October 2017 ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday, 28 October 2017

MUYI SALATI GA ANNABI SAW (DARAJOJI 40) Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Mal.Aminu Ibrahim Daurawa

MUYI SALATI GA ANNABI SAW (DARAJOJI 40)

Yin salati ga Annabi saw, yana jawo wa mai yi darajoji 40
Kamar yadda Ibnul Qayyim ya kawo a cikin littafin sa, da ya wallafa akan salati ga Annabi saw, mai suna Jala'ul afham.
Na 1, Yin salati Bin umarnin Allah ne.
Na 2 , Koyi da Allah swt, shima yana yiwa Annabi saw. salati
Na 3 , koyi da Mala'iku, suma suna salati ga Annabi saw .
Na 4 , Samun lada goma.
Na 5 , Samun daraja goma.
Na 6 , yafe laifi goma.
Na 7 , Amsa adduar wanda ya fara da salati.
Na 8 , samun ceton Annabi saw .
Na 9 , Gafarta zunubin mai yawan salati .
Na 10 , Allah zai yaye, masa abinda yake damunsa.
Na 11 , Zaiyi kusa da Annabi saw. Ranar Alkiyama
Na 12 , Wanda yayi salati ya sami ladan Sadaka.
Na 13 Salati sababi ne na biyan bukata.
Na 14 , Allah taala Zaiyi salati ga wanda ya yiwa Annabi saw, salati.
Na 15 ,Salati ga Annabi saw, yana tsarkake mai yawan yinsa.
Na 16 , Zai sami bushara da Aljannah.
Na 17 Tsira daga tsananin kiyama
Na 18 yiwa Annabi saw salati yana tuno maka abinda ka manta
Na 19 , salati yana cikin hakkokin Annabi saw.
Na 20 , Salati yana kamsasa majalisi.
Na 21, Salati yana korar talauci.
Na 22 Salati ga Annabi saw yana kore rowa .
Na 23 Bazaa durmaza hancin mai salati ba.
Na 24 Mai salati ya kama hanyar Aljannah.
Na 25 Idan akayi taro aka tashi babu salati, zaayi warin mushen jiki.
Na 26 , A fara magana da yabo ga Allah da salati ga Annabi saw.
Na 27 samun haske akan siradi ranar Alkiyama
Na 28 fita daga Jafa'i, na laifi, idan anyi salati.
Na 29 Mai yawan salati ga Annabi saw, yana samun yabo da girma.
Na 30 samun Rahma
Na 31 soyayyar Annabi saw, ga mai salati
Na 32 Annabi saw ya Nuna yana son mai masa salati.
Na 33 Samun shiriya da rayuwar zuciya .
Na 34 Duk mai yiwa Annabi saw salati, ana gayawa Annabi saw, sunan sa.
Na 35 Tabbata akan siradi ranar Alkiyama
Na 36 Yiwa Annabi saw, salati, rokon Allah, kuma ibada ne.
Na 37 Salati ga Annabi saw godiya ne ga Allah.
Na 38 salati ga Annabi saw zakka ne da tsarki g
Share:

MECECE DUNIYA?!

MECECE DUNIYA?
*******************
'Yan uwa wannan rayuwar ta duniya fa rudani ce da wasa, da yaudara mai dauke hankali.. Shaitan yana amfani da ababen cikinta wajen yaudarar da zukata da shagaltar da tunanin Bil Adama.

Rayuwar nan ta duniya Mafarki ne wanda ke cike da alkawura marassa tushe, Marassa makama.. Wanda yayi sammakon farkawa daga wannan mafarkin shine wanda ya rabauta.

Ita rayuwar duniya tamkar cin kasuwa ne. Lokutan da Ubangiji ya baka awannan rayuwar sune tamkar kudaden cin kasuwar.. Babu wanda ya rabauta sai wanda yayi amfani da kudinsa wajen sayen abubuwan da zasu amfaneshi idan ya koma gidansa na ainahi..

Wato yayi amfani da lokutansa wajen neman ilimin addini da kuma aiki dashi, Ko taimakon addini da jikinsa da Aljihunsa da basirarsa da dukiyarsa..

Yayi amfani da ranaikunsa da dararensa wajen nafilfili da Zikirin Allah da Karatun Alqur'ani da kira zuwa ga tafarkin Allah..

Amma wanda yayi amfani da lokutansa wajen Kallon abinda ya haramta, rawa da waqa, zaman gulmace-gulmace, cin mutuncin Musulmai, tafiya wajen sa'bon Allah, rushe tarbiyyar al'ummah, to wadannan sune asararru, sune wadanda basu ci ribar kasuwancinsu ba..

Ya kai 'Dan uwa!! Ko kasan cewa duk abinda kake gadara dashi awannan duniyar (Kudi, Mulki, daukaka, dukiya) sai da wasu suka sameshi kafinka?.

Kuma yanzu dolensu sun tafi sun barshi?. Suna Qarkashin Qasa suna girbar abinda suka shuka na alkhairi ko sharri??.

Yadda yanzu basu nan sai dai labarinsu, mafiya yawansu ma ko labarin nasu babu....  To hakanan kaima gobe sai dai labarinka... Jibi kuma ko labarin naka ma babu!!!.

Lahira ita ce gidanka na ainahi.. Gidanka matabbaci.. Yi Qokari ka tanadar ma kanka guzuri mai yawa ta hanyar Ibadah mafi saurin tseratarwa daga wuta. Wato Zikirin Allah safiya da maraice..

Yima guzurinka Stamp na Ikhlasi.. Kuma ka zubar da Miyagun kaya daga cikin guzurinka ta hanyar Istighfari..

Ka Qamsasa guzirin naka, ka Qara masa tsada ta hanyat Salati da Tasleemi ga Annabinka mafi daraja.. Alfaharin Banu Hashim, Farin cikin Halittu, Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata agareshi da iyalan gidansa tsarkaka da dukkan Sahabbansa yardaddu da mabiyansa har zuwa ranar sakamako. Ameeen.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (24/10/2017 05/02/1439).


Share:

SU WAYE FIQAHA'US SAHABAH?

SU WAYE FIQAHA'US SAHABAH?
********************************
Wasu Sahabbai ne manya wadanda suka shahara a fagen ilimi da fahimtar addini. Kuma mafiya yawansu sun dauki zamani mai tsawo suna tare da Manzon Allah (saww).

Masu kokari ne wajen Ilmantarwa da karantarwa tun azamanin Manzon Allah (saww) da kuma bayansa. Wadanda daga irin fatawoyinsu ne aka gina fahimtoci na manyan Mazhabobin nan na Maluman Fiqhu.

Mafiya shahara daga cikin Fiqaha'us Sahabah sun hada da :

- Sayyiduna Abubakrin bn  Abi Quhafah (Assiddeeq).

- Sayyiduna Umar bn Al-Khattab (Al Faruq).

- Sayyiduna Uthman bn Affan (Dhun Nurayn).

- Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib (Abul Hasanaini).

- Abdullahi bn Mas'ud.
- Zaidu bn Thabit.
- Abu Musal Ash'ariy.
- Mu'az bn Jabal.
- Ubayyu bn Ka'ab.
- Abud Darda'i.

Sai kuma Ummul Mumineen,  Nana A'ishah bintu Abibakrin  (Allah shi yarda dasu baki dayansu).

Sannan acikin kashi na biyu kuma akwai wadanda ake kira "AL- ABADALAH". Wato dukkansu sunayensu Abdullahi ne. Kuma dukkansu 'ya'yan Sahabbai ne kuma sun riski lokacin rayuwar Manzon Allah (saww). Kuma sun tattaro Ilimai masu yawa wadanda kusan sun shiga kowanne fanni na ilimin addini. Gasu nan kamar haka :

- Abdullahi bn Abbas.
- Abdullahi bn Umar.
- Abdullahi bn Zubayr bn Awwam.
- Abdullahi bn Amru bn Al-As.

Allah shi yarda dasu baki dayansu.

Dukkansu baki daya kowanne yana da manyan abubuwan da ya kebantu dasu na falala da fifiko acikin sauran Sahabbai.

Muhammad 'dan Sahlu dan Abu Khaysamah ya karbo daga Babansa yana cewa :

"Wadanda suka kasance suna bayar da fatawa azamanin Manzon Allah (saww) mutum uku ne daga Muhajirun, uku kuma daga mutanen Madeenah.

Umar da Uthman da Aliyu da Ubayyu bn Ka'ab  da Mu'azu bn Jabal da Zaidu bn Thabit. Shi kuwa Abdullahi bn Abbas ya kasance idan an tambayeshi game da wani abu, in dai babu acikkn littafin Allah da Sunnar Annabinsa (saww) to yana yin furuci ne da Qaulin Abubakar (ra) idan kuma babu to yakan yi fatawa da maganar Umar (Allah shi yarda dasu baki dayansu. Ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (17/10/2017 27-01-1439).


