August 2017 ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday, 31 August 2017

WASIYYAH GAME DA SALLAH! Zauren fiqhu

WASIYYAH GAME DA SALLAH!
*******************************
Acikin addinin Musulunci bayqn kalmar shahada babu wani abu mafi muhimmanci kamar sallah. Ita ce ginshikin dukkan ibadu. Amma ayanzu babu abinda matasa zuka fi wulakantarwa fiye da ita.

To bari mu biyo cikin tarihi mu dubi yadda take awajen Annabawan Allah (alaihimus salam). Sune mafiya daraja agun Allah amma ku dubi yadda zuke game da sallah :

Annabi Eisa (as) yana cikin tsumman goyo, alokacin da yayi magana yana cewa :

"KUMA (UBANGIJINA) YAYI MUN WASIYYAH DA YIN SALLAH DA ZAKKAH MUTUKAR INA RAYE".

Shin ko zuciyarka zata iya kwatanta maka jariri acikin zanin haihuwarsa yana magana, har ma yana yin bayani game da Muhimmancin sallah?.

Annabi Ibraheem (alaihis salam) yayi shekaru Tamanin (80) kafin ya samu haihuwar 'dansa yna farko. Mma haka ya 'dauki wannan Mai jegon tare da Jaririn nata ya kaisu cikin Qungurmin dajin Sahara mai ya ajiyesu (Wato Gurbin Birnin Makkah na yanzu).

Ya daga hannunsa yana addu'a yana cewa : "YA UBANGIJINMU HAKIKA NI NA AJIYE WASU DAGA CIKIN ZURIYYATA ACIKIN WANI KWARI MARAR SHUKE-SHUKE, A KUSA DA 'DAKINKA MAI ALFARMA.

"YA UBANGIJI DOMIN SU TSAYAR DA SALLAH NE... ".

'Dan uwa dubi Muhimmancin Sallah!.


Yayin da Annabi Musa (alaihis salam) yazo ganawa da Ubangijinsa (SWT) a farkon ganawarsu abinda Allah yace masa :

"NI NINE ALLAH BABU WANI ABIN BAUTA SAI DAI NI. KA BAUTA MIN KUMA KA TSAYAR DA SALLAH SABODA AMBATONA".

'Yan uwa ku dubi muhimmancin sallah dai!.


Lokacin da Fir'auna da Qaruna suka matsa ma mutanen Annabi Musa (as) sai Allah yayi wahayi ga Annabi Musa da Annabi Haruna cewa :

"SAI MUKAYI WAHAYI ZUWA GA MUSA DA 'DAN UWANSA CEWA KU TANADAR MA MUTANENKU GIDAJE A MISRA (KO ISKANDARIYYAH) KUMA KU SANYA GIDAJENKU BISA ALKIBLAH, KUMA KU TSAI DA SALLAH.. KUMA KAYI MA MUMINAI ALBISHIR".

Malamai suka ce albarkacin wannan sallolin da suka rika yi suna rokon Allah, sai Allah ya gaggauta basu nasara, kuma ya hallakar da makiyinsu (Fir'auna da Jama'arsa).

Ga Annabi Sulaiman (as) ya fito yana kallon dawakansa har rana ta fa'di bai sani ba. Don haka ya dauki takobi ya rika safe wuyoyinsu da Qafafunsu don neman yardar Allah, saboda kallonsu ne ya shagaltar dashi har rana ta fa'di bai sallaci la'asar ba. (Kamar yadda Qurtubiy ya fa'da a tafseerinsa).

ANNABI ZAKARIYYA (AS) Ya riga ya tsufa sosai Lokacin da Mala'iku suka zo masa da albishir cewa zai samu haihuwa. Amma sun sameshi yana sallah ne. Allah ya gaya mana :

 "SAI MALA'IKU SUKAYI KIRANSA ALHALI SHI YANA TSAYE YANA SALLAH ACIKIN MASALLACI''.

Yayin da Allah ya cika ni'imominsa bisa babban bawansa, wato Annabi Muhammadu (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) Sallah ita ce ibadar da ya za'ba yake yinta babu dare babu rana domin nuna godiyarsa ga Ubangijinsa har sai da Qafafunsa suka kumbura amma bai dena ba.


Lokacin da wasu Kafirai suka shagaltar da Manzon Allah (saww) game da sallar La'asar, sai da yayi wata addu'a mai ban-tsoro akansu.

Yace "ALLAH YA CIKA QABURBURANSU DA GIDAJENSU DA WUTA JAMAR YADDA SUKA SHAGALTAR DAMU DAGA SALLAR LA'ASAR".


'Yan uwa Sallah fa ita ce Qarshen abinda Manzon Allah (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) yayi ma al'ummarsa wasiyyah da ita aranar da zai bar duniya.

Ya Allah ka sanyamu cikin bayinka masu tsaida Sallah bisa lokutanta tare da cikakken ikhlasi.

DAGA ZAUREN FIQHU (28-08-2017 06-12-1438).

Ya Allah ka daukaka darajojinmu dayi mana arzikin duniya da lahira, ka haramta ma jikkunanmu cin wuta damu da iyayenmu da iyalanmu da 'yan uwanmu da dukkan Musulmai baki daya.

DOMIN SAMUN MUHIMMAN ABUBUWAN TARIHI DA FIQHU DA HADISAI, KU ZIYARCI SHAFUKANMU www.zaurenfiqhu.com FACEBOOK @zaurenfiqhu ko kuma www.facebook.com/zaurenfiqhu

KARANTA WANNAN
HUKUNCIN SALLAR IDI A RANAR JUMU'AH!!! DAGA KWAMITIN BINCIKE NA ILIMIN ADDINI DA FATAWA NA KASAR SAUDIYA




Share:

(Video) KUSKUREN DR. GUMI GAME DA HADISIN UMMU SALAMAH NA ASKI DA YANKE FARCE GA MAI LAYYAH !!


KUSKUREN DR. GUMI GAME DA HADISIN UMMU SALAMAH NA ASKI DA YANKE FARCE GA MAI LAYYAH !!

Allah kanuna mana gaskiya gaskiya ce kabamu ikon binta. Allah kanuna mana karya karya ce kabamu ikon barinta Ameen.

DOMIN SAUKO DA WANNAN VIDEO SAIKU DANNA WANNAN BLUE RUBUTU DAKE KASA 👇👇👇

DOWNLOAD VIDEO NOW

     AYI KALLO LAFIYA

SHIGA NAN DOMIN KARANTAWA.
KURAKUREN DR.AHMED GUMI GAME DA HADISIN UMMU SALAMA NA ASKI YANKAN FARCE GA MAI LAYYA



KUCI GABA DA KASANCEWA DA WANNAN SHAFIN A KODA YAUSHE MUN GODE.
Share:

HATTARA DAI KOREN MACIJI ACIKIN CIYAWA! Zauren fiqhu

HATTARA DAI KOREN MACIJI ACIKIN CIYAWA!
***********************************************
Daga cikin dukkan ni'imomin da Allah yake yiwa bayinsa, bayan imani dashi da kuma Soyayyar Annabinsa (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) babu kamar Ilimi da kuma aiki dashi.

Babban abun farin ciki ne yadda awannan zamanin zaka ga Qananan yara sun haddace Alqur'ani, sun haddace litattafai na hadisai, sun haddace Seerah nai yawa, Kuma daidai gwargwado ana bada himma wajen ibadah.

To amma inda gizo yake saqar shine wajen aiki da abinda aka koya, da kuma kyautata dabi'u acikin kowacce Mu'amala.

Zaka ga Matashi mai ilimi, mai kyawawan tufafi, kullum yana masallaci, ga siffah irin ta masu tsoron Allah. Amma zuciyarsa "Wayam" babu cikakken tsoron Allah ko muraqabah da Ubangijinsa.

Kwanan nan wata baiwar Allah take koka min wata matsala da taso ta afka!. Domin ita dai yarinya ce mai kulawa da addini, ga kuma ilimi daidai gwargwado. Kuma burinta ta samu mutum mai addini mai tsoron Allah amatsayin miji gareta.

Kwatsam sai wasu Malamai suka zo Makarantarsu sukayi musu Lekchochi akan addini. Har ma wani daga cikin Maluman ya kyalla ido ya ganta yace yana so. Ya karbi lambar wayarta kullum yayi mata Text. Ayoyin Alqur'ani da hadisai da sauransu.

Ana haka har dai yaje gidan su yarinyar yayi gaisuwa, Ya nemi izinin iyayenta game da neman aurenta.. Kuma suka amince masa (Saboda la'akari da siffofinsa).

Amma tun aranar da ya koma gida sai ya turo mata text mai tada hankal kamar haka "DARLING, TUNDA NAZO GIDANKU NAYI GAISUWA AI MUN ZAMA DAYA". ( A karshen maganar dai yace wai yana so ta amince su rika yin chatting irin wanda zai sa mutum yayi wanka!!).

Ta nuna masa ita bata gane me yake nufi ba.. Sai yace wai shi sha'awa ce ke damunsa, don haka yake neman agajinta, ta rika yi masa hotuna tana tura masa, ko kuma su rika yin "SEX CHAT".

Tun daga ranar taji kamar zazzabi ya rufeta, ta gujeshi ta goge lambar wayarsa ma. Kuam tace masa har abada kar ya sake kulata..

To wallahi irin haka tana yawan faruwa atsakanin matasa. Kuma Allah ne ka'dai  yasan yawan 'Yan matan da suka rasa Budircinsu ta dalilin irin wadannan Shaitanun Samarin (KURA DA FATAR RAGO).

Duk yadda kike son saurayi, kada soyayyarsa tasa ki biye masa ku rika sa'ba ma Allah. Idan kikayi haka kinci amanar Allah da Manzonsa (saww) kuma kinci amanar Mahaifanki da 'yan uwanki da danginki (Kin shigo musu da alfasha cikin zuriyarsu).

