáddan sau 108 tsakanin watan Afrilu da kuma watan Yulin 2017.

NAIJ.com ta tattaro cewa Kwamandan sojin sama na Operation Lafiya Dole, dake yaki a arewa maso gabas, Air Commodore Tajudeen Yusuf, ne ya bayyana hakan a Yola, babban boirnin jihar Adamawa.
Share:

Buhari ya matsu ya dawo gida – Gwamna Ortom ya yi Magana bayan ziyarar Landan

- Gwamnan jihar Benue ya bayyana cewa shugaba Buhari na Allah Allah ya dawo Najeriya

- Samuel Ortom yabce shugaban kasar ya tambaye game da tsaro a jihar Benue

-Ya kuma bayyana cewa shugaban kasar zai dawo da zaran ya gama maganinsa a Landan

A ranar Alhamis, 28 ga watan Yuli, Gwamnan jihar Benue Samuel ya bayyana cewa shugaba Buhari na Allah Allah ya dawo Najeriya.

Ortom yace Buhari na Allah Allah ya dawo da zaran ya kammala maganinsa a Landan.

Ya kara da cewa shugaban kasar ya ji sauki sosai wanda yace alama ce ta cewa Allah na amsar adduóín miliyoyin ýan Najeriya kan halin da Buhari ke ciki.

Ya kuma ce Buhari ya yi barkwanci da gwamnonin da suka kai masa ziyara.

Ortom ya kuma bayyana cewa shugaban kasar ya nuna kulawa kan halin da tsaro ke ciki a jihar Benue da kuma yadda shi gwamnan ke magance su.
Share:

Menene tafkin al -kauthara ?? Zauren fiqhu

MENENE TAFKIN AL-KAUTHARA ?
**********************************
"ALKAUTHAR, WANI KOGI NE ACIKIN GIDAN ALJANNAH. GEFENSA BIYU NA ZINARE NE, KUMA YANA GUDANA NE AKAN DURRU DA YAQUTU (PEARLS AND DIAMONDS).

"QASAR CIKINSA TAFI ALMISKI QAMSHI, RUWAN CIKINSA YAFI ZUMA ZAQI, KUMA YAFI QANQARA HASKEN FARI".

Ibnu Maajah da Tirmidhiy ne suka ruwaitoshi ta hanyar Abdullahi bn Umar (ra) daga Manzon Allah (saww).

Ya Allah ka azurtamu da samun shan wannan ruwa, Ka shigar damu aljannarka Firdausi don rahamarka Ya Allahu Ya Rahman.

Salati da aminci su tabbata bisa Shugaban Talikai, Ma'abocin Tafkin nan na Alkauthara, Mai Mafificin Matsayi aranar Mahshar.. Annabi Muhammadu (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam).

DAGA ZAUREN FIQHU (03-11-1438  27-07-2017).

MASU KWAFAR RUBUCE-RUBUCEN ZAUREN FIQHU SUNA CHANZAWA, KUJI TSORON ALLAH KU DENA CIN AMANAR ILIMI DOMIN ALLAH ZAI TAMBAYEKU.
Share:

NECO Result 2017| Check NECO Result Here Online


NECO Result 2017| Check NECO Result Here Online
NECO Result 2017|Check NECO June/July Result HereOnline.
NECO Resu lt 2017


ination (SSCE) and the GeneralCertificate in Education (GCE) in June/July and December/January respectively
Beforeyouproceed to check your2017 NECO GCE result online,youhave to purchase NECO result checkingscratch card.
N/B: Cards are available in all NECO offices.
How to Check 2017 NECO GCE Result Here.
1. Go to NECO result checkingportal
CLICK HERE TO CHECK
2. Select yourexamination type i.e. Nov/Dec
3. Select youryear of examination i.e. 2017
4. Enter the result checkingscratch card PIN numberin the required column
5. Enter yourexamination number
6. Finally, click on Check My Result button to access your2017 NECO GCE result.
Share yourresults with others usingthe comments section.
Good Luck.
Searches Related to NECO Result on google.com
Whenwillthe 2017/18 NECO Resultbe released
Whenwillthe 2017WAEC Resultbe released
Whenwillthe 2017WAEC Resultbe released
WithheldNECO Resultreleased
Checknecoresult with NECO scratch card
Checknecoresult without scratch card
NECO result 2011/2012/2013/2014/2015/2016/201
necoresult newsupdates
necoresult nov/dec 2017/2018 updates
PrintOut NECO result 2017/18
www.necoresult2017.com

Share:

Thursday 27 July 2017

Nigerian EFCC ta kwato 'naira biliyan 329 daga kamfanonin mai'