Share:

NA SAKI MATATA SAU BIYU, SAI NA SAKE SAKINTA BAYAN DAURA SABON AURE, KO AKWAI DAMAR KOME?? Dr.jamilu yusuf zarewa



*NA SAKI MATATA SAU BIYU, SAI NA SAKE SAKINTA BAYAN DAURA  SABON AURE, KO AKWAI DAMAR KOME ?*


*Tambaya*

Assalamu alaikum don Allah malam ka warware mana wannan matsala, yanzu haka muke cikinta, mutum ne ya sake matarsa shika Daya 1, ya koma da ita bayan wasu shekaru ya sake mata shika daya, har idarta ya kare ya sake biyan sadaki ya dawo da ita yanzu kuma sun sake rabuwa shika daya 1, kuma suna son junansu akwai aure a tsakaninsu ko sai ta sake auren wani ? shikan bayan da ya mata har idarta ya kare aka sake daura aure a matsayin shika nawa ne yake kanta nagode Allah ya kara imani da basira sai naji daga gareka


*Amsa*
Wa'alaykumussalam

To dan'uwa idan abin haka yake kamar yadda ka siffanta, to babu damar kome, sai in  ta auri wani mijin na daban, saboda igiyoyin da suke tsakaninku sun yanke gaba dayansu .
Auren da kuka sake, ba zai goge sakin da ka yi a baya ba, da ace ta auri wani bayan saki biyun da ka mata, kafin ka sake auranta, da ba'a kirga da saki biyun baya ba, a daya daga cikin maganganun malamai, amma tun da ba ta auri wani  ba, ya wajaba ku hakurewa juna .

Don neman Karin bayani duba : Al-mugni na Ibnu-Khudaamah 7\388 .

Allah ne mafi sani .

*Dr, Jamilu Zarewa*

3\5\2015

Ga dukkan mai son shiga ​ZAUREN FIQHUS SUNNAH​ sai ya yi saving wannan number +2348122248585  sannan ya tura da sunansa da adireshinsa ta whatApp. Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba.

ADMINS
Share:

Monday, 23 October 2017

Audio:-Muhadara:Manzon Allah (S A W) Rahma ne - Sheikh ahmed tijjani yusuf guruntum


MUHADARA MUHADARA

Daga:-

Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum 


DOMIN SAUKO DA WANNAN AUDIO SAIKU SHIGA WANNAN BLUE RUBUTU DAKE KASA.


Ayi saurare lafiya

Share:

HUKUNCIN KALLON WASAN KWAIKWAYON ANNABAWA!!? Dr.jamilu yusuf zarewa

*HUKUNCIN KALLON  WASAN KWAIKWAYON ANNABAWA*


*Tambaya*


Assalamu Alaikum
Malam Don Allah Tambaya Na ke da shi Da Fatan Za'a  Fahimtar da ni. -wai Shin Kaset din da akeyi na Tarihin Annabawa Ya Halatta A Kalle shi ? Allah Ya Saka Da Alkhairi .



*Amsa*
Wa'alaykumussalam.

To dan'uwa  malamai da yawa sun haramta yin wasan kwaikwayon annabawa saboda dalilai kamar haka :

1. Hakan zai iya bude kofar da wasu masu kallon za su yi  isgilanci ko ba'a ga annabawan Allah, isgilanci ga annabawa kuma yana iya  fitar da mutum daga musulunci, kamar yadda aya ta : 65 a suratu Atttauba ta yi nuni zuwa hakan.

2. Wasu daga cikin masu shirya film din suna wuce gona-da-iri, kamar masu nuna annabi Isa a matsayin Allah, addinin musulunci kuma ya haramta duk abin da zai kai a riki wani annabi ko managarci a matsayin Allah.

3. Irin wadannan wasannin na kwaikwayo, suna ragewa annabawa matsayi, saboda masu film din suna cakuduwa da matan da ba muharramansu ba, wanda hakan kuma  ragewa annabawa kima ne.

4. Kasancewar hakan ya sabawa hikimar Allah ta sanya shaidanu ba sa iya kama da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi , kamar yadda ya zo a hadisi.

5. Kasancewar hakan zai jawo aki girmama annabawa, a kuma yi musu karya, domin wasu masu yin wadannan fina-finan mutanen banza ne, ka ga sai a dinga kallon annabawan da siffar wadannan.

Allah ne mafi sani.

*Dr Jamilu Zarewa*

13/6/2014

Ga dukkan mai son shiga ​ZAUREN FIQHUS SUNNAH​ sai ya yi saving wannan number +2348122248585  sannan ya tura da sunansa da adireshinsa ta whatApp. Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba.

ADMINS
Share:

HUKUNCIN AURE CIKIN AURE?? Dr.jamilu yusuf zarewa

*HUKUNCIN AURE CIKIN AURE*


*Tambaya*

Assalamu alaikum, mallam tambaya muke da ita. Mace ce aka aurar
tana ‘yar-shekara 14 ga wanda bata so, to sai
mijin yayi tafiya har tsawon wata hudu (4) To
sai matar tasa aka rubuta mata saki tace ya
saketa, bayan ya dawo yace bai saketa ba,
amma ba’a yarda ba.
Da ta kare idda tayi aure
da wani har suka haihu, daga baya kuma suka
rabu, kuma yanzu ta ga musifu suna ta
samunta, sai take tunanin ko wancan abin ne da
tayi. Tana neman fatawa, ina hukuncin ta, da
yaran data haifa da miji na biyu?


*Amsa*
Wa'alaykumussalam

Malam amsar wannan tamba yana da mutukar
wahala, saidai na nemi taimakon wasu daga
cikin malamaina, ga abin da na samo :

1. Abin da ta yi mummuna ne a shari’ar
musulunci saboda ta yi aure cikin aure.

2. Zaman da su ka yi da mijinta na biyu, a
matsayin mazinaciya take, saboda haka duk
kwanciyar da suka yi da wannan mijin na ta
zina ne.

3. Yaran da su ka Haifa da mijnta na biyu,
‘ya’yansa ne, tun da bai san abin da ya faru ba
a baya.

4. Har yanzu igiyar aurenta ba ta warware ba
tsakaninta da mijinta na farko, saboda haka har
yanzu ita matarsa ce saidai in ya sake ta.

5. Mijinta na farko, zai iya dawowa da ita, ba
tare da sake daura aure ba, saidai dole sai
bayan ta tuba, domin ita a matsayin
mazinaciyya take, kuma Allah ya hana auren
mazinaciya.

6. Ya wajaba a gare ta ta yawaita istigfari
saboda girman zunubin da ta aikata.

7. Zai yi kyau su je wajan Alkali wanda ya san

shari’ar musulunci, domin ya yi musu hukunci.

ALLAH NE MAFI SANI.

*Dr. Jamilu Zarewa*

20/11/2016
Share:

HUKUNCIN MATAR DA TA YI AURE KAFIN A SAKETA - Dr.jamilu yusuf zarewa

*HUKUNCIN MATAR DA TA YI AURE KAFIN A SAKETA*


*TAMBAYA :*

Assalamu alaikum Malam.  Mace ce aka aurar tana 'yar-shekara 14 ga wanda bata so, to sai mijin yayi tafiya har tsawon wata hudu (4) To sai matar tasa aka rubuta mata saki tace ya saketa, bayan ya dawo yace bai saketa ba, amma ba'a yarda ba. Da ta kare idda tayi aure da wani har suka haihu, daga baya kuma suka rabu, kuma yanzu ta ga musifu suna ta samunta, sai take tunanin ko wancan abin ne da tayi. Tana neman fatawa, ina hukuncin ta, da yaran data haifa da miji na biyu?


*AMSA:*
Wa alaikum assalam

 Malam amsar wannan tambaya yana da mutukar wahala, saidai na nemi taimakon wasu daga cikin malamaina, ga abin da na samo :

*1.* Abin da ta yi mummuna ne a shari'ar musulunci saboda ta yi aure cikin aure.

*2.* Zaman da su ka yi da mijinta na biyu, a matsayin mazinaciya take, saboda haka duk kwanciyar da suka yi da wannan mijin na ta zina ne.

*3.* Yaran da su ka Haifa da mijnta na biyu, 'ya'yansa ne, tun da bai san abin da ya faru ba a baya.

*4.* Har yanzu igiyar aurenta ba ta warware ba tsakaninta da mijinta na farko, saboda haka har yanzu ita matarsa ce saidai in ya sake ta.

*5.* Mijinta na farko, zai iya dawowa da ita, ba tare da sake daura aure ba, saidai dole sai bayan ta tuba, domin ita a matsayin mazinaciyya take, kuma Allah ya hana auren mazinaciya.

*6.* Ya wajaba a gare ta ta yawaita istigfari saboda girman zunubin da ta aikata.

*7.* Zai yi kyau su je wajan Alkali wanda ya san shari'ar musulunci, domin ya yi musu hukunci.
Allah ne mafi sani.