'Yan Mata kuyi hankali da irin wadannan samarin domin kuwa sunfi hatsari, Kuma sun fi wuyar ganewa fiye da "KOREN MACIJI ACIKIN CIYAWA".

Kiyi hankali kada saurayi ya mayar dake "KARUWAR GIDA". Ya kwashe miki albarkar rayuwarki! Ya janyo miki asarar duniya da lahira, da zubewar mutunci agun Allah da bayinsa.

NASIHA CE DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (29-08-2017 07-12-1438).


Share:

KURAKUREN DR. GUMI GAME DA HADISIN UMMU SALAMAH NA ASKI DA YANKE FARCE GA MAI LAYYAH !! Minbarin malamai

KURAKUREN DR. GUMI GAME DA HADISIN UMMU SALAMAH NA ASKI DA YANKE FARCE GA MAI LAYYAH

Na ga wasu faifan bidiyo guda biyu wadanda a cikinsu Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi yake cewa: -wai- Hadisin A'isha (ra) ya soke Hadisin da Ummu Salamah (ra) ta ruwato Annabi (saw) ya hana yin aski da yanke farce ga mai yin layyah idan watan Zul- Hijja ya kama.

To bayan mun nazarci maganar Dr., mun fahimci lallai akwai kurakurai a cikinta, daga ciki:

1- Kafin a yi Da'awar Hadisi kaza ya soke Hadisi kaza sai an tabbatar da cin karo a tsakaninsu, saboda asali babu karo tsakanin Hadisan guda biyu, saboda Hadisin A'isha (ra) a kan Hadaya yake magana, Hadisin Ummu Salamah (ra) kuma a kan Layyah yake magana. Don haka maganar a ce: daya ya soke daya ma ba ta taso ba.

2- Kuma ko za a sallama a kan akwai karo tsakaninsu to sai mu tambayi Dr. Gumi mu ce masa: Me Dr. yake nufi da "sokewa", a inda ya ce: Hadisin A'isha (ra) ya soke na Ummu Salamah (ra)?

In "Naskhu" yake nufi, wato soke hukunci, to muna so Dr. ya tabbatar mana da Tarihin Hadisan guda biyu, ma'ana; lokacin da kowane Hadisi ya faru, saboda akwai bukatar sanin Tarihi. Saboda ba za a ce: Hadisin A'isha (ra) ya soke na Ummu Salamah (ra) ba har sai an tabbatar cewa; Hadisin Ummu Salamah (ra) ne ya fara zuwa a farko, daga baya kuma Hadisin A'isha (ra) ya biyo baya.

In kuma ba sokewa na "Naskhu" Dr. yake nufi ba, "Tarjihi" yake nufi, to sai mu ce: ai kafin a isa ga "Tarjihi" sai an yi kokarin yin "Jam'i"; a hada Hadisan guda biyu a yi aiki da su gaba daya, kamar yadda Malaman Malikiyya suka yi, suka hada Hadisan biyu suka ce: MUSTAHABBI ne kar a yi aski, kar a yanke farce, a maimakon su ce: Wajibi ne.
Su ba "Tarjihi" suka yi suka jefa Hadisin Ummu Salamah (ra) a Bola ba, kamar yadda shi Dr. ya yi.

A baya an bayyana wa mutane hakikanin Mazhabar Malikiyya game da wannar mas'ala, inda muka ga cewa: magana mafi rinjaye a Malikiyya ita ce: MUSTAHABBI ne nisantar aski da yanke farce, ma'ana; yin aski da yanke farcen MAKRUHI ne ga mai layyah a cikin kwanaki goma na Zul- Hijjah.

3- In kuma "Tarjihin" za a yi sai mu ce:

(1) Hadisin A'isha (ra) gamamme ne (Aam), Hadisin Ummu Salamah (ra) kuma kebantacce ne (Khaas), a bisa ka'idar Malaman Usulul Fiqh: ana dora gamamme ne a kan kebantacce. Don haka sai a ce: komai ya halasta ga mai layyah, amma ban da aski da yanke farce.

(2) Hadisin A'isha (ra) aiki ne, Hadisin Ummu Salamah (ra) kuma magana ne, a bisa ka'ida ana gabatar da magana ne a kan aiki.

(3) Hadisin A'isha (ra) ya zo da lafazi guda biyu; daya a sake Mutlaqi, an ce: komai, daya kuma an kayyade shi da kusanar iyali. Bukhari da Muslim sun ruwaito daga A'isha (ra):
«لقد كنت أفتل قلائد هدي رسول الله صلى الله عليه وسلم، فيبعث هديه إلى الكعبة، فما يحرم عليه مما حل للرجال من أهله، حتى يرجع الناس»
صحيح البخاري (7/ 103)

"Na kasance ina tufka alamomin hadayar Manzon Allah (saw), sai ya aika da hadayar tasa zuwa Ka'aba (Makka), amma babu abin da yake haramta a gare shi na abin da ya halasta wa maza GAME DA IYALINSA, har sai mutane sun dawo".

Ga lafazin Muslim kuma kamar haka:
«أنا فتلت تلك القلائد من عهن كان عندنا، فأصبح فينا رسول الله صلى الله عليه وسلم حلالا، يأتي ما يأتي الحلال من أهله، أو يأتي ما يأتي الرجل من أهله»
صحيح مسلم (2/ 958)

"Ni ina tufka alamomin hadaya daga auduga da muke da shi, sai Manzon Allah (saw) ya wayi gari a cikinmu yana cikin halasci (ba mai haramar aikin Hajji ba), yana aikata abin da wanda ba ya cikin harama yake aikatawa GAME DA IYALINSA, ko cewa ya yi: yana aikata dukkan abin da mutum yake aikatawa GA IYALINSA".

Ma'ana; iyali ne Annabi (saw) bai nisanta ba.

Don haka, a bisa ka'idar Malaman Usulul Fiqh, ana dora Mutlaqin Nassi ne a kan kayyadadde, a hade Hadisan guda biyu a yi aiki da su gaba daya.
Shi ya sa Imamu Tahawiy ya ce:
فكان في هذا الحديث القصد بالذي كان رسول الله صلى الله عليه وسلم لا يجتنبه هو ما كان يجتنبه من أهله مما يجب على المحرم اجتنابه من أهله في إحرامه، لا ما سواه من حلق شعره، ولا من قص أظفاره، وذلك لا يمنع ما في حديث أم سلمة الذي رويناه، ويكون تصحيح ما رويناه عن أم سلمة، وما رويناه عن عائشة: أن يكون حديث أم سلمة على منع من أراد أن يضحي , وله ما يضحي , عن حلق شعره، وقص أظفاره في أيام العشر حتى يضحي، وحديث عائشة على الإطلاق لما سوى قص الأظفار، وحلق الشعر، له من تلك الأيام، وأنه فيها بخلاف ما المحرم عليه في إحرامه في تلك الأشياء كلها، حتى تتفق هذه الآثار كلها، ولا يضاد بعضها بعضا.
شرح مشكل الآثار (14/ 141 - 142)

Haka babban Malamin Malikiyya Ibnu Rushd (Kakan) shi ma ya ce:
وقد جمع بين الحديثين بعض من ذهب إلى الأخذ بحديث أم سلمة بأن قال: معنى حديث عائشة أنه لم يحرم على رسول الله - صلى الله عليه وسلم - شيء مما أحل الله له من أهله حتى نحر الهدي على ما جاء في بعض الآثار عنها وحرم عليه ما سوى ذلك من حلق الشعر وقص الأظفار على ما جاء في حديث أم سلمة.
البيان والتحصيل (18/ 166 - 167)

Wannan bisa fahimtar wadanda suka tafi a kan wajabcin nisantar aski da yanke farce kenan.

4- Kuma abin da ya fi shi ne mu dauki fahimtar Malaman da suka ce: WAJIBI ne kar a yi aski da yanke farcen, saboda yana daga cikin ka'idoji na kubutar Addinin bawa, mutum ya fita daga tsakanin sabanin malamai, gara ka dauki fahimtar Malaman da suka ce WAJIBI ne, don kar ka aikata ka wayi gari ka aikata Haramun.

5- Sa'annan kuma wani abin mamaki da Dr. ya yi shi ne rushe Hadisin Ummu Salamah (ra) da Qiyasi, inda ya nuna cewa: in za a yi aiki da Hadisin Ummu Salamah (ra) to kamar yadda ba za a yi aski ba, ba za a yanke farce ba, to haka ma kar a shafa turare, kar a yi jima'i. Alhali Dr. ya manta cewa: Qiyasi ba ya rushe Hadisi, kamar yadda ba ya yi masa "Naskhu" ya goge shi, kuma kamar yadda ba a Qiyasi a tare da Nassi. Duk wani dalibin ilimi ya san haka, balle kuma kwararre a Usulul Fiqh.

Don haka in Dr. ya ce: don me ya sa ba ku sa turare, ba ku nisantar jima'i kamar yadda kuke nisantar aski da yanke farce?
Sai mu ce: saboda Annabi (saw) bai hana turare da jima'in ba, alhali ya hana aski da yanke farce.

6- Daga cikin abin da Dr. ya fada ya ce: "A cikin Littatafan Mazhab, babu wanda ya ce: in za ka yi layya ka tsaya cikin datti".

Wannar magana ba dadai ba ce, saboda maganganun Malaman Malikiyya da aka kawo daga littatafan Mazhabar a rubutun da ya gabata mai taken: "HUKUNCIN ASKI DA YANKE FARCE GA MAI LAYYAH A MAZHABAR MALIKIYYA" suna karyata wannar magana.

Shiga nan ka karanta:
https://www.facebook.com/amyuguda/posts/1604515102945514?sw_fnr_id=3982568894&fnr_t=0

A ciki an kawo maganganun Malaman Mazhabar Malikiyya guda goma sha daya (11). Ga karin guda daya da ba a kawo a can ba. Al- Sawiy ya ce:
تنبيه: يندب ترك حلق الشعر من سائر البدن وترك قلم الأظفار في التسعة الأيام الأول من ذي الحجة لمن يريد الضحية ولو بتضحية الغير عنه
حاشية الصاوي على الشرح الصغير = بلغة السالك لأقرب المسالك (2/ 141)

"Fadakarwa: Mustahabbi ne barin aski a jiki gaba daya, da barin yanke farce a kwanaki taran farko na Zul- Hijjah ga wanda ya yi niyyar layya, ko da wani ne zai yi masa layyan".