Hukumar yaki da cin hanci da rshawa ta Najeriya EFCC, ta ce ta kwato kimanin naira biliyan 329 ($1.4 biliyan) da wasu kamfanonin mai suka karkatar tare da hadin gwiwar kamfanin mai na kasa na NNPC.
Wata sanarwar da ta fitar ta kara da cewar an kwato kudaden ne tsakanin Yulin 2016 zuwa watan Yulin 2017 bayan wani korafi da ta samu kan zargin aikata ba daidai ba.
Hukumar ta ce bincike ya nuna cewar kamfanonin sun karbi mai da yawa daga gwamanti ba tare da biyan kudi yadda ya kamata ba.
Sanarwar ta ambato mai magana da yawun hukumar, Wilson Owujaren, yana cewar kamfanonin man sun hada da NNPC da Conoil Plc da Total Plc da OVH Energy da Oando Plc da Forte Oil and Gas da MRS Oil Plc da kuma NIPCO Oil Plc.
Kawo yanzu babu daya daga cikin kamfanin da ya ca uffan game da sanarwar ta EFCC.
An dade ana zargin cewar ana tafka almundahana a harkar man Najeriya inda kasar ta fi samun kudaden shiga.
Kotu ta ba da umarnin kwace kadarorin Diezani
Wani jami'in EFCC ya kubuta a hannun 'yan bindiga
Kakakin EFCC din ya ce takardar koken da aka tura wa hukumar EFCC ta yi zargin cewar kamfanonin da ke sayar da man sun yi sama da fadi da naira biliyan 40 tare da shugabannin NNPC.
Daga nan ne aka mika batun ga wata runduna ta musamman wadda ta gudanar da bincike a cikin sirri, in ji Mista Owujaren.
Ya kara da cewa bayanan da jami'anmu suka samu sun nuna cewar gwamnatin tarayya na bin kamfanonin man bashin naira biliyan 91.5 tsakanin 2010 zuwa 2016.
"Da aka zurfafa bincike kan zargin, sai aka gano cewar kamfanonin na ci gaba da karbar mai daga gwamnati ba tare da biyan kudi kamar yadda dokokin bashi na NNPC/PPMC suka tanada ba.
Karin bincike kan wannan ya sa an ganon naira biliyan 258.9,'' in ji kakakin na EFCC.
Mista Uwujaren ya yi bayanin cewa jumullar bashin ta tsaya ne kan naira biliyan 349.8.
Wannan ne ya sa kawo yanzu bashin da ya yi saura ya kasance naira biliyan 20.7.
Wadannan kamfanoni na yin huldar kasuwanci dadab daban na kamfanin NNPC, ciki har da yi masa dillancin danyan mai da kuma batun shigo da tataccen man fetur kasar.
Share:

NIMC National ID Card is Out, Check If Your ID is Ready, Sept 2011 – May 2017 Enrollment

           




The National Identification Management Commission (NIMC), has recently released the National ID Card of September 2011 – May 2017, you can check if your ID is ready online by following the simple steps below:
1. Follow the apply link below,
Click here to check
2. Click the proceed button
3. Fill in your First Name, Last Name and the Last 6-digits of your National Identification Number (NIN)
4. :Click the ‘ application button below’.

Also as explained by the NIMC’s Director of Technical Services, the new e-ID card can also serve as a cash card. So the card holder can withdraw money in any place. Moreover, especially within the West African sub-region, it soon would become possible to travel with this card only, passport-free.

New: The e-Identification (eID) Card can also be used as an Automated Teller Machine (ATM) Card in any Automated Teller Machine (ATM) around the world.
Update your profile to qualify for the new e-ID Card Automatic Teller Machine Service.

Share:

(mp3) Duk inda ahlus-sunnah suke aqidar su daya ne.- Sheikh kabiru haruna gombe

*MUHADARA MUHADARA*

MAI TAKEN: *DUK INDA AHLUS SUNNAH SUKE AQIDAR SU DAYA NE*

Tare da: *Sheikh Kabiru Haruna Gombe*

2/11/1438
26/7/2017​

Domin sauko da wannan audio saiku danna wannan blue rubutu dake kasa 👇👇👇

DOWNLOAD AUDIO NOW

Ayi saurare lafiya

ZAKU IYAYIN SHARE ZUWA SOCIAL MEDIA DINKU DOMIN YAN'UWA SUKARU A NAN 👇👇👇
Share:

Kalli Hotunaan shugaba buhari da gwannoni dasuka kaimasa ziyara a kasar london

                                       
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da karin wasu gwamnonin kasar da suka masa ziyara a London inda ya ke jinya.
Cikin gwamnonin bakwai da suka kai wa Shugaba Buharin ziyara har da gwamnonin PDP.
Gwamnonin da suka ziyarci shugaban na Najeriya sun hada da Abdulaziz Yari na jihar Zamfara, da Dave Umahi na jihar Ebonyi, da Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, da Kashim Shatima na jihar Borno, da Samuel Ortom na jihar Benue, da kuma Abiola Ajumobi na jihar Oyo.
Shugaba Buhari yana cikin nishadi a wannan hoton.
Baya ga gwamnonin, shugaba Buhari ya kuma gana da matarsa Aisha.


