Abubuwan daya kamata mace mai yaron ciki ta kula dasu!! Dr.jamilu yusuf zarewa ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Sunday, 8 October 2017

Abubuwan daya kamata mace mai yaron ciki ta kula dasu!! Dr.jamilu yusuf zarewa

*ABUBUWAN DA YA KAMATA MACE MAI YARON CIKI TA KULA DA Su!!!*


*Tambaya*

Assalamu alaikum
Don Allah Malam wata tambaya aka yi min, shi ne na ke son a taimaka min wajan ba da amsa, tambayar ita ce : me ya kamata mai yaron ciki ta kula da shi ?


*Amsa*
Wa'alaykumussalam

To malama akwai abubuwan da ya kamata mace ta kula da su, lokacin da take da ciki, ga wasu daga ciki :

1. Ki yi kokari, ki dinga cin halal, saboda lokacin da yaro yake ciki, na daga cikin lokutan da yaro yake ginuwa, don haka, idan kina cin haramun, yaron zai ginu da ita, sai Allah ya fara cirewa gabobinsa son alkhairi, tun yana yaro, domin duk jikin da ya ginu da haramun zai zama mai kasala wajan aikata abin da Allah yake so, kamar yadda malamai suka yi bayani.

2. Wasu malaman suna cewa : yawan saduwa yana karfafa yaro a ciki, saboda Annabi s.a.w ya kamanta ciki da shuka, kamar yadda ya zo a hadisin Abu dawud, mai lamba ta :  1847, kuma shuka tana kara karfi duk lokacin da aka bata ruwa.

3. Neman masa tsari daga shaidan, kamar yadda mahaifiyar nana Maryam ta nemarwa 'yarta tsari, lokacin da ta haife ta.

4. Nisantar duk wani abu da zai cutar da shi, saboda musulunci ya yi umarni da kula da rai, don haka zai yi kyau a matsayinki na sabon aure, ki nemi shawarar magabata da kuma likitoci, saboda ki gujewa abin da zai cutar da yaronki.

5. Zuwa asibiti, lokaci-lokaci don tabbatar da lafiyar yaron.

ALLAH SHI NE MAFI SANI.

*Dr, Jamilu Zarewa*

16\6\2014

Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support