Wannan shi yake nuna kuskuren maganar Dr. inda yake cewa; -wai- Fuqaha'u ba su yi aiki da Hadisin Ummu Salamah (ra) ba.
To a nan sai mu tambayi Dr. wadanne Fuqaha'un yake nufi?
Mu dai mun samu Malaman Malikiyya sun yi aiki da Hadisin, kai hasali ma Sahabbai (Salaf) sun yi aiki da shi kamar yadda Imamu Tahawiy ya ruwaito daga Qatada ya ce:
"إن كثير بن أبي كثير سأل سعيد بن المسيب: أن يحيى بن يعمر يفتي بخراسان - يعني كان يقول -: " إذا دخل عشر ذي الحجة، واشترى الرجل أضحيته، فسماها , لا يأخذ من شعره وأظفاره "، فقال سعيد: قد أحسن، كان أصحاب رسول الله صلى الله عليه وسلم يفعلون ذلك , أو يقولون ذلك".
شرح مشكل الآثار (14/ 142)

"Lallai Kathir bn Abi Kathir ya tambayi Sa'eed bn Al- Musayyab cewa; lallai Yahya bn Ya'amar yana fatawa a Khurasaan, yana cewa: {Idan kwanaki goman Zul- Hijjah sun shiga, mutum ya sayi layyarsa, ya ambace ta a matsayin dabbar layyah, to kar ya cire gashinsa ko farcensa}.
Sai Sa'eed ya ce masa: {Hakika ya kyauta, saboda Sahabban Manzon Allah (saw) sun kasance suna aikata hakan, ko cewa ya yi: suna fadan hakan}".

Don haka wannan yana karyata maganar Dr, kuma yana karyata fadinsa -wai- Sunna ba ta tafi a kan Hadisin ba.

Ta yaya za a ce: Sunna ba ta tafi a kansa ba, alhali ya tabbata daga Annabi (saw), Sahabbai sun yi aiki da shi, Malaman Fiqhun Mazhabobi sun aiki da shi in ban da Hanafiyya da Dr. Gumi?!

Saboda haka, alal akalli Malaman Malikiyya sun tafi ne bisa MUSTAHABBANCIN rashin yin aski da yanke farce a cikin wadannan kwanaki goma ga wanda ya yi niyyar yin layyah. Don haka mai so a bi Malikiyya a kan wannan ya kamata ya dora mutane.

Saboda haka, jama'a kar ku lura da maganar Dr. ku yi watsi da ita ku rike maganar sauran Malamai da suka ce MUSTAHABBI ne ko WAJIBI.

7- Sa'annan kuma siffanta wannan aiki na Shari'a, wanda aka shar'anta mana yinsa da cewa: "tsayuwa cikin datti" BABBAN KUSKURE NE, saboda in mun lura za mu ga rashin aski da yanke farce suna cikin aiyukan Hajji, aibanta wannan da kiransa da "tsayuwa cikin datti" yana lazimta aibanta aikin Hajji.

Sa'annan kuma me Dr. zai fadi game da Annabi (saw) da ya zauna ba aski ba yanke farce har tsawon kwanaki goma sha biyar (15), saboda ya yi harama a Zul- Hulaifa a ranar 24 ga watan Zul- Qa'ada. A'isha (ra) da Ibnu Abbas (ra) suka ce:
خرجنا مع رسول الله صلى الله عليه وسلم، لخمس بقين من ذي القعدة، لا نرى إلا الحج
صحيح البخاري (2/ 171) صحيح مسلم (2/ 876)

Annabi (saw) ya zauna cikin harami, babu aski ba yankan farce har zuwa ranar 10 ga Zul- Hijja ranar da ya yi aski, don haka za a ce: Annabi (saw) ya tsaya a cikin datti kenan?!

Saboda haka muna fatan Dr. zai zama mai lura da kalmomi da yake amfani da su yana sukan Hadisan Annabi (saw), "lawazim" dinsu munana ne matuka a Addini.

Allah ya kubutar da mu.
Share:

Wednesday, 30 August 2017

Video:- Abin Da Zaka Kula Dashi Ranar Sallah Dr Abdalllah Usman Gadon Kaya

Video:- Abin Da Zaka Kula Dashi Ranar Sallah Dr Abdalllah Usman Gadon Kaya

GORON SALLAH

MAI TAKEN: Abin Da Zaka Kula Dashi Ranar Sallah

TARE DA: DR.ABDALLAH USMAN UMAR GADON KAYA

7/12/1438
29/8/2017​


Download video now
Share:

Audio:-Nasiha Mai taken: Ranar Arfa Tare da: Dr Isah Ali Ibrahim Pantami


Takaitaciyar Nasiha

Mai taken: Ranar Arfa

Tare da: Dr Isah Ali Ibrahim Pantami

7/12/1438
29/8/2017​


Download Audio Now
Share:

Makwabcin Sheikh Kabiru Gombe ya kai kararsa gaban kotu kan zarginsa da aikata wani laifi !! - Naijhausa.com

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan ya amsa sammacin da wata kotun jihar Kano ta aike masa sakamakon kararsa da wani makwabcinsa ya shigar akansa, kamar yadda jaridar Alfijir ta ruwaito.
Shi dai wannan makwabci na Malam Kabiru Gombe yayi kararsa ne gaban kotu kan zarginsa da take hakkin makwabtaka, kamar yadda ya shaida ma alkalin kotun, Sarki yola
Majiyar NAIJ.com ta ruwaito makwabcin yana fadin wai Kabiru Gombe ya sanya wasu waga wagan Tagogi a sabon gidansa daya gina a unguwar Sabuwar Gandu, inda makwabcin ke zarginsa da samun damar liken matayensu.
Makwabcin Sheikh Kabiru Gombe ya kai kararsa gaban kotu kan zarginsa da aikata wani lafi
Sheikh Kabiru Gombe
Makwabcin ya kara da cewa “Wannan Malamin ya gina manyan tagogi, sa’annan ya sanya musu bakaken gilasai, ta yadda shi zai iya ganin jama’a, amma mu ba zamu gan shi ba.” kamar yadda majiyar NAIJ.com ta rwuaito.
Wannan makwabci dai ya cigaba da shaida ma kotu cewar tun lokacin da aka fara ginin gidan suka janyo hankalin Malamin, amma bai dauki wani mataki game da hakan ba.
Sai dai lauyan Malamin Ishaq Adam Ishaq ya bayyana ma kotu cewar ba wani bane ke damun wannan makwabci illa bakin ciki da hassada da suke yi Malamin sakamakon daukaka da Allah yayi masa.
Daga karshe dai Alkali Sarki Yola ya aika da jami’an kotu da su tafi su gano masa yadda wadannan tagogi suke, sa’annan su kawo masa rahoton abinda suka gani, bayan nan sai a cigaba da sauraron karar.

SHIGA NAN  (Video) abinda zaka kula dashi ranar Sallah - Dr abdullahi usman gadon kaya

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.
Share:

RANAR ARFAT

*RANAR ARFAT*

Babu wata RANA a wajen Allaah da tafi Wannan Rana ta *Arfa.*

A wannan rana ne Allaah Zai kusanto ga zuwa duniya, kuma zai zama yana alfahari da bayinSa na duniya wanan ranar.

An karbo Hadisi daga Ibn Hibban (RA), Cewa, ANNABI (SAW) ya ce, Allaah  Madaukaki, yakan saukowa saman duniya (sama ta 1), a ranar Arfa yana mai alfahari da bayinSa,
sai ya cewa mala'iku ku kalli bayiNa sun zo daga sassa na duniya daban-daban don su amsa kiraNa.

Sai Allaah (SWT) Ya tambayi mala'iku ya ce, me ku ka ji suna rokoNa game da shi? Sai mala'iku su ce mun ji suna rokon Aljannarka Ya Ubangiji.

Sai Allaah (SWT) ya ce dasu, shin sun ga Aljannar tawa ne? Sai su ce a'a ba su riga sun ganta ba, sai dai sun yi imani da cewa akwai ta.

Sai Allaah (SWT) Ya ce, ya ya ku ke gani inda a ce sun ganta? Sai su ce ya Ubangiji inda sun ganta da sun tsananta wajen neman Ka shigar da su cikinta.

Sai Allaah (SWT) Ya sake tambayarsu, me kuma ku ka ji suna neman na tsare su daga gareta? sai su ce, mun ji suna neman Ka tsaresu daga wutarKa Ya Ubangiji.

Sai Ya ce shin sun ga wutar ne? Sai su ce ba su ganta ba Ya Ubangiji, sai ya ce ya ya ku ke tsammani idan da a ce sun ganta?

Sai su ce Ya Ubangiji in da sun ganta da za su tsananta wajen neman Ka tsare su daga gareta. Sai Allaah (SWT) Ya ce, ina mai shaida muku cewa na gafarta musu.

 (Abu Ya’la, Ibn Khzayma, Al-Bazzar da Ibn Hibban).

A wannan Rana shaidan yake Raina kansa, a wannan rana cike zuciyarsa (Shaidan LA) take da bakin ciki.

Abu Ad-Darda ya rawaito Manzon Allaah (SAW) yana cewa babu ranar da Shaidan ya tsana kamar ranar Arfah, saboda a ranar ne yake raina kansa da kansa, an kaskantar da shi da ringa jin haushi. Dalilin jin haushin Shaidan kuwa a wannan rana shi ne saboda Ubangiji yana ‘yanta bayinSa da dama a wannan rana, babu wata ranar da ta kai wannan ‘yanta bayi sai dai ranar yakin Badr, wanda Ubangiji ya ‘yanta bayinSa da dama a wannan ranar, wannan ya sa Shaidan yake kasance cikin kunci a wannan rana.