                Hotunan shugaba buhari da gwannoni dasuka kaimai ziyara a kasar london




Share:

Jagoran mahajjaci (01)

JAGORAN MAHAJJACI (01)

Fassarar: Dr Abubakar Sani Birnin Kudu

Ministry of Islamic affairs na Saudi Arabia suka buga

KA'ABAH ALQIBLAR MUSULMAI

Ka’abah Mai Daraja ita ce 'Dakin Allah ‘yantacce
Zukatan Musulmi duk inda suke a banngarorin duniya gareshi suke karkata.

 Goshi da zukatan bayin Allah masu khushu’i da qasqantar da kai ga Allah sau biyar a yini da dare, duk wannan 'Daki suke fuskanta.

Musulmi na kwararowa tawaga-tawaga zuwa 'Daki ‘yantacce daga kowace hanya da wuri mai nisa, tun daga zamanin da Annabi Ibrahim ya ginashi,don yin aikin hajinsu, kuma domin suyi 'Dawafi a wannan 'Daki mai daraja.

Wannan don ya qara tabbatar da cewa wannan 'Daki shine:Daki na farko da aka sanyawa mutane domin su bautawa Allah a cikinsa bisa ilimi da basira, da aqida tsabtatacciya, wadda bata gurbata da miyagun aqidu da
ra’ayoyin da suka saki hanya ba.

Allah Ta’ala yana cewa:
{Kuma lallai 'Daki na farko da aka aza domin mutane, shi ne wanda ke Bakka mai albarka kuma shiriya ga talikai. A cikinsa akwai ayoyi bayy￾anannu (misali) matsayin Ibrahima. Kuma wanda ya shige shi ya kasance amintacce. Kuma aikin hajin 'Dakin wajibi ne domin Allah a kan mutane,
ga wanda ya samu iko zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirta to lallai Al￾lah Mawadaci ne daga barin talikai} Suratu aal Imran: 96-97.

Daga Ibrahim Nasidi Abu-Ilham 25/07/2017
Share:

Masu hikima sunce ?? (fitowa ta 29) Dr.mansur ibrahim sokoto

MASU HIKIMA SUN CE

Fitowa ta 29

131. Kada ka halaka dukiyarka kayi ta turawa magabta don ka samu, ta haka ka ci dukiyar wadansu.

132. Da yardar Allah, ka kan ga runduna kadan sun kori runduna masu yawa.

133. Ka sallami mutum da kyakkyawar magana ya fi ka ba shi sannan ka yi masa gori.

134. Allah ba ya dora maka abin da ba ka iyawa.

135. Ba za ka samu abin da kake so ga Allah ba, sai kayi alheri da abin da ka fi so.


Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi

Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

3/11/1438
27/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

Duniya makaranta !! (fitowa ta 29) dr.mansur ibrahim sokoto

DUNIYA MAKARANTA

Fitowa ta 29

141. Idan kana son ganin yadda duniya za ta kasance a bayanka, ka duba yadda take a bayan mutuwar wani irinka. Za ka ga yadda masoya ke manta masoyansu, rigima ta harde tsskanin magadansu wanda bai manta ka kawai shi ne Allah mahaliccinka. Manta da kowa ka nemi yardarsa.

142. Wand ba sallah an harmata ma sa jin dadin duniya, kuma zai gamu da wahalhalu a wurare guda hudu: A nan duniya, da ranar mutuwa, da cikin kabari da ranar hisabi.

143. A nan duniya ana debe ma sa albarka, a cire ma sa kwarjini daga fuska, a sa ma jama'a kyamar sa.

144. A ranar mutuwa zai mutu da wulakanci da yunwa da kishirwa.

145. A cikin kabari Allah zai kuntata ma sa, a hasa ma sa wuta a cikin sa, a aika ma sa kurmarci a tsakanin fatar jikinsa da namansa.

146. A ranar hisabi za a bakanta fuskarsa, a yi masa hisabi dalla dalla, sannan a hada shi da Zabaniyawa da za su wurga shi cikin wuta.

a. Ya kai dan uwa mai sallah ka gode ma Allah q kan ni'imar da kake cikin ta da wadda za ka shiga a cikin a bayan mutuwarka.

Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

3/11/1438
27/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

Masu hikima sunce ?? (fitowa ta 28) dr.mansur ibrahim sokoto

MASU HIKIMA SUN CE

Fitowa ta 28

126. Idan ba ka son ka yi wa mutane aikin kirki, to, kayi musu yadda suka yi maka.

127. Idan makwaucinka ya ki ka, to, ka juyar da kofar gidanka. Sai ka huta, ya huta.

128. Amfanin hasken fitila na wadansu ne, ba nata ita kanta ba.

129. Kada karbar da mutane suke yi ma shawararka ya hana ka karbar tasu idan sun fada maka. Kada ka umurci mutane da alheri sannan ka kaurace masa.

130. Sau da yawa kakkan ki wani abu, amma ya same ka. Samuwarsa kuwa ta zama alheri ce gare ka. Sau da yawa kakan so samuwar wani abu, amma ka rasa shi. Kuma rashin nasa ya zama shi ne alheri gare ka.

Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi

Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

2/11/1438
26/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

Duniya makaranta (fitowa ta 28) dr.mansur ibrahim sokoto

DUNIYA MAKARANTA

Fitowa ta 28

136. Karatu akwai wuya, ilimi akwai dadi. Nema akwai wuya, arziki akwai dadi. Zama da jahilci ba wuya, rashin ilimi akwai takaici. Haka duniya take, yaro bata hankalin dare ka yi suna!

137. Allah ya ya mana kunnuwa biyu da idanu biyu amma ya yi mana baki guda daya saboda ya fi son mu yi kallo, mu yi saurare fiye da yadda mu ke magana

138. Idan na kwarai da mugu suka hadu kowa ma yana iya gane banbamci. Amma a tsakanin na kwarai da wanda ya fi shi, da mugu da wanda ya fi, wannan sai masu hankali ke iya rarrabewa.

139. Ba a sanin matsayin saurayi sai ya yi aure. Ba a sanin halin talaka sai ya wadata. Ba a sanin gaskiyar dan Siyasa sai ya kai ga mukami.

140. Ba kowane wayayye ne mai ilimi ba. Ba kuma kowane mai ilimi ne yake da wayewa ba. Idan Allah ya ba ka ilimi nemi sanin duniya da zamanin da kake cikin sa, sai ya zama kana daa haske a kan haske. Idan kuma kana da wayewa da sanin duniya matsa kusa da malamai ka kara sani, sannan ne wayewarka za ta amfane ka.

Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

2/11/1438
26/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

Masu hikima sunce ?? (fitowa ta 27)

MASU HIKIMA SUN CE

Fitowa ta 27

121. Kar ka tambayi mutum halinsa. Ai da ganin fuskarsa ka san halinsa.

122. Mai hankali ba shi zama cikin kasar da a ke wulakanta shi.

123. Kakan rabu da wadanda ba ka son rabuwa da su, kamar yadda kakan zauna d wadanda ba ka son zama da su.

124. Wanda bai fara yi maka alheri ba, kada ka kokarta ka fara yi masa godiya.

125. Da hankalinka ko mutucinka ya cutu, gara jikinka ya cutu.

Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi

Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

1/11/1438
25/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

Duniya makaranta. (fitowa ta 27)

DUNIYA MAKARANTA

Fitowa ta 27

131. Zunubin da ya sa ka yin da-na-sani da komawa ga Allah ya fi ibadar da ta sa ka girman kai da dagawa!

132. Sarakunan da suka yi mulkin duniya duk sun tafi ba su san dadin duniya ba. Ba wutar lantarki, ba ruwan Firijin, balle kuma Fanka da AC. Ba su hau keke ko Mashin ba, ballantana motoci da jirge. Ba su san abin ake kira Tarho ba ballantana wayar tafi-da-gidanka. Duk hasken gidajensu a wancan lokaci bai wuce na Kyandurda Fitila mai amfani da kalanzir ba. A yau kai Sarki ne amma ba ka gamsu da abin da ka samu ba. Idan kana da mota ta makwaucinka kake kallo. Idan kana da gida na wani ka ba ka sha'awa. Oh! Allah Sarki. Dan adam da guri yake mutuwa.

133. Idan ka kas gane wurin da ka yi shuka kada ka samu damuwa. Watarana ruwan sama ne zai nuna ma ka. Haka rayuwa take. Yau da gobe babbar makaranta.

134. Hattara da hawaye guda uku:
a. Hawayen iyaye da
b. Hawayen maraya da
c. Hawayen wanda ka zalunta.
Kowanen su hawayensa na iya nutsar da kai a cikin tekun bala'i.