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
30/6/2014
Share:

TA YI AURE DA CIKIN-SHEGE?? Dr.jamilu yusuf zarewa

*TA YI AURE DA CIKIN-SHEGE??*

 *Tambaya:*

Assalamu alaikum. Malam Wata tayi cikin shege da wani mutum,sai ta nemi wani daban ya rufa mata asiri ya aureta.
Yanzu sunyi Auren,yaya hukuncin Auren a Shari'a yake???

 *Amsa*

Wa alaykum assalamu Zina sabon Allah ne da kuma yada fasadi a bayan qasa. Aure kuwa sunnar Manzon Allah ne, da samar da zuriya mai albarka. Kuma an kwadaitar da mu yin sa. Amma Mazhabar Malikiyya suna ganin matar da aka yi zinar da ita sai ta yi jini wanda ake kira Istibra’i, kafin a daura mata aure domin a raba maniyyin zinar da na aure. Kuma idan har an daura aure ba ta yi wannan jinin ba, to, za a raba wannan auren ko da sun haifi `ya`ya, domin suna ganin an daura auren ne a cikin idda, kuma Allah Ya hana daura aure a cikin idda. Saboda haka, a wurinsu, wannan auren batacce ne kuma rusasshe.
Amma Mazhabar Abu Hanifa da Imam Shafi`i suna ganin macen da ta yi zina, an so ta yi istibra’i kafin ta yi aure, amma idan har an daura auren ba ta yi istibra’i ba, auren yana nan daram, ba za a raba su ba. Kuma suka qara da cewa ko da tana da cikin zinar ne aka daura mata aure, to, auren yana nan. Sai dai Imam Abu Hanifa ya ce: mijin da ta aura, ba zai sadu da ita ba, har sai bayan ta haihu, ko da kuwa cikin zinar nasa ne ko na waninsa.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" Abu- dawud : 1847.
Don neman karin bayani duba : AL-MUDAWWANNAH aL-KUBRAH 2\173 da Al-mugni na Ibnu-Khudaamah 8/79.

A fahimtata, fatawar Malikiyya ta fi inganci kafin ayi auren, saboda fita daga sabanin malamai abin só ne, sannan kuma za'a kaucewa fadawa hadari, amma idan an riga an yi auren to fatawar Hanafiyya abar lura ce, saboda akwai bambanci tsakanin zina da aure, saidai ya wajaba şu nisanci saduwa, kafin ta haihu Saboda hadisin da ya gabata.

Allah ne mafi sani.

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
27/02/2016
Share:

IDAN SAKI YA FITO DAGA BAKI BA YA KOMAWA !! Dr.jamilu yusuf zarewa

*IDAN SAKI YA FITO DAGA BAKI BA YA KOMAWA !!*


*Tambaya*

Assalamu alaikum malam wata baiwar Allah ce suka sami sabani da mijinta sai yabita inda take aiki yaje yana nemanta sai tafadama wata agurin taje tacemai batanan sai mijin yace d yar sakon tace yasaketa saki uku kuma itama taji da kunnenta,sai daga baya yace shi be saketa b shine tace atambaya mata ta saku ko aurensu nanan tunda ba ita yafada ma ba.Nagode


*Amsa*
Wa alaikum assalam,

Ta saku mana tun da saki ba'a wasa da shi in har ya fito daga baki  ko da wasa ne ba ya komawa, musamman kuma wacce aka yiwa sakin ta ji da kunnanta, ai karya ta kare.
Inkarinsa ba zai yi amfani ba, tun da an tabbatar ya furta.

Don neman karin bayani duba: Zadul-ma'ad 5/204.

A mazhabarmu a Malikiyya ta saku saki uku, amma akwai malaman da suke ganin za'a bar shi a saki daya, tun da saki uku A kalma daya Bidi'a ne, kuma haka  ake hukuntawa a zamanin Annabi S.A.W. da zamanin Abubakar RA da wani bangare na zamanin Umar RA .
Kamar yadda hadisin Ibnu Abbas ya tabbatar da hakan

Allah ne mafi sani.

*Dr, Jamilu Zarewa*

16/09/2017
Share:

ANGO YA MUTU KAFIN AMARYA TA TARE, YAYA BATUN GADO DA TAKABA ? Dr.jamilu yusuf zarewa

*_ANGO YA MUTU KAFIN AMARYA TA TARE, YAYA BATUN GADO DA TAKABA ?_*


*_Tambaya_*


Assalam Alaikum, Dr. an daura auren wasu yau ba'a dauko amarya ba sai gobe, amma Allah yayi wa angon rasuwa..tambayata anan wai shin za tayi takaba? Kuma tanada gadonshi?


*_Amsa_*
Wa'alaykumussalam

To dan'uwa idan miji ya mutu bayan an daura aure kafin ya tare da amryarsa, ya wajaba amaryarsa ta yi masa takaba, kuma a bata gadonta cikakke, kamar yadda Annabi S.a.w. ya yi hukunci da hakan ga Barwa'u 'yar Washik lokacin da mijinta ya mutu kafin su tare a hadisi mai lamba ta: 1145, wanda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta shi .

Allah ne mafi sani.

*_Dr. Jamilu Yusuf Zarewa_*

1/05/2016

Ga dukkan mai son shiga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH* sai ya yi saving wannan number +2348122248585  sannan ya tura da sunansa da adireshinsa ta whatApp. Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba.
Share:

Thursday, 19 October 2017

RIGIJI GABJI! Ina Malikawan Nigeria! Toh yau dai ga Imamu Malik yayi gabas Dr Ahmad Gumi yayi kudu. !

DAGA MIMBARIN SALAFIYYAH NETWORK NIGERIA
!
LALLAI INDA MALIKIYYAR SUKE YI DA GASKE TOH DA KASHE DR AHMAD GUMI KAWAI ZA AYI DOGARO DA FATAWAR IMAMU MALIK DANGANE DA DUK WANDA YAYI MUSUN CEWA QUR'ANI BA MAGANAR ALLAH BANE INDAI HAR BAI TUBA YA JANYE KALMAR BA.
!
RIGIJI GABJI! Ina Malikawan Nigeria! Toh yau dai ga Imamu Malik yayi gabas Dr Ahmad Gumi yayi kudu.
!
Wannan ke 'kara tabbatar da cewa An shigo cikin rigar malikiyya ne kawai ana ta fesa ma al'umma gubar mu'utazilanci a Masallacin Sultan Bello Kaduna. Allah (T) ya ce AlQur'ani maganarshi ce Dr Ahmad Gumi kuma ya ce A'a halittar Allah ne. Lallai inda ace malikiyyan da ake yi na gaskiya ne toh da kashe Dr Ahmad Gumi kawai ya kamata ayi dogaro da wannan bayanin na Imamu Malik acikin wannan rubutun kamar haka:

قيدة الإمام مالك )رحمه الله( في القرآنذكر الإمام البخاري في )خلق أفعال العباد( عن مالك قوله"القرآن كلام الله"وذكر اللالكائي بسنده عن أبي محمد يحيى بن خلف المقري قال كنت عند مالك بن أنس سنة ثمان وستين فأتاه رجل فقال يا أبا عبد الله ما تقول فيمن يقول القرآن مخلوق قال "كافر زنديق اقتلوه"وذكر اللالكائي أيضا عن أبي الحسن بن العطار محمد بن محمد قال سمعت شريح بن النعمان يقول سالت عبد الله بن نافع وقلت له إن قبلنا من يقول القرآن مخلوق فاستعظم ذلك ولم يزل موجعا حزينا يسترجع قال عبد الله بن نافع قال مالك بن أنس من قال القرآن مخلوق يحبس حتى يعلم منه توبةوذكر ابن أبي حاتم بسنده عن ميمون بن يحيى البكري قال قال مالك بن أنس من قال القرآن مخلوق يستتاب فإن تاب وإلا ضربت عنقهوجاء في المدونة "قال ابن نمير: سمعت أبا مصعب يقول: سمعت مالكاً يقول: القرآن كلام الله غير مخلوق، قال أبو مصعب فمن شك أو وقف فهو كافر".وفي ترتيب المدارك للقاضي عياض" "قال ابن أبي أويس سمعت مالكا يقول: )القرآن كلام الله وكلام الله منه وليس من الله شيء مخلوق(
!
Fassara:
Imamul Bukhaariy ya ambaci maganar Maaliku cewa " Alƙur'aani maganar Allaah ne" (Khalƙu Af'aalil Ibaad)Kuma Allaalikaa'iy ma ya ambata daga Baban Muhammad Yahya ɗan Khalaf Almuƙ'riy yace: ina wajen Maaliku ɗan Anas a shekara ta ɗari da sittin da takwas,yayin da wani mutumi ya ce: Allaah gafarta baban Abdullaahi (Imamu Maalik) me zaka faɗi game da wanda yake cewa Alƙur'aani HALITTA ne? Sai yace:"KAAFIRINEZINDIƘI, KU KASHESHI"
!
Har ilaa yau Allaalikaa'iy ya saake ambata daga baban Alhasan ɗan Al-Atɗaar Muhammad ɗan Muhammad yace naji Shuraihu ɗan Annu'umaan yanacewa na tambayi Abdullaahi ɗan Naafi'u na ce dashi ansami daga cikin mutananmuwanda yake cewa ALƘUR'AANI HALITTA NE! sai hankalinshi ya tashi dajin haka, kuma bai gushe ba yana mai takaicin maganar da nuna damuwa matuƙa yana istirjaa'i (salati), Abdullaahi ɗan Naafi'u sai yace Maaliku ɗan Anas yace:DUK WANDA YACE ALƘUR'AANI HALITTANE za'a tsare shi har sai an tabbatar ya tuba daga shi (wannan muguwar aƙidar).
!
Ɗan Baban Haatimu ya ambaci magana ta hanyar Maimuun ɗan Yahaya al-Bakariy cewa Maaliku ɗan Anas yace: DUK WANDA YACE ALƘUR'AANI HALITTA NE, ZA'A NEMESHI DA YA TUBA, INYA TUBA SHIKENAN, IN KUWA YAƘI ASARE WUYANSA.Yazo a cikin Mudawwana (littafin Maalikiyyah) cewa " ɗan Numairin yace: naji baban Mus'abu yana cewa: naji Maaliku yana cewa: ALƘUR'AANI MAGANAR ALLAAH NE ba halitta bane.Sai baban Mus'abu yace: Duk wanda ya yishakkar haka ko kuma yace shi baruwanshi (ba zai ce halittane ko ba halitta ba) KAAFIRINE.
___________________
Muhammad Shittu Abu Uwaisat.
Share:

Dr. Gumi ya ce SALAF basu yi magana ba akan cewa shin Alqu'ani maganar Allah ne ko halittar sa ne ?? TOH AMMA KO SHIN WANNAN MAGANAR NA BABAN BOLA GASKIYA NE?

AN ZO INDA SU SHEIKH SA'IDU MAI KWANO GUSAU DA SHEIKH ALBANIY ZARIA SUKA CE MANA ANA NAN BABAN BOLA ZAI ISO WURIN.
!
BABAN BOLA YA JEFO WASU BOMABOMAN AMMA MALLAM  ABU AHMAD ATEEQ SULAIMAN YA TARWATSA SU DA IZININ ALLAH ASA'ILIN DA YA KAI ZIYARA BABBAN SHAFIN DA YAKE JAGORANTA NA 'YAN 'KUNGIYAR ANTI HADITH.
!
Dr. Gumi ya ce SALAF basu yi magana ba akan cewa shin Alqu'ani maganar Allah ne ko halittar sa ne ?? TOH AMMA KO SHIN WANNAN MAGANAR NA BABAN BOLA GASKIYA NE??
....
AMSA:
Mallam Abu Ahmad Ateeq yace: Dr. Gumi 'karya yake yiwa SALAF _ kuma dama ya saba yi musu 'karya _ , wannan mas'alar tana daga cikin matsalolin da babu wani littafi na SALAF da zaka ga bai tattauna ta ba . Da ace Dr. Gumi ya karanta littafin RISALA na fi'khun MALIKIYYAH , da yaga yanda SALAF suka tattauna mas'alar tun daga mu'kaddimar littafin .

2. Dr. Gumi yace malaman Musulmi magabata sun yi kuskure saboda rashin sani , da suka tafi akan cewa AL'KUR'ANI MAGANAR ALLAH NE !!! TOH AMMA KO SHIN WANNAN MAGANAR NA BABAN BOLA GASKIYA NE??
..
AMSA :
Anan DR.GUMI ya warware maganar sa ta farko , ya fa'da cikin wacce tafi ta farkon muni !! Dama haka 'yan bidi'a suke , basa tabbatuwa akan matsaya 'daya ; kullun suna cikin ru'dani !!!
Bai kamata ba Dr. Gumi ya kuskurantar da magabatan Musulmi akan IJMA'IN su akan cewa Al'KUR'ANI MAGANAR ALLAH ne , tunda sun dogara ne akan nassoshi na shari'a akan wannan matsayar tasu , daga cikin nassoshin akwai kamar haka :
ALLAH YA CE :
" ﻭ ﺇﻥ ﺃﺣﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺸﺮﻛﻴﻦ ﺍﺳﺘﺠﺎﺭﻙ ﻓﺄﺟﺮﻩ ﺣﺘﻰ ﻳﺴﻤﻊ ﻛﻼﻡ ﺍﻟﻠﻪ "
Saboda haka , abunda ya kamata Dr. Gumi yace shine
:
" Allah ya yi kuskure da yace Al'ku'ani maganar sa ne
...
3. Dr. Gumi yace SALAF da suka ce Al'kur'ani maganar Allah ne , hakan da suka ce babu komai lura da yanayin zamanin su , amma Mu a wannan zamanin dolene mu sauka dàga wannan matsaya ta SALAF , sai mu 'kudurta cewa Al'kur'ani HALITTA ne !! TOH AMMA KO SHIN WANNAN MAGANAR NA BABAN BOLA GASKIYA NE??
..
AMSA :
A'a Dr. Gumi , Mu SALAF sun wadatar damu , kuma Mu bama ganin AQIDAR MUSULUNCI tana sauyawa saboda banbancin zamani . Amma kai da kake ganin ana iya yiwa musulunci
gyare _gyare sa'banin yanda yake , to kana iya fita ma daga cikin sa , wannan matsalar ka ce !!!
!
MU TARA A DARASI NA GABA DON JIN CI GABAN WADANNAN AQEEDUN MU'UTAZILAWAN DA AKE DASAWA A MASALLACIN SULTAN BELLO KADUNA.  ALLAH (T) MUKE ROKO DA YA TSARE MANA IMANINMU.
Share:

Wednesday, 18 October 2017

Kissa:- miyasa sai banu umayya??




*ME YA SA SAI BANU UMAYYA?!*
   
(Rubutun Babban Masanin Tarihi, Dr. Ali as-Sallabiy).

Ibnu Kathir (r) yana cewa:

"Kabilar Banu Umayya sun ci kasuwar Jihadi; ba su da abin yi sai shi. Sun kaskantar da kafirci da kafirai. Kwarjinin Musulmi ya cika zukatan kafirai. Ba sakon da Musulmi su ka sa a gaba face sun ci shi da yaki."

Ba a san wata Kabila da ta yi mulki ta yi wa mutane abin da Kabilar Banu Umayya (r) ta yi musu ba. Banu Umayya suna da falala a kan al'ummar Musulmi tun kafuwar Musulunci har zuwa ranar al-kiyama. 

* Uthman dan Affan dan kabilar Banu Umayya ne. Shi ne ya tattara al-Kur'ani.

* Ummul Muminina, Ummu Habiba 'yar Abu Sufyan (r) 'yar kabilar Banu Umayya ce. Ta ruwaito mana sunnonin Manzo (SAW) ma su yawa.

* Mu'awiya dan Abu Sufyan dan kabilar Banu Umayya ne. Daya ne daga marubuta wahayi.

* Abdullahi dan Sa'id dan al-As dan Kabilar Banu Umayya ne. Daya ne daga shahidai goma sha uku na Badr.

* Yazid dan Abu Sufyan dan kabilar Banu Umayya ne. Shi ne ya shigar da Musulunci Lebanon; ya jagoranci rundunonin Sham.

* Yazid dan Mu'awiya dan kabilar Banu Umayya ne. Shi ne kwamandan rundunar farko da ta yaki Kusdandiniyya (Istanbul); Annabi (SAW) kuma ya ce "An gafarta wa rundunar farko da ta yi yaki a Kusdandiniyya).

* A cikin Banu Umayya a ke da Khalid dan Yazid. Shi ne ya kirkiro ilimin kimiyya.

* A cikin Banu Umayya a ke da Ukbatu dan Nafi'u (r). Shi ne ya kai Musulunci arewacin Afirka.

* A cikin Banu Umayya a ke da Umar dan Abdul Aziz.

* Wanda ya gina 'Kubbatul Sakhrah' (ta Masallacin Kudus), Abdul Malik dan Marwan, dan kabilar Banu Umayya ne.

* Banu Umayya ne suka kai Musulunci Andalus da Armenia da Azerbaijan da Georgia. Haka ma Turkiyya da Afghanistan da Pakistan da Indiya da Ozbakistan da Turkumanistan da Kazakhstan. Duka sun shiga Musulunci ne a hannun mahayan Banu Umayya.

* Banu Umayya ne suka kai Musulunci Turai; dama dai Andalus Banu Umayya ne suka bude ta. Kudancin Faransa bai taba zama kasar Musulunci ba sai zamanin mujahidan Banu Umayya.