★ Mafificiyar addu’ar da Mutum zaiyi a ranar Arfa ita ce:

ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ،ﻟﻪ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻗﺪﻳﺮ

LA’ILAHA ILLALLAHU WAHADAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI’IN KADEER.

Fassara:-
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allaah, Shi Kadai, babu abokin tarayya a gare Shi.. Mulki nasa ne Shi Kadai, yabo ma nasa ne Shi Kadai, kuma Shi Mai iko ne akan komai.

Akwai azumi a ranar arfa, wanda Manzon Allaah SAW ya ce: azumin yana zama sanadiyar Allaah SWT Ya sharewa mutum zunubin shekara 2,

Kuma ana kar6a addu'a a wanan ranar

NB; Arfat zata fado ne a ranar lahadi 09/12/1438 daidai da 31/08/2017 in-shaa-Allaah

Ya Allah kasa mu dace da Alkheran da ke cikin Wannan Rana ta Arfat.

*© Dausayin Mutanen Kirki*


Share:

SHIN DA YIN LAYYA DA BIYAN BASHI WANNE YAFI?

*SHIN DA YIN LAYYA DA BIYAN BASHI WANNE YAFI?*

الحمد لله.

*AMSA;* Biyan Bashi shine yafi, kuma shine yake dole sama da yin layya, saboda dalilai Masu Yawa.

1- Biyan Bashi dolene, Layya kuma Sunnah ce Mai qarfi, ba'a gabatar da Sunnah akan wajibi, har a wajan wadanda suke ganin layya wajibice, sunce biyan bashi shine abun gabatarwa akan layya, domin layya a wajan wadanda Sukace dolece, tana Zama tilas ne akan mai iko, Mai bashi kuma ba Mai iko bane.

2- A cikin biyan bashi akwai kubuta daka nauyin dake kan mutum, wajan ayyana layya kuma shagalane da nauyin, babu shakka Sauke nauyi shine yafi sama da shagala dashi.

3- Bashi Haqqin bayine, Layyah haqqice ga Allah da Mawadaci, A wannan hali za'a gabatar da hakkin bayine

4- Ci gaba da Zaman bashi akan mutum akwai hadari babba, saboda tsoran kada sai ranar alqiyama za'a biya da kyawawan ayyukan mutum.

Acikin haka akwai hadari domin a wannan halin mutum yana cikin tsananin buqatar kyakkyawan aiki koda dayane.

Da Wannan zai bayyana gareka cewa biyan bashi yafi sama da yin layya, saidai idan bashi yana da lokaci maitsawo, ta yanda wanda ake bin bashi yana da mafi rinjayen zaton zai iya biyan bashin alokacin da aka deba masa, idan yayi layya, ko ya ranci abunda zai iya biya koda alokacin bai biyaba, Babu laifi akansa ya yanka layya gwar-gwadon Abunda Allah ya buda masa, zai samu lada da Sakamako Awajan Allah.

Kamar yanda bayani yazo acikin littafin Sharhin Mumti'i (8/455).

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*


Share:

WACCE DABBA CE TAFI FALALA WAJAN YIN LAYYA DA ITA?

*WACCE DABBA CE TAFI FALALA WAJAN YIN LAYYA DA ITA?*

الحمد لله سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA :* Dabbar datafi falala wajan layya Itace (Raqumi) Sannan (Saniya) Sannan (Tunkiya) Sannan Tarayyah wajan yanka (Saniya) haka Abu Hanifa da Shafi'i sukace.

Saboda fadin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ( Wanda yaje masallacin juma'a da Wuri asa'ar farko, Kamar ya gabatar da Sadakar ( Raqumi ne) Wanda yaje asa'a ta biyu kamar ya gabatar da ( Saniya) ne, Wanda yaje a sa'a ta uku kamar ya gabatar da (da rago mai qaho ) ne, Wanda yaje a sa'a tahudu kamar ya gabatar da ( Kaza)ne, Wanda yaje Asa'a ta biyar kamar ya gabatar da ( Kwai) ne,

*Bukhari (881) da Muslim (850).*

Domin yankane da'ake neman kusancin Allah dashi, sai raquma tafi falala kamar hadaya, yi da Rago yafi falala akan mutane su hadu suyi da (Raqumi) domin Zubar jini shine manufa a layya, Wanda yake shi kadai zai samu kusancin Allah da zubar dashi baki daya, A cikin tumaki da awaki rago shine yafi falala, domin dashi Annabi Sallallahu Alaihu wasallam yayi layya, saboda yafi kyawun nama.

*Duba Al-Mugni (13/366).*

Kamar Yanda yazo a *fatawa Lajnah (11/398).*

Abunda ake hujja dashi cikin hadisin shine yanda aka samu fifikon kusantar Allah tsakanin (Raqumi da Saniya) da (Tumaki da Awaki) Saboda raqumi yafi kudi da yawa da nama da amfani, Haka Malaman mazhabobi ukun nan sukace: *Abu hanifa, da Shafi'i, da Ahmad*.

Imamu Malki yace: Abunda yafi falala wajan layya shine ragon daya shekara daya, sanann Saniya, sannan Raqumi.

Domin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yayi layya da raguna guda biyu, shi kuwa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam baya aikata abu sai wanda yake yafi falala.

Amsa akan wannan sai ace: Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya zabi ragone don sauqaqawa Al'ummarsa, domin suna koyi dashi, Bayaso ya taqurawa Al'ummarsa, haqiqa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya bayyana falalar raqumi akan Saniya.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*



Share:

MENENE HUKUNCIN YANKAN LAYYA DA HANNUN HAGU?

*MENENE HUKUNCIN YANKA LAYYA DA HANNUN HAGU?*

الحمد لله سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA :* Mustahabbine Mutum ya yanka dabba da hannun dama, domin yafi hutar da dabba, Yanda mafi yawan Mutane suna Amfani da hannun dama ne.

Yanka da Hannun hagu Sabanine na Wanne yafi falala, wanne yafi hutar da dabba, Saidai idan da hannun Hagune mutum zai iya yanka hakan shine yafi falala Agareshi, sama da ya yanka da dama.

Ba Sharadi bane wajan yanka ya Zama da hannun dama, ya Halatta yankawa da Hannun dama Dana hagu.

Domin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yace: ( Wanda ya zubar da jini ya Ambaci sunan Allah kuci).

Bai iyakance da Hannun hagu ko dama ba, saidai babu kokwanto da Hannun dama yafi falala, domin Hannun dama yafi qarfi, idan ko yafi Qarfi da shine Abun yankawar zaifi jin Sauqi.

Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yayi Umarni da Sauqaqawa Abun yanka inda yace: ( Allah ya Wajabta Kyautatawa Akan kowane Abu, idan zakuyi kisa ku kyautata kisan, idan zakuyi yanka ku kyautata yanka, Dayanku ya Wasa Wuqarsa, ya hutar da Abun yankansa.)

Idan Mutum bahagone yankawa da hagu shine yafi falala awajansa, .

Babu Laifi dan Mutum ya yankan layyarsa da hannun hagu.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*


Share:

MENENE HUKUNCIN WANDA BAYA IYA HALATAR YANKA LAYYARSA,?

*MENENE HUKUNCIN WANDA BAYA IYA HALATAR YANKA LAYYARSA,?*

الحمد لله سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA :* Abunda yafi shine mutum ya halarci yanka layyarsa da kansa, idan bazai iyaba, babu laifi wani yaje ya shaida masa yankan layyar tasa.

Domin Wakilci wajan halattar yanka layya ya halatta babu Sabani tsakanin Malamai,

Halartar yanka layya mustahabbine ba dole ba.

Ibnu Qudama yace: Idan ya yanka layyar da hannunsa haka shine yafi, domin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya yanka layyarsa da hannunsa.

Idan Kuma ya wakilta wani ya halatta, saboda Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya Wakilta Aliyu ya qarasa yanka Masa hadayarsa, wannan Babu Sabani akansa, An so ya halarci yanka layyar sa.

*Al-Mugny (13/389-390)*

Ladan layya idan bayarwa kayi ayi maka, dukkan wanda ka Niyyata acikinta zai samu ladan, koda baka halarci yanka taba, saboda fadin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ( Dukkan Ayyuka Saida Niyyah, kowanne mutum akwai Abunda ya niyyata.

Wallahu A'alamu

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*


Share:

SHIN DALILAN YIN LAYYA DALILAINE NA WAJABCI KO MUSTAHABBANCI?

*SHIN DALILAN LAYYA DALILAINE NA WAJABCI KO MUSTAHABBANCI?*

الحمد لله سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA :* A wannan mas'alar akwai Sabani Shahararre tsakanin Malamai, Mafi yawan Malamai suna ganin Sunnatuwar layya ne ba wajabcin taba.

Hanafiyyah da Imamu Ahmad a wata ruwaya da Shaikul
Ibnu taimiyyah ya zaba sun tafi akan wajabcin layya akan mawadaci.

Ibnu qudama yace: mafi yawan malamai suna ganin layya sunnah ce mai qarfi ba dole bace, .

An ruwaito haka daka *Abubakar da Umar da Bilal, da Abi mas'uud Al-badary* Allah yaqara yarda dasu.

Haka *Suwaid bin gafala da sa,'eed bin Musayyeeb da Al-qama da Aswad, da Ada'u da Shafi'i, da Ishaq, da Abu Saur, da Ibnu Munzir* sukace.

Rabi'ah da Malik da Saury da Auza'iy da Lais, da Abu hanifa, sukace: Dolece .

Saboda hadisin da Abu huraira Allah yaqara yarda dashi yace: Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Wanda yake da Wadata baiyi layya ba, kada ya Kusanci masallacin mu).

Daka Miknaf bin Sulaim, Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( yaku Mutane akan dukkan mutanen gida, kowacce shekara akwai layya, da yankan watan rajab na jahiliyyah.).

