*TARAYYAN MAZA DA MATA YAYIN SALLAN JANAZA*
Fatawowin Mata fitowa 3
*TAMBAYA:*
Shin ya halatta Mace ta yi tarayya da Maza yayin sallan Janaza?
*AMSA:*
Abun da yake asali a dukkan ibada wanda Allah Ta'ala Ya shar'anta a littafinSa ko ManzonSa, Sallallahu 'alaihi wa sallama, Ya nusar da mu a cikin sunnoninsa, shi ne, tana game maza da mata, har sai idan an samu wani dalili da ya kebance maza ko mata.
Kuma sallan janaza tana daga cikin ibadu wanda Allah da ManzonSa suka shar'anta, don haka tana game maza da mata. Sai dai sahun mata yayin sallan janaza yana kasancewa ne a bayan sahun Maza, kuma ya tabbata cewa Mata sun yi ma Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, salla kamar yadda maza suka yi masa, sai dai basu zuwa makabarta domin rufe mamaci saboda Manzon Allah, Sallallahu' alaihi wa sallama, ya yi hani akan haka.
Amsawa: Al-Lajnatu al-Daa'imah Lil iftaa'i.
A duba littafin فتاوى المرأة المسلمة shafi na 443.
✍🏼 Tattarawa:
*_Mal Umar Shehu Zaria_*
Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

0 comments:
Post a Comment