135. Mala'iku suna da hankali ba su da sha'awa. Dabbobi suna da sha'awa ba su da da hankali. Dan adam ne Allah ya hada ma sa guda biyun. Idan hankalinka ya rinjayi sha'awarka ka bi sawun Mala'iku. Idan sha'awarka ta zarce hankalinka ka shiga sahun dabbobi.

Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

1/11/1438
25/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

(mp3) Karatu da aiki dashi shine mafita a gareku, idan ba aiki ba dashi matsala ne a gareku duniya da lahira

*MUHADARA MUHADARA.*          
 
              *TA IYAYE MATA.*
       
Mai Taken 👇

*KARATU DA AIKI DASHI SHINE MAFITA A GAREKU, IDAN BA AIKI DASHI MATSALA NE A GAREKU DUNIA DA LAHIRA.*


Tare da :- *Sheikh Musa Yusuf Asadus-sunnah (Hafizahullah).*


*Daga Masallacin Ahlul baiti Wassahaba Kaduna.*

Ranar Lahadi
29/10/1438
23/07/2017

Domin sauko da wannan audio saiku danna wannan blue rubutu dake kasa👇👇👇

DOWNLOAD AUDIO NOW

Ayi saurare lafiya

ZAKU IYAYIN SHARE ZUWA SOCIAL MEDIA DINKU DOMIN YAN'UWA SUKARU A NAN 👇👇👇
Share:

(mp3) Karatun littafin Al-aqidatu dahawiyyah - Sheikh musa yusuf asadussunnah

*Karatun Littafin.*


*AL-AQIDATU DAHAWIYYAH.*


Darasi na (23).


Tare da :- *Sheikh Musa Yusuf Asadus Sunnah (Hafizahullah).*

*Daga Masallacin Malam Khamis Al-misirry Dake bye pass Kaduna.*


Ranar Litinin
30/10/1438
24/07/2017

Domin sauko da wannan audio saiku danna wannan blue rubutu dake kasa 👇👇👇

DOWNLOAD AUDIO NOW

ZAKU IYAYIN SHARE ZUWA SOCIAL MEDIA DINKU DOMIN YAN'UWA SUKARU
Share:

Tuesday 25 July 2017

Amfanin zakka da sadaka a rayuwar bawa musulmi.

*AMFANIN ZAKKA DA SADAKA A RAYUWAR BAWA MUSULMI*

✍🏼Rubutawa: *_Dr Aliyu Muhammad Sani, Hafizahullah_*

Daga cikin amfani da fa'idojin Zakka, tana tsarkake mai bayar da ita, kuma tana kara masa imani, kuma tana tsarkake dukiyar tasa, kuma tana karata ta bunkasata, kuma tana amfanar da wanda aka ba shi ita.

1. Amma tsarkakewa da take yi wa shi mai bayar da ita, lallai tana tsarkake halayensa, tana tsarkake shi daga kwadayi da rowa, da munanan halaye da da biyu. Kuma tana bunkasa halayensa, sai ya siffantu da siffofin masu karamci da kyauta da yin alheri wa mutane, kuma masu godiya ma Allah a kan abin da ya yi musu na arziki da ni'imomi, saboda ba da Zakka yana daga cikin manyan aiyukan godiya ma Allah, ita kuwa godiya ma Allah a kullum tana tare da samun kari daga wajensa.

Kuma Zakkar tana bunkasa ladansa da sakamakonsa a wajen Allah, saboda Zakka da ciyar da dukiya ana ninka ladansu ninki masu yawa, gorgodon imanin wanda ya bayar da ita da Ikhlasinsa, da kuma amfaninta da ajiyeta a muhallinta (nau'in mutane takwas (8) wadanda ake ba su Zakka).

Kuma Zakka tana fadada zuciya, ta faranta rai, kuma tana kare wa bawa bala'o'i da cutuka masu yawa.

Kuma Zakka da Sadaka suna kulla soyayya a tsakanin Musulmi, suna gusar da gaba da kiyayya a tsakaninsu, su mai da su, su zama 'yan uwa abokan juna, saboda dabi'a ce ta zukata son wanda ya kyautata mata, wannan zai sa a samu hadin kai a tsakanin musulmai su zama al'umma guda daya a kan Addinin Allah, masoya juna.

Kuma Zakka da kyauta suna sa wadanda aka ba su su yi addu'o'in da Allah yake amsawa ma wadanda suka bayar da ita.