Darul Qudny ya ruwaito hadisi da isnadi daka ibnu Abbas daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: abubuwa uku wajibine akaina, akan ku kuma nafila ne, wutiri, da Yankan layya, da raka'atanul fajri.

Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Wanda yai nufin zaiyi layya, kada ya aske gashinsa ko farcensa,) Ya Alaqanta ta da Iko  wajibi ba'a jinginashi da iko, .

*Al-mugny (11/95).*

Dalilan dukkan Bangarori biyu na Malamai suna da yawa, saidai dukkansa basu kubuta daka matsala a isnadojinsu ba, ko daka jayayya wajan kafa hujja dasu ba, .

Wadanda Sukace dolece, suna kafa hujja da hadisin Abu huraira ( Wanda yake da wadata yaqi yin layya kada ya kusancinmu masallacinmu) ibnu Majah.

Malaman hadisi basu sallama ingacin maganar daka Annabi ba, sunyi masa hukunci da cewa maganar Abu hurairace ,bata Annabi ba, .

Baihaqi acikin Sunan dinsa (9/260) yace: Labari yazomin Abu isah Atturmuzi yace: Hadisine sahihi, yace: Ja'afar bin rabi'ah ya ruwaitoshi da waninsa daka Abdurrahaman Al-a'araj, daka Abu huraira.

Ibnu hajar yace: ibnu majah ya fitar dashi da Ahmad, mazajensa Amintattune, saidai anyi sabani wajan shin maganar Annabi ce,.

*Fatahul bary (12/98)..*

Wasu sun rinjayar da cewa hadisine mauqufi, kamar Ibnu Abdul barri da Abdul haq acikin Ahkamul wusdaah (4/127) da Munzry acikin Targeeb wattarheeb, da Ibnu Abdul hady acikin tanqeeh (2/498) duba Hashiyar Masu tahqiqin sunanu Ibnu majah (4/303).

Hadisi na Biyu, shine hadisin Abu ramlah daka miknaf bin sulaim Marfu'an, Abu dauda ya ruwaitoshi (2788) da Turmuzy (1596) da Ibnu majah (3125).

Wasu Malamai sun raunatashi saboda jahalar Abu ramlah, sunansa Ãmir, Al-kidaby yace: Hadisine mai rauni, Abu ramlah ba'a sanshi ba, *Ma'alimul Sunan (2/226).*

Zaila'iy yace: Abdul haq yace: Isnadinsa mai raunine, Ibun qaddaãn yace: illarsa shine jahalar abi ramlah, sunansa Amir ba'a sanshi ba saida wannan, ibnu Auun ya ruwaitoshi daka gareshi.Duba *Nasburrayah (4/211).*

Wadanda Sukace: Mustahabbice sun kafa hujjah da dalilai masu yawa, Mafi muhimmancin sune guda biyu.

Hadisin Ibnu Abbas Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Abubuwa uku Wajibaine akaina, akanku kuma Nafilane, *Wutiri, da Yankan layya, da Sallar walaha.)*

Ahmad ya ruwaitoshi (2050) da Baihaqy (2/467).

Hadisin Malamai na da da yanzu sun raunatashi.

Ibnu hajar yace: An ruwaitoshi daka Abiy janaba  Al-kalbi daka ikrimah, Abu janaba za'ifine, mudallasine, yana yin An-ana.

Malamai Sun raunata hadisin kamar *Ahmad da Baihaqy, da Ibnu Salah, da Ibnul jauzy, da Nawawi* da wasunsu.

*Talkeesul Habeer (2/45- 258).*

Hadisi na Biyu: Hadisin Ummu salamah Annabi Sallalahu Alaihi wasallam yace: ( Idan Goman farko na zhul-hijjah ya shiga wanda yake san yin layya, kada ya yanke farcensa ko gashinsa ko fatarsa) *Muslim (1977).*

Imamu Shafi'i yace: Wannan daliline akan layya ba dole bace, Duba *Al-majmu'u (8/386).*

Hadisan da suke nuna Wajabcin layya akwai matsala akansu, duk da wasu malamai sun kyautata wasunsu.

Haka hadisan da suka nassanta Mustahabbanci, ta bangaren isnadi sunfi tsananin rauni.

Abunda yake qar-fafa rashin Shar'antuwar layya sune Abu biyu:

@- Barranta Ta tun asali, matuqar wani dalili kubutacce daka cin karo bai zo ba, to lallai Asali shine rashin wajabci.

Kamar yanda Bin baaz ya bayyana acikin *fatawa dinsa (18/36).*

@- Zantukan sahabbai ingantattu da aka ruwaito daka Sahabbai, ya inganta daka *Abubakar da Umar* da wasunsu sun kasance basa layya, don tsoran kada Wasu mutane su dauka dole ce.

Kamar yanda Baihaqi ya ruwaito  acikin *Ma'arifatu Sunan  Wal-Ãsãar (14/16)  Ka sake duba Sunanul Kubra (9/444) .*

Nawawi acikin *Al-Maj-Mu'u (8/383)* yace: Zantukan da aka ambata daka Abubakar da Umar, Baihaqi ya ruwaitosu da Isnadi kyakyyawa.

Haitami yace: Dabarani ya ruwaitoshi acikin Kabeer mazajensa Ingantattune. Duba

*Mu'ujamul zawa'id (4/18) Albani ya Ingantashi acikin Irwa'u (4/354)..*

Mas'alar dai akwai sabani Abun lura tsakanin malamai.

Wanda sukace: Mustahabbice shine Abunda dalilinsu yafi bayyana agaremu.

Mesan Qarin bayanai saiya duba *Ahkamul Az-hiyyah Wal-zakah na Shaiek Usaimeen, Da Al-Mufassaal fy Ahkamul Azhiyyah.*

Wallau A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*


Share:

YAYA AKE RABA NAMAN LAYYAR DA ZA'ACI DA WANDA ZA'AI SADAKA DASHI?

*YAYA AKE RABA NAMAN LAYYAR DA ZA'ACI DA WANDA ZA'AI SADAKA DASHI?*

الحمد لله سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA :* An ruwaito Umarni da Sadaka da naman layya acikin hadisai ingantattu, kamar yanda aka ruwaito izinin ci da kuma adanawa,

Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daka Aisha Allah ya qara mata yarda tace: Wasu Mutanen Qauye sunzo madina, lokacin layya azamani  Annabi sallallahu Alaihi wasallam, Sai Yace: Ku ajiye naman layya kwana uku, sai kuyi sadaka da Sauran, bayan wata shekarar sai yace: Kuci ku ajiye, na hanaku ajiyewa ya wuce kwana uku saboda baqin da sukazo madina ne.

*Muslim (3643).*

Nawawi yace: acikin Hadisin akwai Umarni da yin sadaka, Abunda yake wajibi ayi sadaka dashi shine abunda sunan sadaka zai gaskatu akansa kawai,

Amma anfiso kayi Sadaka da Mafi yawan naman layyar, mafi karanci shine ka kasa naman gida uku, kayi Sadaka da kashi daya, kayi kyauta da daya, kaci kashi daya.

Wasu sukace: Kaci rabi kai sadaka da rabi, wannan qasa yake wajan kamalar Abunda akeso.

Amma sadaka ta Wadatarwa kawai, abunda sunan sadaka zai gaskatu akansa ya isar.

Cin Naman Layyar Mustahabbine ba dole ba.

Malik Yace: Babu haddi na abunda zakai sadaka dashi na layya, ko wanda zakaci, zaka ciyar da talakawa da mawadata, in kaga dama ka basu danye, inka ga dama ka basu dafaffe ko soyayye.

*Al-kafi (1/424).*

Shafi'iyyah Sukace: Anfi so kayi sadaka da mafi yawan naman, sukace: Mafi qarancin kamala shine kayi sadaka da daya bisa uku, kaci daya bisa uku, kayi Kyauta da Daya bisa uku. ya halatta kaci rabinta, kyauta da wani sashinta shine dole.

*Nailul Audããr (1/145) da Sirajil Wahàaj (563).*

Ahmad yace: Mudai muna bin hadisin Abdullahi bin Abbas Allah yaqara musu yarda, (kaci daya bisa uku, kaciyar da wanda kaga dama da daya Bisa uku, kayiwa miskinai da talakawa sadaka da daya bisa uku).  Abu musa Asfahani ya ruwaitoshi acikin waza'if yace: hadisine kyakkyawa, shine maganar ibnu mas'uud da Ibnu Umar ba'a samu wanda ya Saba musu ba cikin sahabbai.

Duba *Al-Mugny (8/632).*

Dalilin Sabani Akan haddin abunda za'ai sadaka dashi shine sassabawar ruwayoyi,

An samu ruwayar da tazo batare data ayyana abunda za'ai sadakar dashi ba kamar hadisin *Buraida* Allah yaqara yarda dashi, Wanda turmuzi ya ruwaito (1430). yace: Hadisine kyakkyawa Ingantacce.

Wasu sunyi aiki dashi cikin sahabbai da wasunsu Allah yaqara yarda dasu.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*



Share:

SHIN LAYYA WAJIBICE AKAN MAI AIKIN HAJJI?

*SHIN LAYYA WAJIBICE AKAN MAI AIKIN HAJJI?*

الحمد لله سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA :*Malamai Sunyi sabani akan hukuncin layya akan mai aikin hajji, wasu sukace mustahabbice akan mai aikin hajji, wasu sukace babu layya akan mai aikin hajji..

Wadanda sukace babu layya akan mai aikin hajji sunyi sabani akan sababin rashin shar'antuwarta akansa abisa magan-ganu guda biyu:

Nafarko: Sukace mai hajji babu Sallar idi akansa, yankansa kuma shine hadayar tamattu'i, ko Qirani.

Na Biyu : Mai hajji matafiyine, layya kuma an shar'antawa mazaunin gidane, wannan shine maganar Abu hanifa, awajansa mai aikin hajji, idan dan cikin makkah ne shi ba matafiyi bane,  layya ta wajaba akansa.

