*_JINI YANA ZUBO MINI, BAYAN CIKINA YA KAI WATA HUDU?_*
*Tambaya*
Assalamu Alaikum Dr. dan Allah inada tambaya akan matar da keda ciki yakai wata hudu sai jini ya rinka xubar mata daga baya kuma sai ya dauke bayan kwana guda ko biyu yakan iya dawowa ko bayan wasu awoye shin ya hukuncin sallar ta? xata jinkirta sallah sai jinin ya dauke ko xata rika yin wanka duk sanda ya dauke tayi rankon sallolin baya ne.
Nagode
*Amsa*
Wa alaikum assalam
To 'yar'uwa mutukar cikin ya kai wata hudu kuma jinin da yake fita yana hade da ciwon haihuwa, to ya zama jinin biki, kuma zai hana sallah, amma Idan babu ciwon haihuwa to mutukar ya zo da sifar jinin haila (baki ko karni) to zai zama haila, tun da a zance mafi inganci mai ciki tana iya yin haila.
In ya fita daga wadannan biyun zai zama jinin cuta ta yadda ba zai hana sallah ba, in har jinin kusa-kusa yake fita, za ki iya jinkirta salloli, sai ya dan tsagaita, sai ki rama sallaolin da aka yi su kina da tsarki, saboda addinin musulunci addini ne mai sauki, babu kunci da damuwa a cikinsa, kamar yadda aya ta karshe a suratu Al-hajj ta yi bayanin haka.
Allah ne mafi Sani.
*Amsawa*✍🏻
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
03/02/2016
Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

0 comments:
Post a Comment