2. Sannan kuma Zakka tana bunkasa dukiyar da aka fitar da ita daga gare ta, tana kare ta daga masifa da bala'i, kuma tana janyo mata albarka, kamar yadda Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, Ya ce:

*_"Sadaka ba ta tauye dukiya, a'a, tana karata ne"._*

Allah Ya ce:

{وَمَا أَنْفَقْتُمْ مِنْ شَيْءٍ فَهُوَ يُخْلِفُهُ وَهُوَ خَيْرُ الرَّازِقِينَ} [سبأ: 39]

*_"Duk wani abu da kuka ciyar, to Allah Zai maye muku gurbinsa, kuma shi ne fiyayyen masu arzurtawa"._*

 3. Amma amfanin Zakka ga wanda aka ba shi ita, lallai Allah Ya yi umurnin a bayar da ita ne ga mabukata, daga fakirai, da miskinai da wadanda ake bi bashi, da kuma bayar da ita don 'yanta bayi, da kuma bayar da ita don gudanar da maslahohin da musulmai suke bukatansu, don haka duk lokacin da aka ajiye Zakkar a muhallinta, aka bayar da ita ga wanda ya dace, to za a biya masu bukatunsu da yaye musu laruran da suke ciki, fakirai za su wadata ko talaucinsu zai ragu, kuma za a samu daman gudanar da aiyuka na maslahar al'umma gaba daya.

Inda a ce, mawadata da masu arziki za su fitar da Zakkan dukiyoyinsu ta fiskar da aka shar'anta, a bayar da ita ga wanda Allah Ya yi umurni, da an cimma maslahohin Addini da na duniya masu yawan gaske, da an kawar da talauci ko an rage shi, da an magance sharri masu yawa, na zaman banza da rashin aikin yi, da sace – sace da fashi da makami, da ha'inci da satar dukiyar al'umma, da an samu ci gaban tattalin arziki a cikin al'ummar musulmi.

Wannan ne fa ya sa Zakka ta zama daga cikin manyan abubuwan da suke nuna kyawun Shari'ar Muslunci, saboda abin da ta kunsa na janyo maslahohi da amfani wa mutane da kawar da barna da abin da zai cutar da su.

Daga littafin Sheikh Ibnu Sa'adiy, Rahimahullah: Al- Riyadhun Nadhirah.

Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
Share:

Hukuncin mace tayi tafiya batare da muharrami ba !! Mal.Umar shehu zaria

*HUKUNCIN MACE TA YI TAFIYA BA TARE DA MUHARRAMI BA*

Fatawar Mata fitowa ta 1

*TAMBAYA:*
Mene ne hukuncin mace ta yi tafiya ba tare da Muharrami ba?.

*AMSA:*
An hana mace ta yi tafiya face tare da Muharrami wanda zai tsare ta kuma ya kare ta daga barnan mabarnata da fasikancin fasikai.

Hakika hadisai ingantattu sun zo wanda suke hana mace ta yi tafiya ba tare da Muharrami ba, daga cikin su:

An rawaito daga Abdullahi Dan Umar, Radhiyallahu Anhu, ya ce: Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: *_Kada mace ta yi tafiya na kwanaki uku face tare da ita akwai Muharrami_*.

Sannan an karbo daga Ibn Sa'id, Radhiyallahu Anhu, Lallai Manzon Allah, Sallallahu' alaihi wa sallama, Ya hana mace ta yi tafiya yini biyu ko darare biyu face tare da mijinta ko Muharraminta.

Kuma an karbo daga Abi Hurairah, Radhiyallahu Anhu, daga Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: *_Ba Ya halatta ga mace ta yi tafiya na jini da dare face tare da ita akwai Muharraminta_* Bukhari da Muslim ne suka riwaito.

Amsawa: *_Sheikh Saleh al-Fauzan, Rahimahullah_*

A duba littafin فتاوى المرأة المسلمة shafi na 863.

✍🏼 Tattarawa: *_Umar Shehu Zaria_*

Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
Share:

Masu hikima sunce ?? (fitowa ta 26) dr.mansur ibrahim sokoto

MASU HIKIMA SUN CE

Fitowa ta 26

116. Zaman dan Adam a duniya kamar wata ne da haskensa. Idan hasken wata ya fara tun magariba har safe, to, hasken ya dinga raguwa kenan har mutuwarsa.

117. In dai jagabanka hankaka ne, to, kada ka yi kuka ina ya bi da kai hanyar mushe.

118. Wanda ya yi tsawon rai a duniya, zai ga abin da zai faranta masa rai, ya kuma ga abin da zai bakanta masa rai.

119. Komai dadin da ka ji a duniya, wadansu sun riga ka ji, sun kuma riga ka bari. Haka kai kuma za ka bar shi yadda suka bari.