Hanafiyyah sukace: Wajibice akan matafiyi da Mazaunin gida,  kamar yanda yazo  acikin *Al-Mabsuud (6/171).*

Yazo acikin *"Jauhara (5/285-286)"* Layya ba wajibi bace akan mai hajji matafiyi, amma wanda yake mazaunin makkah wajibice akansa koda zaiyi hajji.

Malikiyyah sukace: Babu layya akan mai hajji, saboda kasancewarsa mai hajji, ba saboda kasancewar sa matafiyi ba. Kamar yanda yazo acikin *Mudawwanah ( 4/101).*

Shafi'iyyah sukace: Layya Mustahabbice akan mai hajji

Imamu Shafi'i yace: Layya Mustahabbice akan mai hajji mazaunin makkah, da wanda ke kai kawo tsakanin gari zuwa gari, da Mazaunin gida,  da wajibice akan wasu banda wasu, da akan mai hajji zatafi zama dole, domin yankane, mai hajji kuma akwai yanka akansa, saidai bai halatta a wajabtawa mutane abuba saida hujja, babu ban-banci tsakaninsu.

*Al'Ummu (2/348).*

Ibnu hazam yace: Layya ga Mai hajji mustahabbice kamar yanda take akan wanda baije hajji ba, .

Wasu sunce babu layya akan mai hajji, Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya kwadaitar akan yin layyah, bai halatta a hana mai hajji falala da samun kusanci ga Allah ba, batare da wani nassi akan hakan ba.

*Al-Muhalla ta Ibnu hazam (5/314-315).*

Hanabila sukace:Layya ta halatta gamai aikin hajji.

Kamar yanda ibnu qudama acikin *Al-mugny (7/180)* Ya fada.

Hadisi yazo daka Aisha Allah yaqara mata yarda Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya yiwa matansa layya a mina ahajjin bankwana.

*Bukhari (5239) da Muslim (1211)* suka ruqaito.

Wasu malamai sunyi raddin hujja da wannan hadisin kamar ibnul qayyeem sukace: Abunda ake nufi da layya a hadisin shine hadaya.

Duba *zhadul Ma'adi (2/262-267)..*

Shaikul Islam da ibnul qayyeem sun zabi maganar masu cewa babu layya akan mai aikin hajji,.

Duba *Al'iqna'a (1/409) da Al-Insaaf (4/110)* Shaik Usaimeen ya rinjyar da wannan zancen..

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*


Share:

MENENE HUKUNCIN YIN LAYYA DA DABBA MAI CIKI?

*MENENE HUKUNCIN LAYYA DA DABBA MAI CIKI?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Malamai Sunyi Sabani akan yin layya da dabba mai ciki, jamhur din malamai sun tafi akan halaccin yin layya da dabba mai ciki, basu Ambaci dabba mai ciki, acikin aibukan da suke hana ayi layya da dabba ba,

Shafi'iyyah sun sabawa Jamhur sukace: Bai halatta yin layya da dabba mai ciki ba,

Yazo: acikin *Mausu'ah fiqhiyyah (16/281).*

Malamai Basu Ambaci dabba mai ciki cikin aibukan da suke hana ayi layya da dabba ba, sabanin shafi'iyyah, inda suka bayyana rashin halaccin yin layya da dabba mai ciki, saboda ciki yana bata ciki, nama ya zama lababbe,.

Ingantacciyar magana shine: Ya halatta ayi layya da ita, idan babu wani abun dazai hana ayi da ita na daban,.

Jaririn da aka Samu acikin dabbar layya, idan an sameshi araye za'a wankeshi aci,

Ibnu qudama yace: idan an sameshi rayayye rayuwa tabbatacciya, daza'a iya tsaftaceshi ba'a tsaftace shi ba, harya mutu, toba tsafta tacce bane, Ahmad yace: idan ya fito araye dole, a tsaftaceshi, domin wani rai ne daban.

*Al-Mugny (9/321).*

Idan aka samu jariri acikin dabbar layya matacce, jamhur din malamai sukace: Za'aci namansa, domin ya tsarkaka da tsarka kuwar uwarsa,

*Abu dauda ya ruwaito (2828) da Turmuzi (1476) ibnu majah ya ingantashi (3199) da Ahmad (10950).*

Daka Abu sa'idin daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Tsarkakuwar jariri, tsarkakar Uwarsa ne) Albani ya ingantashi *acikin Sahihul jami'i (3431).*

Wannan kamar yanda mukace shine mazhabar jamhur din malamai. sabanin Hanafiyyah.

Shaikul Islam ibnu taimiyyah acikin *maj-mu'u fatawa (26/307)* Yace:

Layya da dabba mai ciki ya halatta, idan aka samu danta ya mutu, tsarkinsa shine tsarkin uwarsa, awajan shafi'iyyah da Ahmad, da Wasunsu, yayi gashi ko baiyi gashi ba.

Idan aka sameshi araye, za'a yankashi.

Awajan malikiyyah : idan yayi gashi, ya halatta, idan baiyi gashi ba, bai halatta aci ba.

Awajan Abu Hanifa : baya halatta aci harsai an tsarkake shi bayan fitowarsa.

Saidai Wasu malamai Sun karhanta cin naman jaririn dabba ta fuskar lafiya.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*

KARKA MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.


Share:

MENENE HUKUNCIN CINYE NAMAN LAYYA DUKA, KO SADAKA DASHI GABA DAYA?

*MENENE HUKUNCIN CINYE NAMAN LAYYA DUKA, KO SADAKA DASHI GABA DAYA?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Nassoshi Na shari'a sunyi nuni akan wajabcin yin sadaka da Wani abu na naman layyah, koda kadanne, Allah madaukakin sarki yace:

( Kuci daka naman layyarku, ku ciyar da Talakan daya kame bai roqa ba, da talakan daya roqa saboda buqata, saboda haka Allah ya Yassare muku ita danku zama masu godiya) Suraul Hajji aya ta (36).

Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Kuci naman layya, ku ajiye, kuyi sadaka) *Muslim (1971).*

Malaman da Sukace yin sadaka da Naman layya wajibine sune: *Shafi'iyyah da Hanabila,* Itace sahihiyar Magana Azahirin nassosin shari'a.

Wajibine sadaka da wani abu na naman wanda sunan sadaka zai gaskatu akansa, domin manufa shine yalwatawa miskinai,

Abisa Wannan idan mutum ya cinye naman layyar sa, duka wajibine ya siya yayi sadakar,

*Rauzatul dhalibeen da Umdatul mufteen (3/223).*

Kamar yanda Marudy ya fada acikin *"Al'insaaf (6/491)*.

Kamar yanda Buhty yafada acikin *kashshaful Qina'i (7/444).*

Kamar Yanda Shaik Usaimeen ya bayyana acikin *Maj-mu'u fatawa dinsa (25/132)*

Malamai Sunyi Sabani akan wajabcin cin wani abu daka cikin Naman layya,

Jamhur din malamai suna ganin cin wani Abu na naman layya mustahabbine, ba dole bane, wannan shine fatawar Manyan Mazhabobinnan guda hudu.

Wasu sun tafi akan wajabcin cin wani Abu daka cikin naman layya koda kadanne, saboda zahirin nassosin shari'a da sukai Umarni akai.

Nawawi yace:Cin naman layya mustahabbine ba dole bane, shine mazhabar mu da Malamai gaba daya, sai Abunda aka hakaito daka wasu magabata na wajabcin cin naman, saboda zahirin hadisin dayai Umarni aci wani abu daka layya, da fadin Allah madaukakin Sarki ( Kuci daka naman layya) Jamhur din malamai sun dora wannan umarni akan halacci da Mustahabbanci,

*Sharhin Sahihu Muslim (13/131).*

Ibnu qudama yace: da Mutum zaiyi sadaka da naman layya gaba daya, ko mafi yawan naman, ya halatta.

*Al-mugni (13/380)*.

Idan ka yanka raguna da yawa, ko wanne saika debi wani abu daka namansa kayi Sadaka dashi.

da Zaka yanka raguna goma ko akuyoyi ko tumaki, ko wanne daka cikinsu saika debi namansa kayi Sadaka dashi, mustahabbine kowacce dabba kaci wani Abu na naman dukkan dabbobin daka yanka.

Domin kowacce layya cin gashin kanta take..

Shi yasa da Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya soke abun hadayarsa saiyai umarni a debo masa wani kaso daka naman kowacce raquma.

Jabir dan Abdullahi Allah ya qara musu yarda yace: Sai muka nufi Abbatuwa Annabi ya Soke raquma talatin da Uku da hannunsa, sai ya bawa Aliyu ya yanka Abunda yai Saura.

Sannan yai Umarni akawo masa daka naman kowacce sai aka sanya atukunya aka dafa masa yaci namansu, yasha romonsu.

*Mualim (1218).*

Wannan yana nuna kowacce dabbar layya da'aka yanka tana da hukunci nata ita kadai.

saboda hakane yai Umarni akawo masa wani Abu daka kowacce taguwa.

Nawawi yace: acikin wannan akwai mustahabbancin cin hadayar nafila, da layyya.

Malamai Sukace: cin naman kowacce dabba daka yanka sunnah ne, cin yanka daya na kowacce dabba akwai wadatarwa, ka sanya atukunya don kowacce ya zama akwai romon nata naman.

*Sharhin Muslim (8/192).*

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*


Share:

ME AKE FADA YAYIN YANKA DABBAR LAYYA?

*ME AKE FADA YAYIN YANKA LAYYA?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Wanda zai yanka layya sunnah yayin yanka layyar shine yace; *Bismillahi, Wallahu Akbar, Allahumma haza minka walaka, Haza Anniy,* Idan Wani zaka yankawa layyar sai kace ( *Haza An fulan,* ka Ambaci Sunansa).

*(Allahumma Taqabbal Min Fulan, Wa Ãli fulan,)* saika Ambaci Sunansa.