* Abdurrahman Addakhil dan kabilar Banu Umayya ne. Shi ne ya ceto Andalus daga rugujewa.

* Abdurrahman Annasir dan kabilar Banu Umayya ne. Ya kasance daga manyan sarakunan duniya. Banu Umayya sun baza manzanninsu a lungu da saqon duniya suna kiran mutane zuwa ga addinin Allah (SWT); Manzannin Banu Umayya sun kai Musulunci China, wadanda su ka musu lakabi da *(masu fararen kaya)*.

* Ilimi ya yadu an yi mulki da adalci a zamanin Banu Umayya, a ka fara tattara hadisan Annabi a mulkin Banu Umayya.

* A zamanin Mulkin Banu Umayya a ka fara tattara hadisan Annabi, suka fassara kundaye zuwa larabci, su ka yi takardun kudin na Musulunci, su ka kera jirgin ruwan yaki na Musulunci na farko a tarihi.

* A zamanin mulkin al-Walid dan Abdul Malik dan kabilar Banu Umayya Musulunci ya yi kasaitar da bai taba yin irinta ba a tarihi.

* A zamanin Banu Umayya aka yi kiran sallah a duwatsun Himalayan kasar Sin, da qungurmin yankin Afrika da dazukan kasar Indiya da ganuwar Kusdundiniyya da kofofin Faris, da jigayin Portugal da gabban bakin kogi da fakon Georgia da bakin kogin Cyprus.

* A duk wadannan garuruwan farar tuta ce ta Banu Umayya dauke da kalmar *(La ilaha illallah Muhammadun Rasulullah)* ke kadawa.

*Allah Ya sakawa Banu Umayya kan abin da suka yi wa Musulunci da Musulmi.*

Da wannan na ke ganin dalilin da ya sa suka kafawa Banu Umayya kahon zuka.

Ga dukkan mai son shiga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH* sai ya yi saving wannan number +2348122248585  sannan ya tura da sunansa da adireshinsa ta whatApp. Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba.
Share:

Alqur'ani maganar Allah ne kuma wahayin shine?? Dr.ibrahim jalo jalingo

ALKUR'ANI MAGANAR ALLAH CE KUMA WAHAYIN SHI:

1. Ba a siffanta Alkur'ani Mai girma da cewa: Shi halitta ce, ko kuwa shi mai halitta ne ba, a'a abin da ake cewa game da shi shi ne: Alkur'ani Mai girma magana ce ta Allah, kuma wahayi ne naSa, wannan shi ne mazhabar Magabata; Imam Malik da waninsa.

2. Imam Husain Al-Bagwiy ya ce cikin littafinsa Sharhus Sunnah 1/186:-
((وقد مضى سلف هذه الأمة وعلماء السنة على ان القرءان كلام الله ووحيه ليس بخالق ولا مخلوق، والقول بخلق القرءان ضلالة وبدعة لم يتكلم بها احد في عهد الصحابة والتابعين رحمهم الله)).
Ma'ana: ((Magabatan wannan Al'ummah tare da Malaman Sunnah sun tafi a kan cewa: Alkur'ani Maganar Allah ce kuma wahayin Shi, sam ba mai halitta ba ne ba kuma wanda a ka halitta shi ba ne. Maganar cewa Alkur'ani halitta ce bata ce, kuma bidi'ah, babu mutum daya a zamanin Sahabbai da Tabi'ai Allah Ya yi musu rahama da ya taba hurta wannan maganar)).

3. Imamul Baihaqiy ya ruwaito cikin Sunan Athari na 21,415 daga Yahya Bin Khalaf Al-Muqri ya ce:-
((كنت عند مالك بن أنس، فجاءه رجل فقال: ما تقول فيمن يقول: القرءان مخلوق؟ فقال: زنديق كافر فاقتلوه)).
Ma'ana: ((Na kasance a gurin (Imam) Malik Dan Anas, sai wani mutum ya zo ya ce: Me kake cewa game da mutumin da yake cewa: Alkur'ani halitta ce? Sai (ya amsa) ya ce: Zindiki ne kafuri ku kashe shi)).

4. Imamuz Zahbiy ya ce a cikin littafin "Mukhtasarul Uluwwi Lil Aliyyil Gaffar" shafi na 75: Maimuun Bin Yahya Al-Bakriy ya ce:-
((قال مالك: من قال القرءان مخلوق يستتاب فان تاب وإلا ضربت عنقه)).
Ma'ana: ((Malik ya ce: Duk wanda ya ce Alkur'ani halitta ce, to a neme shi da ya tuba, in ya tuba shi ke nan, in kuma bai tuba ba sai a sare wuyansa)).

Allah muke roko da Ya tausaya mana Ya tsare mu daga fadawa cikin bidi'o'in Mu'utazilawa, da ma sauran bidi'o'in. Ameen.
Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
Share:

Tuesday, 17 October 2017

Ba'a Barin Ingantaccen Hadithi Saboda Ya Sabawa Wata Nazhaba Dr Ibrahim Jalo Jalingo


1. Matafiyar Annabi mai tsira da amincin Allah ita ce sama da dukkan wata matafiya (mazhaba), sannan fiqhunsa  shi ne sama da dukkan wani fiqhu.

2. Bin mazhabar (matafiyar) wani malami daga cikin Malaman Musulunci ba laifi ba ne matukar dai hakan bai kai mutum ga barin yin aiki da wani ingantaccen hadithin manzon Allah mai tsira da amincin Allah ba, in kuma ya kai shi ga barin yin aiki da wani ingantaccen nassin hadithin Annabi to lalle hakan ya haramta a bisa ittifakin dukkan Magabata na kwarai; saboda Annabi Muhammadu ne kawai Allah Ya aiko wa wannan Al'umma, duk kuma wani wanda ba shi ba to mabiyi yake a gare shi, kuma maganarsa shi Annabi Muhammadu tana sama da maganarsa.

3. To amma in aka sami wata mas'ala da babu nassin Annabi mai tsira da amincin Allah a kanta to a nan dukkan wani malami mai ikon yin ijtihadi sai ya yi ijtihadinsa  kuma duk hukuncin da ya samu kaiwa gare shi cikin ijtihadin nasa to da shi ne zai bauta wa Allah Ubangijinsa. Sannan kuma shi aammiy mara ikon yin ijtihadin Ilmi sai ya yi koyi da wanda zuciyarsa ta fi kwanciya da shi cikin mujtahidan da suka yi ijtihadin Ilmi a cikin wannan mas'ala wacce babu ingantaccen nassin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah a cikinta.

4. Ke nan wajibi ne a kan ko wane musulmi ya gina addininsa a kan sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah; saboda duk wanda ya bar yin aiki da ingantaccen hadithin Annabi mai tsira da amincin Allah cikin wata mas'ala daga cikin mas'aloli kuma cikin zabinsa da jin dadinsa a bisa hujjar cewa: mazhabarsa ta saba wa hadithin, ko wata darika tasa ta Sufaye ta saba wa hadithin, ko wani tsari na kungiyarsa ya saba wa hadithin, ko wani tsari na duniyarsa ya saba wa hadithin to lalle wannan ya bace ya bar hanyar Muminai, ya bar fikhun Sahabbai da Tabi'ai da Tabi'ut Tabi'in, Wannan shi ne abin da nassoshin Alkur'ani mai girma da Sunnah mai daraja ke tabbatarwa. Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah ya ce cikin Majmuu'ul Fataawaa 24/202:-
((واما من تبينت له السنة فظن ان غيرها خير منها فهو ضال مبتدع بل كافر)).
Ma'ana: ((Amma wannan da Sunnah ta bayyana gare shi, sannan ya yi zaton cewa waninta ya fi ta alheri, to shi dan'bidi'ah ne, kai kafiri ne ma)).
Ya kuma ce cikin littafin 27/125:-
((ومن ترك النقل المصدق عن القائل المعصوم واتبع نقلا غير مصدق عن قائل غير معصوم فقد ضل ضلالا بعيدا)).
Ma'ana: ((Wanda ya bar nakalin da aka gaskata daga mai fada wanda yake ma'asuu'mi, sannan ya bi nakalin da ba a gaskata ba daga mai fadan da ba ma'asuu'mi ba, hakika ya bace bata mai nisa)).

Allah Ya taimake mu Ya dora mu a kan daidai har kullum. Ameen.
Share:

Monday, 16 October 2017

(Video)Takaitaccen bayani Mai matukar amfani - Dr.ibrahim isah ali pantami


Takaitaccen bayani mai matukar amfani

 daga:
   Dr. Isa Ali Pantami.

DOMIN SAUKO DA WANNAN VIDEO SAIKU SHIGA WANNAN BLUE RUBUTU DAKE KASA


Ayi kallo lafiya



Share:

ADDU'AR SAMUN DUKIYA DA 'YA'YA MASU ALBARKA


Wannan addu'ar an tsagota ne daga shahararriyar addu'ar nan wacce Manzon Allah (saww) yayi ma Sayyiduna Anas bn Malik (ra) alokacin da Mahaifiyarsa ta kawoshi gareshi.