120. Da ba ya jure ma wulakanci kamar yadda jaki da la'imi suke jure masa.


Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi

Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

30/10/1438
24/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

Duniya makaranta !! (fitowa ta 26) dr.mansur ibrahim sokoto

DUNIYA MAKARANTA

Fitowa ta 26

126. Tsare gaskiya ba ya hana rayuwa jin dadi. Karya da zulanci da zulunci da cin amana ba su kawo samu.

127. Abu biyu idan kana da su kai Sarki ne: Lafiya da wadatar zuci.

128. Duk abin da ya sa ka damuwa idan ka yi nazarin sa ya taba sa ka murna. A duniya babu abin murna na din-din-din sai dai a aljanna.

129. Karamin yaro da Fensir yake rubutu. Idan ya girma sai ya koma ga Biro. Dalilin haka shi ne, kuskuren yaro mai saukin gogewa ne. Goge kuskuren babba kam akwai wahala gare shi.

130. Mutane iri biyu ne: Wani yana rayuwa ne don ya ci, wani kuma yana ci ne don ya rayu. Koka gane bambanci tsakaninsu?

Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

30/10/1438
24/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

Duniya makaranta !! ( fitowa ta 25) dr.mansur ibrahim sokoto

DUNIYA MAKARANTA

Fitowa ta 25

121. Marar gaskiya kamar mai yagaggen wando ne, duk inda zai zauna sai ya rinka kame-kame. Mai gaskiya a natse yake zamansa.

122. An gane mimini ne a wurare guda uku: Idan ya samu ya gode ma Allah, idan ya rasa ya koka ma Allah, idan ya shiga damuwa ya koma ma Allah.

123. Abubuwa uku idan suka hadu da wasu uku ba su da magani: Talauci idan ya hafu da kasala. Kiyayya idan ta hadu da hassada. Jahilci idan ya hadu da girman kai. Allah ka sa mu gama da duniya lafiya.

124. Abubuwa uku ba su da tsada: Ilimi da Lafiya da Sadaki.

125. Idan kudi suka fara zance dole ne gaskiya ta rufe bakinta.

Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

29/10/1438
23/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

Masu hikima sunce ?? (fitowa ta 25) dr.mansur ibahim sokoto

MASU HIKIMA SUN CE

Fitowa ta 25

111. Sau da yawa kakan ga wanda ya tara duniya ba shi ne mai cin ta ba. Kamar yadda ka kan ga wani ya cinye duniyar da ba shi ya tara ba.

112. Har mulkin Annabi Sulaimanu ya faru ya kare dare da rana suna nan yadda suke. Ballai ma wani.

113. Duk masifar da ta samu dan Adam yana jin ciwon ta. Amma ya fi jin ciwon dariyar da abokan gaba suke yi masa.

114. Hakikanin mai jin dadi a duniya shi ne wanda tubatuban zamani ba su same shi ba.

115. Idan ka yi gudun wani abin da Allah ya kaddaro maka, ka yi gudun banza. Inda ka sa fuskarka duk shi ne zaka taras


Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi

Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

29/10/1438
23/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

Masu hikima sunce ?? ( fitowa ta 24) dr.mansur ibrahim sokoto

MASU HIKIMA SUN CE

Fitowa ta 24

106. Mai son duniya da lahira kamar mai mata biyu ne a duniya. Idan ya shirya da daya sai su bata da daya.

107. Iyakar dan Adam ya yi kokari bisa sha'anin duniyarsa, amma ba tilas ne duk sha'aninsa ya zo masa yadda yake so ba.

108. Ka girmama kanka don mutane su girmama ka. Idan kai ka wulakanta kanka faufu, babu mai girmama ka.

109. Idan zukatan masoya suka kusanci juna, nisan jiki ba ya raba su.

110. In dai kana da lura kwanakinka na duniya sa yi maka wa'azi, domin ba dayan su da zai wuce ka ba ka ga wani abin mamaki ba.


Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi

Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

28/10/1438
22/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

Duniya makaranta !! (fitowa ta 24) dr.mansur ibrahim sokoto

DUNIYA MAKARANTA

Fitowa ta 24

116. Makaho idan idonsa ya bude karya sandarsa yake yi. Wani ma kona ta zai yi da wuta. Haka dan Adam yake da saurin manta alheri da kin tuna baya. Duk wanda za ka taimake shi yi ma sa don Allah. Idan kana jiran godiya da sakayya daga mutane babu shakka za ka sha mamaki.

117. Wawa ne yake fadin abin da zai aikata. Mai kuri shi yake bayyana abin da ya aikata. Mai natsuwa aikinsa ne ke bayyana matsayinsa.

118. Gishiri da Sukari kalarsu daya ce. Banbancinsu yana bayyana ne idan aka dandana. Haka mutane su ke; sai an gwada akan san na kwarai.

119. Zama da mutanen kirki yana karar da kai ababe guda shida: Son Allah, da bin Allah, da ambaton Allah, da gudun duniya, da son lahira da barin giraman kai.