Abunda yake dole, shine *Bismillah* Abunda ya qaru akai sunnah ne, ba dole bane.

*Bukhari ya ruwaito hadisi (5565) da Muslim (1966)* Daka Anas Allah ya qara masa yarda yace: Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yayi layya da raguna guda biyu kosassu, ya Ambaci Sunan Allah, yai kabbara ya yanka su).

Kamar yanda *Muslim ya ruwaito (1967)* irinsa daka Aisha Allah yaqara mata yarda.

Yasa ta kawo masa wuqar dazai yanka ragunan layyarsa sai yace: *( Allahumma Taqabbal Min muhammad Wa Ãli muhammad Wa min Ummati Muhammad)*

Turmuzi ya ruwaito hadisi (1521) daka jabir bin Abdullahi Allah yaqara yarda dashi yace: ( Na halarci layyar Annabi Sallallahu Alaihi wasallam a wajan sallar idi, lokacinda ya gama khudubarsa sai ya sauko daka minbarinsa aka kawo masa rago ya yanka shi da hannunsa, yace; *( Bismillahi, Wallahu Akbar, Haza Anniy, wa Amman lam yuzahhi min Ummaty,)*

Albani ya Inganta shi acikin Sahihu Turmuzi.

Qarin ( Allahumma haza minka walaka) Yazo awasu qarin ruwayoyi.

Duba *Irwa'ul galeel (1138) (1152).*

Allahumma Haza minka walaka, Ai wannan layyar arziqinkace ya Allah, zumuncine daka gareka izuwa gareni, walaka) dankai kadai nayita.

Duba *Sharhin Mumti'i (7/492)*

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*


Share:

SHIN DOLENE SAI MUSULMI ZAI YANKA DABBAR LAYYA?

*SHIN DOLENE SAI MUSULMI ZAI YANKA DABBAR LAYYA?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Sharadine a yanka layya da niyyar layyace za'ayi,  idan mutum ya yanka da niyyar yaci nama layyar batai ba.

Imamun Nawawi Rahimahullahu yace: Niyya sharadice ta Ingantuwar layya.

*Al-Maj-mu'u (8/380).*

Bai Halatta ka wakilta kirista kafiri wajan yanka layya ba, tare da cewa yankan kirista halal ne aci, saidai saboda yankan layya ibadace, bai halatta ka wakilta kirista ba.

Saboda kirista bashi daka cikin Masu wannan ibadar da neman kusancin Allah, domin kafirine, ba'a karbar ibadarsa, idan bata halatta akaran kansa ba, bai halatta yayiwa wani ba,

Amma Da Mutum zai wakilta kirista ya yanka masa layya dan yaci nama babu laifi.

*Sharhin Mumti'i na Shaiek Usaimeen (7/494).*

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*

Share:

Tuesday, 29 August 2017

SHIN YA HALATTA MUTUM YACI BASHI DAN YIN LAYYA?

*SHIN YA HALATTA MUTUM YACI BASHI DAN YIN LAYYA?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Layya ba Dole bace, Saboda ba'a ruwaito dalilai na Shari'a akan Wajabcinta ba, Masu cewa wajibice dalilansu raunane.

*Maj-mu'u fatawa bin baaz (18/36)*

Wadanda sukace: wajibice sun shardanta sai in kana da wadata

*Duba Hashiyatu Ibnu Abideen (9/452).*

Da Masu cewa dolece da Masu cewa sunnah ce, Ba wajibi bane karbar bashi dan siyan Abun layya, domin ba dole bace.

Anso Mutum ya nemi Bashin ya sai Abun layya idan yana da tabbas din zai iya biya, kamar Ma'aikaci sai ya karbi bashin Abun layya kafin ya karbi Albashinsa Aqarshen wata. idan yasan yanada Taurin bashi ko bashi da halin biya, Abunda yafi masa kada yaci bashin.

Domin zaka shagaltar da kanka cikin nauyin bashi akan abunda ba tilas ne ba.

Shaikul Islam Ibnu taimiyyah rahimahullahu yace: Idan kana da Halin biyan bashi saika nemi bashi dan kayi layya, Wannan Abune mai kyau, Amma ba dolene ka aikata hakan ba.

*Maj-mu'u fatawa (26/305).*

Tareda cewa yana cikin masu cewa wajibice.

Ala Ayyi halin dai idan kanada halin da zaka iya biyan bashi ya halatta ka nema dan kayi layya.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.


Share:

MENENE AKA HANA GA WANDA YAKE SON YIN LAYYA YA AIKATA?

*MENENE AKA HANA WANDA YAKE SAN YIN LAYYA YA AIKATA?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Idan Watan zul-hijjah ya kama, haramunne akan Namiji ko mace da ya kesan yin layya, ya yanke farcensa ko sumarsa.

Saboda hadisin da *Muslim ya ruwaito (1977)* daka Ummu Salama Allah yaqara mata yarda daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Idan Kuka ga Watan zul-hijja, kuma dayanku yana san Yin layya, ya kame  daka yanke farcensa ko Aske gashinsa)

Imamun Nawawi Rahimahullahu yace: Malamai Sunyi Sabani akan wanda watan zul-hijjah ya kama yana san yin layya.

*Sa'eed da Ibnu Musayyib da Rabi'ah da Ahmad da Ishaq da Dauda da Wasu MalamanvSahafi'iyyah* sukace: Haramunne mutum yacire komai na gashinsa, da farcensa, harsai yayi layya, shafi'i yace: Makaruhine karhanci na Kamala, ba Haramun bane.

Sharhin Muslim.

Mace ya Halatta ta Tsefe gashin kanta, ta Wankeshi, Saidai kada ta Tajeshi, Abunda ya zuba na gashinta yayin tsefewa da Wankewa Baya cutarwa akan layyarta.

*Fatawa bin Baaz (18/47).*

Ya Halatta Wanda yake da Niyyar layya ya gyara tufafinsa ko yasa turare ko yin jima'i.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.



Share:

SHIN YA HALATTA YIWA WANDA YA MUTU LAYYA?

*SHIN YA HALATTA YIWA WANDA YA MUTU LAYYA?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Asali layya an shar'anta ta ga wanda yake rayayye, Kamar yanda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam da Shabbansa suka kasance sunaiwa kansu da iyalansu layya, abunda wasu suke dauka na kebance layya ga wanda ya mutu bashi da Asali.

Yiwa Wadanda ya Mutu layya kashi uku ne:-

Nafarko: Yiwa mamaci layya amma yabi cikin rayayyu, mislai, Ka niyyaci layya ga kanka da iyalanka, rayayyu da Matattu.

Wannan ya halatta, asalin Wannan shine layyar Annabi Sallallahu Alaihi wasallam da iyalan gidansa daka cikinsu akwai wadanda suka mutu

Na Biyu: Yiwa mamaci Layya saboda yabar wasiyyar Ayi masa, za'ai masa don zartar da wasiyyar sa, ( Wannan dolene) saidai idan mutum yakasa, Saboda fadin Allah madaukakin Sarki ( Duk Wanda ya canja Abunda mamaci yai wasici dashi na Alkhairi, zunubin yana kan wanda ya canja wasiyyar, Lallai Allah mai jine mai ganine)

Na Uku: Yiwa mamaci layya dan kyautatawa, kamar yiwa iyaye layyah, Wannan ya halatta.

Malaman Hanabila Sukace: ladan zai isa garesu kuma zasu Amfana dashi, qiyasi akan yi musu sadaka.

Saidai Bama ganin kebance yiwa mamaci layya yana daka cikin Sunnah.

Domin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam bai yiwa kowa layya daka cikin wadanda suka mutu ba a kebance, baiyiwa Ammunsa Hamza layya ba, wanda yana cikin manyan Makusantansa.

Baiyiwa 'ya'yansa wadanda suka mutu a rayuwarsaba, baiyiwa Matarsa khadija ba, tana daka cikin matan da yafi so, kuma ba'a ruwaito daka Sahabbansa ba.

Yana daka cikin Kus-kure abunda wasu suke aikatawa, yiwa mamaci layya farkon shekarar da ya mutu, suna kiranta da layyar rami) suna qudurce babu wanda ya halatta yai tarayya dashi acikin ladanta, ko suyiwa mamatansu layya saboda wasiyyarsu, amma basa yiwa kansu da iyalansu layya,

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.


Share:

Monday, 28 August 2017

WADANNE SHEKARUNE SUKE WAJIBI A KULA DASU YAYIN LAYYA?

*WADANNE SHEKARUNE SUKE WAJIBI A KULA DASU YAYIN LAYYA?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Malamai sun hadu akan akwai wasu shekaru da shari'a ta iyakance wajan layya, bai halatta yin layya da dabbar data gaza daka suba.

Duk wanda ya yanka dabbar data gaza da shekarun layyarsa bata yiba.

An ruwaito hadisai dasuke nuni akan haka, Duba *Al-majmu'u na Nawawi*

*Bukhari ya ruwaito (5556) da muslim (1961)* daka bara'u bin Azib, yace wani dan'uwansa da'ake cewa abu burda ya tambayi manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, yayi layya da akuyar da bata cika shekara guda ba? Annabi yace: jeka kayi layya da ita,  Amma daka kai babu wanda ya halatta yayi da akuyar da batakai shekara daya ba,

*Musilm ya ruwaito hadisi (1963)* daka jabir Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( kada ku yanka dabbar layya sai wacce ta cika shekara, saidai idan kunsamu kanku cikin qunci saiku yanka wacce bata kai shekaraba daka cikin tumaki,

Nawawi acikin Sharhin Muslim yace: Malamai Sukace: *"Musannah"* itace wacce ta tafi shekara ta biyu daka kowanne dangin dabbobin ni'ima *raqumi ko saniya, awaki da tumaki* zuwa sama, Wannan bayanine qarara akan bai halatta yanka wacce bata shekaraba inba Daka dangin tumaki ba, a kowanne hali.