Ga addu'ar nan kamar haka :

اللهم أكثر مالي وولدي وبارك لي فيما أعطيتني.

ALLAHUMMA AKTHIR MALIY WA WALADIY, WA BARIK LIY FEEMA A'ATAITANEE.

FASSARA : "Ya Allah ka yawaita dukiyata da 'ya'yana. Kuma ka albarkaceni acikin abinda ka bani".

ADUBA :

Sahihul Bukhariy hadisi na 1982.

Source;hausaloaded.com
Share:

ABUBUWA GUDA 6 SUNA JANYO RASHIN ALBARKA

ABUBUWA GUDA 6 SUNA JANYO RASHIN ALBARKA



Albarka yana nufin alkhairi mai yawa mai dauwama,Albarka idan ta samu acikin dukiya sai dukiyar ta yawaita ta zama mai yawan amfani,haka idan ta samu acikin 'ya'ya sai su amfaneka duniya da lahira,idan kuma aka sameta a rayuwa sai rayuwar ta zama mai amfanu duniya da lahira mai tserarwa a duniya da lahira.

Allah Madaukakin sarki idan yana nufin bawansa da alkhairi sai ya sanya albarka acikin abinda ya basa,har sai an wayi gari abu kadan yazama mai yawan amfani,karami ya zama babba da izinin Allah.


Daga cikin abubuwan da suke janyo rashin albarka a rayuwa ga kadan daga cikinsu;-

1-Na farko
*"Rashin jin tsoran Allah da rashin kiyaye dokokinsa da umarninsa"*.

Allah ﷻ،yana cewa:
﴿ﻭﻟﻮ ﺃﻥ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻘﺮﻯ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﻭﺍﺗﻘﻮﺍ ﻟﻔﺘﺤﻨﺎ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺑﺮﻛﺎﺕ ﻣﻦ ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ ﻭﺍﻷﺭﺽ﴾.

Taqwa wato kiyaye dokokin Allah da bin uwarninsa da hanuwa da haninsa yana janyowa saukowar albarka daga sama da kasa,kuma ya yawaita albarka a tsakanin al'umma baki daya,amma rashin Taqwa da yawaita basa umarnin Allah da keta iyakokin Allah yana janyo rashin albarka da daukewar arziqi abayan kasa.

2-Na biyu
*"Gafala cikin rashin Addua da rokon Allah,da rashin kwadayi da neman abinda yake wajan Allah"*

Wata rana Manzon Allah ﷺ sai ya sami Sahabi Abaa Umama R.A shi kadai babu kowa,a tare da shi akwai alamar bakin ciki da damuwa,sai Manzon Allah ﷺ yace da shi;
*(Mi ya zaunar da kai acikin Masallaci yanzu a lokacin da ba lokacin sallah ba??)*sai yace Ya Manzon Allah ﷺ kuncin rayuwa ya sameni kuma ga bashi yayi mini yawa,sai Manzon Allah ﷺ yace;
*(shin bazan Koyarda kai ba abinda idan kafa Allah zai tafiyar maka da bakin cikin da kake cika ba?? Kuma ya biya maka dukkan bashin da yake tare da kai ba??)*sai yace;Eh ya Manzon Allah,sai yace da shi;
*(Idan ka wayi gari ko idan kayi yammaci sai kace:)*
"ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺍﻟﻬﻢ ﻭﺍﻟﺤﺰﻥ،ﻭﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺍﻟﻌﺠﺰ ﻭﺍﻟﻜﺴﻞ،ﻭﻣﻦ ﺍﻟﺠﺒﻦ ﻭﺍﻟﺒﺨﻞ، ﻭﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﻏﻠﺒﺔ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻭﻗﻬﺮ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ،"
Abu Umama yake cewa;
"Sai na riqa fadar wannan adduar sai Allah ya tafiyar min da dukkan damuwata kuma ya biyamin bashin dake kaina".

3-Na Ukku
*"Yanke zuminci yana janyo kuncin rayuwa da rashin albarka acikin rayuwa da arziqi"*

Manzon Allah ﷺ yana cewa;
*(Dukkan wanda yake son Allah ya yalwata arziqinsa kuma ya tsawaita rayuwarsa,to ya sadar da zumincinsa)*.
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭﻣﺴﻠﻢ.

Kyawawan halaye da sadar da zumici yana janyo albarka acikin rayuwa da arziqi da dukiya da 'ya'ya,haka kuma rajin sada zuminci yana janyo rashin albarka acikin su.

4-Na hudu
*"Rashin sadaka da ciyar da dukiya cikin daukaka kalmar Allah"*.

Hakika Allah ﷻ ya hukunta dukkan wanda ya ciyar da dukiya ko yayi sadaka ga masu buqata,to Allah zai yalwata masa kuma ya buda masa hanyar samu mai yawa,kuma ya sanya masa albarka acikin dukiyarsa.

Manzon Allah ﷺ yana Fada ga Asma'h R.A;-
*(Ki ciyar sai Allah ya ciyar dake)*
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ.
A kowane yini Akwai Mala'iku guda biyu suna cewa;
*(Ya Allah ka sanya albarka ka rubaiya duniyar wanda yake ciyarsa,ya Allah ka janye albarka acikin dukiyar wanda baya ciyarsa)*
@ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭﻣﺴﻠﻢ.

5-Abu na biyar
*"Kasala da barin aiki"*

Musulinci addini ne na aiki da addini bane na cima zamne ba,Manzon Allah ﷺ yana cewa;
*(Kuma an sanya aziqina a karkashin inuwar takobina)*
@ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ.

6-Na shida
*"Rashin dogaro ga Allah ingantacce tare da rashin neman arziqi a wajan Allah"*.

Manzon Allah ﷺ yana cewa;
*(Da dai zakuriqa yin dogaro ga Allah hakikanin dogaro,da Allah ya azurta ku kamar yanda yake azurta tsuntsu,yana fita da sassafe cikinsa babu koma,amma ya dawo da yamma cikinsa a cike)*
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺣﻤﺪ ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻭﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﺔ ﻭﺍﺑﻦ ﺣﺒﺎﻥ ﻭﺍﻟﺤﺎﻛﻢ ، ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ :ﺣﺴﻦ ﺻﺤﻴﺢ.


Allah ne mafi sani.


ﺃﺳﺄﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻥ ﻳﻤﻦ ﻋﻠﻴﻨﺎ ﺟﻤﻴﻌﺎ ﺑﺎﻟﺘﻮﻓﻴﻖ ﻭﺍﻟﺮﺯﻕ ﻭﺍﻟﺒﺮﻛﺎﺕ ،،،
ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺑﺎﺭﻙ ﻋﻠﻰ ﻧﺒﻴﻨﺎ ﻣﺤﻤﺪ



Shiga nan
www.duniyarfatawa.com.ng
Share:

Sunday, 15 October 2017

Daidaita Tsakanin Namiji Da Mace A Rabon Gado !!!! Dr jamilu Yusuf Zarewa

Tambaya?

Assalamu alaikum mallam menene hukuncin wanda ke kokarin ganin an baiwa mace  kason da aka bawa namiji wajen rabon gado?

Amsa :
Wa'alaykumussalam, Ya sabawa Allah, Hakan kuma zai iya fitar da Shi daga musulunci in har ya yi gangancin hakan, saboda kokari ne na warware hukuncin da Allah ya zartar. 

Allah ya yi alkawarin wuta mai kuna ga duk Wanda ya sabawa ayoyin rabon gado a  cikin aya ta 14 a suratun Nisa'i.       
             
Wanda ya yi kira a daidaita namiji da mace a rabon gado saboda jahiltarsa da sharia ba za'a kafirta shi ba, Saboda ba duk Wanda ya aikata kafirci ba ne yake zama kafiri kamar yadda aya da hadisai da yawa suka tabbatar.  

Allah ne mafi sani.

14/10/2017

DR JAMILU ZAREWA
Share:

Audio:- Wa'azin Hadin Gwuiwa Nigeria Da Niger -Sheikh Abubakar Gero Argungu

WA'AZIN HADIN GWUIWA NIGERIA DA NIGER

Tare da:
SHEIKH ABUBAKAR GERO (HAFIZAHULLAH)

NA RANAR ASABAR

DAGA DAURA L.G KATSINA STATE NIGERIA


AYI SAURARO LAFIA

Shiga nan
Share:

HUKUNCIN MIKEWA MALAMI KO SHUGABA DON GIRMAMAWA - Dr.jamilu yusuf zarewa

*HUKUNCIN MIKEWA MALAMI KO SHUGABA DON GIRMAMAWA*


*Tambaya :*

Assalamau alaikum Malam. Ina teaching practice ne yanzu, kuma idan na je aji yara suna mikewa damin gaishe ni, mal. na barsu su cigaba ko na dakatar da su ?