120. Har abada akwai zukatan da ke son ka ko da kana munana ma su. Akwai kuma ma su kin ka duk yadda ka kyautata ma su. Kowa da kiwon da ya karbe shi.

Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

28/10/1438
22/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

Monday 24 July 2017

(mp3) Complete Debate tsakanin sheikh musa yusuf asadusaunnah da sheikh yahaya ibrahim masussuka akan asaki hadisan manzon Allah ( S.A.W) akama al'qur'ani kadai !!!

Debate Debate

Akan hadith

Tsakanin

Sheikh musa yusuf asadussunnah

      Da

Sheikh yahaya ibrahim masussuka

Domin sauko da wannan audio saiku danna wannan blue rubutu dake kasa 👇👇👇

DOWNLOAD AUDIO NOW

AYI SAURARE LAFIYA

     Zaku iyayin share zuwa social media dinku domin yan'uwa sukaru a nan 👇👇👇
Share:

Sunday 23 July 2017

Masu hikima sunce ?? (fitowa 23)

MASU HIKIMA SUN CE

Fitowa ta 23

101. Ka gaggauta aikin kirki tun gabanin zuwan ajalinka.

102. Wanda ya kamata ka fi girmamawa a cikin mutane, shi ne wanda idan ya ga aibinka ko kuskurenka, tsoronka ko kwadayin aibinka ba za su hana shi bayyana maka ba, kuma ya bayyana maka a asirce, ba cikin mutane ba.

103. Kada ka yi bakin cikin wucewar al'amarin da, tun fil'azal ba za ka same shi ba.

104. Kada ka yi farin ciki da samun al'amrin da ba zai wuce ka ba.

105. Abin da ya kamata ka yi farin ciki da shi, shi ne yin daidai a cikin sha'anin duniyarka da na lahirarka. Rashin yin haka shi ne damuwarka. Ka san fa ba abin da zai amfane ka cikin dukiyarka kamar wanda ka gabatar don lahirarka ba wanda ka bar wa duniya ba.


Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi

Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

28/10/1438
22/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +234703747774
Share:

Duniya makaranta !! (fitowa ta 23) dr.mansur ibrahim sokoto

DUNIYA MAKARANTA

Fitowa ta 23

111. Alamun mai riya guda uku ne: A fili yana sallah, a boye yana wasa. Idan an gan shi an ga mumini, idan ya kebanta ya koma fasiki. Bakinsa ya fi zuciyarsa karfi. Allah ka kare mu daga sharrin riya.

112. Abu uku ba a wasa da su: Addininka, da kasarka, da mutucinka. Abu uku ba a fadar su: Arzikinka da Iliminka da yawan shekarunka.

113. Ba kowace magana ce ake ba da amsar ta ba. Ko shiru magana ce.

114. Sana'arka arzikinka. Annabbi Dawuda makeri ne. Annabi Zakariyya kafinta ne. Annabi Idris madaunki ne. Annabinmu makiyayi ne. Nemi na kanka. Zaman banza babbar cuta ce. Arziki kuma zomo ne. Zomo ba ya kumuwa da kwance!

115. Yi murmushi idan ka ga mai son ka, zai ji dadi. Yi murmushi idan ka ga mai kin ka, zai ji tsoro. Yi murmushi idan ka ga wanda ya bar ka, zai yi da-na-sani. Yi murmushi ga wanda ka sani da wanda ba ka sani ba. Murmushi kwararjini ne ga namiji, ado ne ga fuskar macce.

Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

28/10/1438
22/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

(mp3) Karatun littafin gulma da illolinta - Mal.umar shehu zaria

Karatun littafin gulma da kuma illolinta

Tare da
Malam umar shehu zaria

DOMIN SAUKO DA WADDANNAN AUDIO SAIKU DANNA WANNAN BLUE RUBUTU DAKE KASA 👇👇👇

004 gulma da illolinta

DOWNLOAD AUDIO NOW

005 gulma da illolinta

DOWNLOAD AUDIO NOW

006 gulma da illolinta

DOWNLOAD AUDIO NOW

007 gulma da illolinta

DOWNLOAD AUDIO NOW

008 gulma da illolinta

DOWNLOAD AUDIO NOW

009 gulma da illolinta

DOWNLOAD AUDIO NOW

010 gulma da illolinta

DOWNLOAD AUDIO NOW

011 gulma da illolinta

DOWNLOAD AUDIO NOW

012 gulma da illolinta

DOWNLOAD AUDIO NOW

013 gulma da illolinta

DOWNLOAD AUDIO NOW

AYI SAURARE LAFIYA

Zaku iyayin share zuwa social media dinku domin yan'uwa sukaru a nan 👇👇👇
Share:

Archive

Unordered List

Support