*Alhafiz acikin Talkees (4/285)* yace: Zahirin hadisin ya nuna baya halatta yanka tunkiya ko rago wanda bai shekara ba, sai idan baka da halin siyan wanda yacika shekara ya tafi ta biyu, ijma'i abisa sabani, wajibine ayi tawilinsa, ya dauki abunda yafi falala, qaddarawarsa shine, Kada ku yanka dabba sai wacce ta cika shekara guda.

Haka Nawawi yace: acikin sharhin Muslim, da Aunul Ma'abuud.

Yazo acikin *Mausu'ah fiqhiyyah (5/83)* wajan Anbaton Sharadin layya.

Dabba ta kai shekarun layya, ta zama *"saniyyah"* raqumi ko saniya ko akuya *(jaz'ah)* ko wacce take sama da ita daka tumaki, bai halatta yin layya da dabbar da batakai *"saniyyah"* ba, Sai cikin tumaki, ko abunda bai kai *jaz'ah* cikin tumaki ba....

Wannan Sharadin An hadu akansa tsakanin malamai Saidai sunyi sabani akan fassarar *Saniyyah da Jaz'ah*.

Kamar yanda ibnu Abdul barri ya fada acikin *tarteebul Tamheed (10/267)*

Kamar yanda nawawi yace: acikin *Al-majmu'u (8/366).*

*Jaz'ah* a dangin tumaki, itace wacce ta cika wata shida awajan ```Hanafiyyah da Hanabila, a wajan Malikiyyah da shafi'iyyah itace: Wacce ta cika shekara.

Al-Musinnah: Daka akuyoyi itace: Wacce ta cika shekara daya,a wajan Malikiyyah da Hanafiyyah da Hanabila, Awajan shafi'iyya kua itace: wacce ta cika shekara biyu```

*Musinnah daka Shanu*: Itace wacce ta cika (shekara biyu) awajan *Hanafiyyah da Shafi'iyya da Hanabila*, Awajan malikiyyah itace: Wacce ta cika shekara uku.

*Musinnah cikin Raquma* itace: Wacce ta cika shekara biyar, awajan Hanafiyyah da Malikiyyah da Shafi'iyyaj da Hanabila.

Duba:- *Bada'i'il Sana'i'i (5/70) da Baharul ra'iq (8/202) da Attaaju wal-ikleel (4/363) da Sharhin Muktasarul khaleel (3/34) da Maj-mu'u (8/365) da Al-Mugny (13/368).*

Yazo afatawa lajnatul da'imah (11/377), Sukace:.

Dalilai na Shari'a Sun nuna ya halatta yin layya da, ( Tunkiya ko ragon da ya kai wata shida) akuya ko taure wacce ta cika shekara guda, Saniya ( Wacce ta cika shekara biyu) raqumi wanda ya cika (shekara biyar) Abunda yake qasa da Wadannan baya halatta ayi hadaya ko layya dashi, domin Dalilai na Qur'ani da Sunnah sahinsu yana fassara sashi.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.



Share:

SHIN DABBA DAYA TA ISARWA MUTUM DA IYALANSA?

*SHIN DABBA DAYA TA ISARWA MUTUM DA IYALANSA?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Dabba guda daya ta isarwa mutum da iyalansa da wanda yaso  ya sanyashi daka cikin musulmi.

Saboda hadisin Aisha Allah yaqara mata yarda tace :an kawowa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam rago mai qaho, sai yace da ita, bani wuqa, saita kawo masa wuqa, saiya karbi wuqar ya kwantar da ragon sai ya yankashi, sai yace: Da sunan Allah, ya Allah ka karbawa muhammad, da iyalan gidan muhammad, da Al'ummar muhammad, Sannan yai layya dashi.

*Muslim*.

Daka Abu Ayyubal Ansary Allah yaqara masa yarda yace: Mutum azamanin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yana yin layya da Akuya ga kansa da iyalansa, suci naman su ciyar.

*Ibnu Majah da Turmuzi, Albani ya Ingantashi acikin Sahihu turmuzi (1216).*

Idan mutum yayi layya da tunkiya ko akuya ga kansa da iyalan gidansa, ta isarwa duk wanda ya sanya acikin niyyar yankan layyar cikin iyalansa wanda yake raye da Wanda ya Mutu,

Idan bai niyyaci komai ba, ya gamesu koya kebance, duk wanda yake ahlinsane ya shiga, a al'ada ko a luggah.

A al'ada ahlin gida sune matayen mutum da 'ya'yansa da 'yan'uwansa.

A lugga kuma dukkan wani makusancinsa cikin zurriyarsa da zurriyar babansa da zurriyar kakansa, da zurriyar kakan babansa.

Akuya ko tunkiya bata isarwa mutum biyu su hadu su saya suyi layya, saboda rashin ruwaito hakan daka Alqur'ani da Sunnah.

Kamar yanda bai halatta mutum takwas su hadu akan raqumi ko saniya ba,

Amma ya halatta mutum bakwai su hadu akan raqumi ko Saniya.

Amma Tarayya wajan lada wannan ba'a iya kanceba.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.


Share:

Sunday, 27 August 2017

MENENE SHARUDDAN YIN LAYYA?

*MENENE SHARUDDAN YIN LAYYA?*

الحمد لله، سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

*AMSA:* Sharuddan layya guda shi dane.

Nafarko: Abunda za'ayi layyar dashi ya zama yana daka cikin dangin dabbobin ni'ima, Sune : *raqumi da saniya da awaki, tunkiya da akuya,*

Saboda fadin Allah madaukakin Sarki :

Kowacce Al'umma Mun sanya mata Abun yanka dansu Ambaci Sunan Allah Abisa Abunda ya Azurtasu dashi na dabbobin Ni'ima. *Suratul Hajji aya ta (43).*

Na Biyu: Abun layya ya zama yakai shekarun da aka iyakance ashari'a, ta kasance ta cika shekara daya idan akuyace ko taure, ko tacika shekara biyu idan tunkiyace ko rago, saboda fadin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam .

( Kada kuyanka layya sai wacce ta cika shekara saidai idan kunsamu quncin tattalin arziki saiku yanka jaz'ah daka jinsin tumaki.

*Muslim.*

Idan raqumine wanda ya cika shekara biyar zuwa sama.

Saniya wacce ta cika shekara biyu zuwa sama.

Tumaki ko akuyoyi wanda ya cika shekara guda.

Sharadi Na biyu dabbar layya ta Kubuta daka Aibuka wanda suke hana ayi layya da ita, guda hudune ga Sunan :

1- Harara garke wacce idonta daya yake akwai matsala, ko wacce idonta zai fari fat wanda ke nuna makanta qarara atare da ita.

2- Rashin lafiya bayyananniya, kamar zazzabi, wanda yake hana dabba kiwo, ko rauni qarara wanda yake lalata namanta, ko wanda yake da tasiri a lafiyarta, ko doguwar rashin lafiya da ta dade tanayi wanda yake mata tasiri a lafiyarta.

3- Gurguntaka mabaiyyaniya,

4- Wacce bata da Mai.

Wadannan Aibuka guda hudu sune suke hana ayi layya da dabbar da take da daya daka cikinsu.

Akwai wasu wadanda suke kamarsu koma suka fisu tsanani, layya bata halatta dasu ;

1- Makauniya wacce bata gani sam.

2-Wacce aka bata magani takecin Abunci sama da ikonta hartai qiba,

2-Wacce bata iya haihuwa da kanta.

4- Wacce ta fado daka saman wani abu ta samu illah,

5- Wacce bata iya tafiya, saboda cuta.

6- Wacce kafarta ta gaba ta guntule, ko ta baya.

Idan ka hada wadannan aibuka da guda hudun da suka gabata zakaga aibukan da suke hana layya da dabba sunkai guda goma.

Hakanan daka cikin sharuddan layya ta zama dabba mallakar mai layyace, ko kuma anyi masa izini yayi layya da ita,

Layya bata halatta da Abunda mutum bai mallakaba, kamar dabbar da akayi fashinta ko qwacenta, ko wacce aka sato, ko wacce akai qarya aka sameta, ko wacce akaiwa wani kirari na qarya ya bayar da ita, da maka-mantansu, domin bai halatta neman kusanci zuwaga Allah da sabo ba,

Layyar wanda aka baiwa kula da maraya tayi, idan yayita da dukiyar marayan, idan Al'ada ta zamto haka, kuma zuciyar marayan zata karaya idan ba'ayi layyar ba.

Haka layya ta hallata idan aka baiwa mutum wakilci, da dukiyar wakilin da izininsa,

Sharadi Na biyar : Kada Abun layya ya zama ya ta'allaqane da haqqin wani, layya bata halatta ga wanda akebi bashi, ya hana bashin yayi layya

Na Shida : Dole mai layya yayi layya a lokacin da aka iyakance, shine bayan sallar idi izuwa faduwar ranar uku ga Sallah.

Wanda ya yanka layyarsa kafin gama sallar idi, ko bayan faduwar ranar uku ga sallah, bashi da layya.

Amma Idan Wani uzurine yasa Mutum bai Samu damar yanka dabbar layyar saba har bayan faduwar uku ga sallah, Kamar wanda dabbarsa ta gudu batare da sakacinsa ba, bai sameta ba har bayan uku ga sallah,  ko wanda ya baiwa wani wakilcin yanka masa ya manta, babu laifi da wannan dan lokacin yin layyar ya wuce zaka yanka,

Qiyasi akan wanda yai bacci baiyi sallah ba koya manta Sallar, zai sallaceta idan yafarka ko ya tuna.

Ya Halatta yanka dabbar layyar cikin dare ko rana, yankawa da rana shine yafi, da kuma ranar idi bayan an sakko daka idin shine yafi falala..

Saboda gaggawa wajan aikata Alkairi.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*

KU KARANTA:- MECECE LAYYA SHIN WAJIBICE KO SUNNAH ??

Kuci gaba da kasancewa da wannan shafin www.duniyarfatawa.cf

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.


Share:

Archive

Unordered List

Support