*Amsa :*

Wa alaikum assalam To dan'uwa akwai malaman da suka ta fi akan cewa makaruhi ne a mikewa malami, akwai kuma wadanda suka haramta, akwai wadanda kuma suka halatta.
Saidai maganar da ta fi ita ce bai hallata malami ya nemi a mike masa ba, saboda fadin Annabi s.a.w. " Duk wanda ya so mutane su mike masa to ya tanaji wurin zamansa a wuta" kamar yadda tirmizi ya rawaito shi kuma ya kyautata shi a hadisi mai lamba ta : 2755, Albani kuma ya inganta shi a silsilatussahihah lamba ta : 5957.
Amma idan aka mikewa malami ba tare da ya nema ba, to wannan babu laifi ga wanda ya mike da wanda aka mike saboda shi, domin ya zo a hadisi cewa : Annabi s.a.w. ya nemi mutanen Madina su mikewa  Sa'ad, lokacin da ya gabato"  kamar yadda Bukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta :2878, wannan sai yake nuna halaccin mikewa ga mutane masu falala kamar malamai da manyan mutane, lokacin da suka gabato .

 Don neman karin bayani, duba : Alminhaj na Nawawy 12/440, da Mirkataul mafaatiih sharhu mishkatil-masaabiih shafi na : 2972 BABU ALKIYAM . .

Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
24\11\2014

Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

Shiga nan
www.duniyarfatawa.com.ng
Share:

HUKUNCI KAYYADE HAIHUWA (FAMILY PLANNING) Dr.jamilu yusuf zarewa

*_HUKUNCI KAYYADE HAIHUWA (FAMILY PLANNING)_*


*_Tambaya_*

Assalamu alaikum
 Shin ko akwai dalilai na shariah da suke halatta mace ta juyar da mahaifarta ko kuma ta samu tazarar haihuwa?


*_Amsa_*
Wa'alaykumussalam,

 To dan uwa amfani da abin da zai kayyade iyali, ya kasu kashi biyu

 1. Ya zama zai hana daukar cikin kwata-kwata, a nan bai halatta ba, saboda ya sabawa manufar shari'a na yawaita al’uma, kuma ‘ya’yan da take da su za su iya mutuwa sai ta koma mai wabi.

 2. ya zama an tsayar da shi ne na dan wani lokaci, kamar mace ta zama tana yawan haihuwa kuma cikin yana wahalar da ita, sai ta yi nufin ta tsara haihuwarta ta yadda za ta haihu duk bayan shekara biyu ko makamancin haka, to wannan ya halatta in dai miji ya bada izini kuma ba zai cutar da matar ba, dalili akan haka shi ne sahabbai sun kasance suna azalu a zamanin Annabi s.a.w. don kar matansu su dauki ciki, kuma ba’a hana su ba, kamar yadda Bukari ya rawaito daga hadisin Jabir mai lamba ta: 4911.

Abin da ake nufi da azalu shi ne idan namiji yana saduwa da matarsa idan ya ji maniyyi zai fito sai ya fitar da azzakarinsa ya zubar da maniyyin a wajen farji.

Duba Dima'uddabi'iyya na Ibnu Uthaimin shafi na 57.

*_Dr. Jamilu Zarewa_*

13/7/2014

SHIGA NAN DOMIN JOINING FACEBOOK GROUP DINMU

https://m.facebook.com/groups/129667237690008?ref=bookmarks
Share:

Saturday, 14 October 2017

HUKUNCIN BOYE KAYA HAR SAI SUN YI TSADA ?

*HUKUNCIN BOYE KAYA HAR SAI SUN YI TSADA ?*

*Tambaya :*

Assalamu alaikum.malam  wata tambaya nake da ita Dr. Wai shin meye gasiyar hukuncin wanda ya sayi kaya a lokacin da suke araha ya boye da niyyar in sunyi tsada ya fito da su ya sayar dan ya sami riba mai yawa? Allah shi dada budi amin

*Amsa :*

Walaikum assalam To dan'uwa ya zo a hadisi cewa : "Ba wanda yake boye kaya sai mai zunubi"  Tirmizi  ya rawaito shi a : 3\567, kuma ya kyautata shi, saidai  malamai sun yi sabani akan irin kayan da ya haramta a boye da wadanda ba su haramta ba :
1. Akwai wadanda suka tafi cewa : duk wani abu da mutane suke bukatarsa to bai halatta mutum ya siya ya ajjiye ba,  da nufin sai yayi tsada ya fito da shi, don haka har tufafi da magunguna bai halatta a boye su ba, saidai idan ya siya ne da nufin ya yi amfani da su  nan gaba. Ko kuma iyalansa, Wannan shi ne maganar Abu-Yusuf babban almajirin Abu-hanifa, kamar yadda yazo a littafin : Daurul-kiyam wal'aklak fil-islam shafi na : 295. Sannan ita ce maganar Malik a Mudawwanah kamar yadda ya zo a : 4\291.
2. Akwai malaman da suka tafi cewa ya halatta a boye abin da yake ba abinci ba ne da mutane za su ci su rayu, kamar barkono, zabibi, mai, da sauransu, saboda yawanci mutane suna cutuwa ne idan aka boye abinci. An rawaito wannan daga  Abdullahi dan Mubarak da Sa'id dan Musayyib kamar yadda Tirmizi ya ambata a Sunan dinsa  3\567   sannan ita ce maganar Shafi'iyya  da Hanbaliyya , kamar yadda ya zo a
Raudatu Addalibiina 3\411 da kuma Almugni 4\154

Wasu malaman suna rinjayar da maganar farko, amma idan ba siyan abin ya yi ba, ya mallake shi ne ta wata hanya, ko kuma ya noma sai ya boye har ya yi tsada sannan ya siyar, to wannan bai haramta ba, ko da kuwa abinci ne, har wasu malaman ma  sun hakaito ijma'in malamai akan halaccin haka, kamar yadda ya zo a Jami'ussagir  shafi na : 481

Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
15/8/2014
Share:

Cikakken bayani akan sallar qasaru, Wasu sunce kwana 3 ce??

*TAMBAYATA (36)*

*INASAN CIKAKKEN BAYANI ASALLAR QASARU WASU SUNCE KWANA UKU NE?*

الحمد لله.

AMSA: ldan Mutum yaqudurci zama agarinda zashi sama da kwana hudu, hukuncinsa shine hukuncin mazaunin gida daka lokacinda yashiga garin dazashi, amma ahanya zaidunga kasaru kafin ya isa zuwa garin, dazarar yashiga garin zaidunga cika sallah bai halatta yai kasaru ba.

Yazo afatawa lajnatul da'imah ( 8/99)

Sukace:Tafiyar daza'ai mata kasaru itace, tafiyar da a'al'ada za'ace kayi tafiya, bacewa za'ai kaje unguwaba wannan tafiyar zakai mata kasaru, gwar-gwadon yanda za'ace tafiya kayi ba inguwa kaje ba, abisa kaddarawa shine sukace kilo mita saba'in, Amma wannan ra'ayin wasu malaman fiqhu ne, indai a yanda aka sani agarinku cewa inakaje gari kaza kayi tafiya, inkaje gari kaza baza'ace tafiya kaiba saidai ace kaje unguwa to bazakaiwa wannan tafiyar kasaru ba, bawai da kilo mita ake tan-tance tafiyar daza'aiwa qasaru da wacce baza'ai mata ba.

Wannan tafiyar duk wani sauki da'akaiwa matafiyi zaka sameshi, kamar shafa akan kuffi wuni da dare na kwana uku, da rage raka'o'in salloli, da hade salloli dashan azumi aramazhaan,

Wannan gawanda bai niyyaci zama agarinda zashiba sama da kwana hudu, amma idan yaniyyaci zama agarin dazashi sama da kwana hudu daka lokacin dayashiga garin garabasar matafiyi tasauka daka kansa, Idan kuma kwana hudun zaiyi cif-cif zaiyi kasaru dasauran rangwamen dake kan matafiyi.

*Matafiyinda yai tafiya amma bai san adadin kwanakin dazaiyiba kuma bai iyakance wani lokaci qayyadadde ba nazamansa agarin dazaije, to zaitayin kasaru koda lokaci maitsawo yazauna agarinda yaje, Babu ban-banci tsakanin tafiya akan jrigi ko kan ruwa ko  akafa*

Sannan yahalatta matafiyi yahada salloli biyu, jam'u taqdem hada azahar da la'asar yayishu farkon lokacin la'asar, ko jam'i taqseer, yahada azahar da la'asar aqarshen lokacin la'asar, haka magariba da isha'i.

Amma abunda yafi shine kada matafiyi yahada sallah sai idan yin kowacce alokacinta zai masa wahala kuma zaisha wuya.

Mu Sani sallar jam'i wajibice akan matafiyi kamar mazaunin gida.

