Aiki 10 landansu dai-dai da qiyamul-laiili ?? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Wednesday, 11 October 2017

Aiki 10 landansu dai-dai da qiyamul-laiili ??

AYYUKA GUDA 10 LADANSU DAI DAI DA QIYAMUL-LAILI!
Mu ji tsoron ALLAH kuma mu binciki kanmu domin tafiya zuwa barzahu zuwa lahira yana nan kusa don haka mu yi tattali.
Mu yi aiki na kwarai domin ALLAH yana kallonmu. Hakika Magabata na kwarai ba sa wasa da KIYAMULLAILI domin guzurinsu zuwa Lahira.
Saboda kaunar da ALLAH yake mana tare da tausaya mana, sai yayi mana kyautan wasu ayyuka masu sauki wanda idan aka yi su za'a sami ladan kiyamullaili, idan kai ragone baka KIYAMULLAILI to kada wadannan ko wasu bangarensu su subuce maka, idan kuma kana KIYAMULLAILIN ka hada da wadannan rayuwarka zai yi albarka da yawan lada, kada in cikaku da surutu ga su nan kamar haka:
1-KARANTA AYOYI 100 A DARE: ANNABI (SAW) yace: "Wanda ya karanta ayoyi 100 da dare za'a rubuta masa ladan kiyamullaili". [AHMD, DRM-3450, SHH-JM'U-6468].
2-KARANTA AYOYI 2 NA KARSHEN BAQARA:
"Wanda ya karanta ayoyi biyun karshen Baqara da dare to ya ishe a matsayin kiyamullaili da kariya." [AHMD, BHR-5010, MSLM, TRMZ-2881, AB DWD-1397, BN MJ-1369, DRM-1487].
3-SALLAR ISHA'I DA ASUBAHI A JAM'I: "Wanda yayi sallar isha'i da asuba a jam'i kamar ya kwana yana kiyamullaili". [MLK, AHMD, MSLM, TRMZ, AB DWD, DRM-1224].
4-KYAWUN HALI: "Lalle Mumini don kyawun halinsa <a kullum> yana samun darajan mai kwana yana kiyamullaili kuma mai wuni da azumi". [MLK, AHMD, AB DWD-4798, BN HBN-480, HKM, SHH JM'I-1620].
5-NIYYAR YIN KIYAMULLAILI: "Wanda ya kwanta da niyyar zai tashi yayi kiyamullaili sai bai samu
farkawa ba har gari ya waye to za'a rubuta masa ladan abinda yayi niyya sai barcin nasa ya zama sadakane UBANGIJINSA yayi masa". [NS'I-1787, BN MJH-1344, SHH JM'I-5941].
6-TARAWIHI A JAM'I: "Wanda yayi sallar <tarawihi> tare da imam har aka karasa dashi, za'a basa ladan kiyamullaili gaba daya". [AHMD, AB DWD-1375, TRMZ, NS'I-1364, BN MJH-1327, SHH JM'I-1615]
7-NAFILA RAKA'A 4 KAFIN AZAHAR: "Wanda yayi nafila raka'a 4 kafin azahar dai-dai yake da salla a sulusin dare". [IBN AB SHYB-5940, SLSLT SHH-1431].
8-KIYAYE WASU LADUBBAN JUM'A: "Wanda yayi wanka kuma yasa wankakken kaya sai yazo juma'a da wuri kuma da kafa bai hau abin hawa ba kuma ya zauna kusa da imam ya saurari khuduba bai yi wasa ko surutu ba, to kowane takunsa daya yana da ladan ibadan shekara daya azuminta da kiyamullailinta". [AHMD, TRMZ, AB DWD, NS'I-1381, BN MJH-1087, DRM-1547, HKM-1041, BN HZM-1758, SHH JM'I-6405].
9-KULA DA GAJIYAYYU: "Wanda yake dawainiya da Gajiyayyu da Miskinai, yana da lada tamkar mai jihadi da kiyamullaili". [AHMD, BHR-5353, MSLM-2982,TRMZ-1969, NS'I-2577, BN MJH-2140, BN HBN-4245, BHQ-12,444].
10-KARANTAR DA WADANNAN ABUBUWAN: ANNABI (SAW) yace: "Wanda ya nunawa mutane
aikin alhairi yana da lada kwatankwacin haka ba tare
da an rage nasu ba".
Don haka ka isar da abinnan da kaji ga iyalanka da abokanka a ciki da wajen Whatsapp (da duk wani social net. ko wata hanyar) zaka sami makudan LADAN KIYAMULLAILI!
Karantawa kadai ba shine mora ba sai an yi aiki dashi. Ni mai fada da Kai me karantawa ALLAH ya bamu ikon aiki dashi KUMA YA HADA MU A ALJANNAR FIDAUSI


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support