BAMBANCI TSAKANIN MUNAFUNCIN ZUCIYA DA MUNAFUNCIN AIKI !!?? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Wednesday, 4 October 2017

BAMBANCI TSAKANIN MUNAFUNCIN ZUCIYA DA MUNAFUNCIN AIKI !!??

*BAMBANCI TSAKANIN MUNAFUNCIN ZUCIYA DA MUNAFUNCIN AIKI*

*_Tambaya:_*
Mal. menene bambanci tsakanin nifakul amali da i'itikaadi ?

*_Amsa:_*
To malam : Nifaqul i'itikadi (wanda ake kudurcewa a zuciya) shi ne boye kafurci da kuma bayyana musulunci, kamar yadda wasu mutane suka yi a zamanin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, duk wanda ya siffantu da wannan to ba musulmi ba ne.

Amma nifakul-amali (aiki) kuwa to shi ne wanda ya zo a cikin hadisin abdullahi dan amr inda annabi s.a.w. yake cewa : "Dabi'u guda hudu duk wanda suka kasance tare da shi, to ya zama cikakken munafiki, wanda kuma yake da daya daga cikinsu to yana da dabi'ar munafukai har sai ya barta : idan ya yi zance ya yi karya, idan aka amince masa ya ci amana, idan ya yi alkawari ya yi yaudara, idan ya yi husuma sai ya yi fajirci". Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta : (34) da Muslim a hadisi mai lamba ta : (106).

Don haka in mutum ya siffantu da daya daga cikin wadannan dabi'u guda hudu, to bai fita daga musulunci ba, saidai yana da tawayar imani.

Allah ne mafi sani.

*_Dr Jamilu Zarewa_*

16/11/2014

Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support