*SHIN YA HALLATA NA YIWA WANI DAWAFI?*
*TAMBAYA:*
Assalamu alaikum, Malam, yayata ta jidda ta ce in tambaye ka mene ne hukuncin yin dawafi ga wani, saboda mutane suna yawan bugowa suna cewa a musu dawafi, kuma ta ce in gaya ma wai don Allah ka amsa a face book, saboda ana bukatar sanin amsar.
*AMSA:*
To, 'Yar uwa, babu wani dalili ingantacce wanda yake inganta yiwa wani dawafi, sannan kuma ba a samu magabata na kwarai suna yi ba, ga shi kuma dawafi ibada ce, ita kuma ibada ba'a yin ta sai da dalili daga al-Qur' ani ko Sunna, amma dai ana iya yiwa wani addu'a lokacin da mutum yake yiwa kansa dawafi.
Akwai dalilai da yawa wadanda suke nuna ingancin yiwa wani Umara ko Hajji, sai dai ba a samu na dawafi a karan kansa ba.
Kiyasin dawafi akan Hajji da Umara ba zai yiwu ba, saboda dawafi tsantsar ibadar jiki ce, hajji da umara kuma ibadu ne da suka hada jiki da dukiya. Duk ibadar da ta hada jiki da dukiya, tana amsar wakilci, amma wacce ake yin ta da jiki kawai ba ta amsar wakilci kamar sallah.
Allah ne mafi sani.
Duba Fatawaa Nurun Aladdarb mai lamba ta: 87
✍🏼Amsawa:
*_Dr Jamilu Yusuf Zarewa_*
7\12\2014.

0 comments:
Post a Comment