Saboda haka idan mutum yaniyyaci zama agarinda zashi sama da kwana hudu, rangwamen mayafiyi baya kansa dazarar yashiga garin.

Idan kuma bai kulla niyyar zama acanba kobaisan yaushe zai dawo ba, kawai daya gama uzurinsa zai dawo gida, tozaita kasarune koda zaiyi wata agarinda yaje.

Dalili Shine Annabi Sallallahu Alaihi Yai kasaru tsawon kwanaki goma sha uku, sannan kuma malamai sukace: Allah bai iyakance adadi ayyananne ba.
Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.

*📝Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai.*
*Watsapp Group.*
*+2348123432272.*
*+2348140925493.*
Share:

Kissar Annabi Adam (AS) “No-1”

Kissar Annabi Adam (as) Na Farko
(1)
KISSAR ANNABI ADAM NA FARKO (AS)
Shida Annabi Adam (As) an halicce shine daga abubuwa guda 2 wato jiki da ruhi,kuma shine jiki na faro da All.. Madaukakin sarki ya taba halitta ,kana aka hura masa rai aka rayar dashi ya zama ya samu kamala ta halittar sa ayoyi daban daban acikin Al’kur’ani sunyi maganganu masu yawa game da aka halicci Annabi Adama (As) wanda hakan ke kara tabbatar da lallai an halicci Annabi Adam ne daga Turbaya, All.. Madausarkiya fadi acikin Alkur’ani cewa lallai All.. ya zabi Annabi Adamu da Nuhu da Ali Ibarahim akan dukkan talaikai, don haka lokacin da All.. yayi nufin halittar Khalifansa wanda zai zama shugaba mai shiryarwa a bayan kasa sai ya bijiro da wannan labarin ga Mala’iku amma sai malak’iku sukaji mamakin wannan labari, sai suka koma ga kawukan su suna magana cewa Ashe All.. zai halicci wata halitta da zai sa ta kasance khalifar sa a bayan kasa wadda zai yi wahala ya kasance mai ilimice da tsarki da tusayi kammar saruan halittun ubangiji dake sama, domin kafin halittar Adam All.. ya halicci wasu mutane wadanda suka tafka zamba da fasadi a bayan kasa , don haka sai suka cewa ubangiji ashe zaka sanya wadanda zasuyi barna da fasadi su zubda jini a bayan kasa? alhali mu muna tsarkake ka muna tasbihi gareka, amma saboda da hikimar da yasa All.. Madaukakin sarki ya halicci Annabi Adam da yake ilimi ne na gaibu babu wanda ya sani banda ubagiji sai All. Ya basu amsa da cewa hakika nasan abinda baku sani ba game da halittar Annabi Adam, don haka nema bayan da All.. Madaukakin Sarki ya Halicci Annabi Adamu (As) sai ya sanar da shi sunayen abubuwa yadda zai iya amfana dasu a bayan kasa ba tare da yasha wahala ba, daga nan sai All.. ya umarci su da suyi sujuda gareshi kuma su girmama shi domin yana dauke da ilimin da su basu dashi, kuma irin kallon da sukeyi masa na kaskantarwa su dawo daga rakiyar sa, wannan yasa ma aka bijirowa da mala’iku sunayen wasu abubuwa kuma akace su fadi sunayen su amma sai suka kasa bada Amsa amma da aka bijiro dasu ga Annabi Adam sai ya fadi sunayen su daya bayan daya, daga nan ne All.. madaukakin Sarki yace musu ashe bance muku nasan abinda ku baku sani ba, sai sukace ya ubangiji mu ba muna nuna rashin amincewar mu da nufin ka ba ne, To a nan ne batun kamalar dan Adam zai zo Inda All.. Madaukakin Sarki ya bukaci ya Annabi Adam zuwa wata kamala ta kololuwa inda anan ne All.. Madaukakin Sarki ya umarci mala’iku da suyi sujuda ga Annabi Adam (As) dukkansu sai sukayi Sujuda banda Iblis shine kawai yaki yin Sujuda yayi girman kai ya Kafircewa Ubangiji, sai dai All.. ya san dalilan da yasa bai yi Sujuda ga Annabi Adam ba, saboda yana ganin yafi Annabi Adama daraja domin shi an halicce shi ne daga lakka yayin da shi kuma Shedan an halicce shi ne daga wuta don haka ba zai yiyu wuta tayi Sujuda ga lakka ba, daga nan sai All. Madaukakin sarki ya koreshi daga Aljannah kuma ya la’ance shi ya zama tsinanne har zuwa ranar tashin Alkiyama sai dai shedan ya nemi All.. Madaukakin Sarki yayi Masar Rangwame ya kyaleshi har zuwa ranar tashin kiyama yace yayi Alkawarin sai yaa halakar da dukkan yayan Adam sai da wanda All.. ya kare daga cikin su, All. Madaukakin sarki ya fitar dashi daga Aljanna kuma yayi Al’kawarin sanya shi a cikin wuta da dukkan wadanda suka bi shi baki daya to bayan da aka fitar da shedan daga Al’jannah sai All. Madaukakin Sarki ya umarci Annabi Adamu da Hauwa’u da su shiga cikin aljanna su zauna domin su ji dadi daga ni’amar da All.. ya tanada acikin Aljnah, aka hallata musu dukkan abinda ke ciki amma sai aka hanesu daga cin wata bishiya, ko ma zuwa kusa da ita, kamar yadda yazo a cikin Alkur’ani mai girma cewa lokacin da aka cewa Annabi Adamu da Matar sa ku shiga cikin Aljanna kuma kuji daga dadin da aka tanadar muku aciki, kuma kada ku kusancin wannan bishiyar har dai zuwa karshen aya, amma sai shedan ya biyo su domin ya yaudare su ya halakar dasu kamar yadda yayi Alkawari, kuma ya sanya musu wasuwasi domin ya cire musu Surturar tsoron All. Da aka sanya musu na karama da kamala, , sai yace musu ubangjin ku ya hana ku cin wannan itaciyar ne ba don komai ba sai idan ku kaci wannan bishiyar to zaku zama mala’iku ne , ko kuma ku dawwama a cikin Aljannah, ya rantse musu cewa lallai ni ina son ku da Alkhairi ne, haka dai shedan yayi ta zawarcin su har ya kai ya yaudare su yasa suka ci wannan Itaciyar lokacin da haka ta faru sai suturar kamala da karama da aka sanya musu ta kwabe daga jikin su, anan All. Maduakakin sarki yayi magana da Annabi Adam (AS) cewa ashe ban hana ku cin wannan bishiyar ba, kuma ban gaya muku cewa shedan makiyin ku bane? Nana da nan sai Annabi Adamu da Hauwa’u suka gane kusakuren da sukayi amma nan ba yana nufin sun yi laifi bane kamar yadda sauran mutane sukeyi ba ne a’a sun bar abinda ake kira da tarkkir Aula ne wato barin abinda ya yafi dacewa amma ba laifi bane domin su Annabawa basa zunubi basa laifi, wanan kenan to daga nan sai suka nemi gafarar ubangiji game da barin abinda ya dace da sukayi, sai All. Ya fitar da su daga cikin Aljannah ya saukar dasu a gidan duniya kamar yadda yazo a cikin Alkur’ani mai girma ” sai shedan ya yaudaresu ya fitar dasu daga inda suke wato aljannah ke nan sai akace ku sauka cikin duniya sashin ku yana adawa da sashi kuma za’a sanya ku tabbata a kasa ku ci gaba da rayuwa har zuwa karshen rayuwar ku, kuma duk wanda ya bi shiryarwar ubangiji kuma bai aikata wani zunubi ba a bayan kasa to mummunar makoma ba zata shafe shi ba. Ya zo acikin tarihi cewa dukkan abubuwa dake cikin Aljannah All.. Madaukakin Sarki ya halartawa Annabi Adam da matar sa banda itaciya daya da aka hanashi ya kusance ta, to shin wacce irin bishiya ce ? Marigayi Allama Dabrasi ya bayyana a cikin Littafin Tafsirin sa na Majma’ul Bayan cewa yazo a cikin ruwayoyi wannan itaciyar Itaciya ce ta Alkama wato kafin ta girma ta isa yankewa, wata ruwayar kuma ta nuna cewa itaciyar Inabi ce kafin ta rika, sai dai Allama Dabrasi ya kara da cewa baya ga batun bishiyar Al’kama da Inabi ruwayoyin da aka samu daga Imam Ali (As) sun nuna cewa wannan Itaciyar itacen Kafur ne,
ku Kasance Tare Damu A Wani Post Na Gaba Kan Ci Gana Da Karatu.

Source: www.sunnahmedia.com.ng

SHIGA NAN DOMIN JOINING FACEBOOK GROUP DINMU

https://m.facebook.com/groups/129667237690008?ref=bookmarks
Share:

Archive

Unordered List

Support